26

29 3 0
                                    

🌼🌼🌼🌼🌼
  *_RAHMATULLAH_*

Rubutu da Tsarawa

🌼🌼 Oumm Arfah 🥰
   Wattpad @oummarfah20

Page 26

https://chat.whatsapp.com/EBcikkJMbAn5uZSaU88orH

   _Subhanallahi wa bi hamdihi, Subhanallahil Azeem_

    _Wannan labarin tun daga farkon sa har ƙarshen sa ƙirƙirarre ne suna, halayya ko wani abu mai kamance da wani ko wata, to arashi ne._

********

    Ganin yadda Baba ya wuce ciki Mamma ta bi shi da kuma kallon da Fa'iza ta bi bayan su da shi ya sa na san akwai abin da ke faruwa wanda ni ban san shi ba. Hannun Fa'iza na ruƙo wacce ta yi zurfi a tunanin ta na ce "meke faruwa? Akwai abin da ya kamata na sani wanda ban sani ba? Ki faɗa min na karanci damuwa a fuskokin ku ku uku" Fa'iza ta yi yaƙe a ganin ta murmushi tayi tace "ba komai ki kwantar da hnkln ki ba abin tada hnkl ba ne" kallon ta kawai na ke ina mamakin yadda ta ke ƙoƙarin raina ma kanta wayau da tunanin ni ta ke raina wa "Ni ba yarinya ba ce, na mallaki hnkln da kallo ɗaya zan iya gane akwai damuwa, sai dai idan ba zaki faɗa ba, sannan yaushe ki ka zo? Don na ga alama ba yau ko jiya ki ka zo ba, sannan ina Haj? Tun da na shigo ban ji motsin ta"  Fa'iza ta ƙi cewa komai sai kawai na miƙe na ce "bari na je na sami Baba shi zai faɗa min me ke nan, idan ke ba zaki faɗa ba" riƙo ni da tayi bayan na nufi hanyar ɗakin Baba shi ya yi daidai da fitowar su da sauri Mamma ta yi ɗakin ta ɗauko mayafin ta Baba kuma ya nufi ƙofa da sauri na tare shi nace "Baba me ke faruwa don Allah, ko ban nemo mafita ba, zan taya ku da addu'a" ya riƙo hannu na ya ce "Rahmatu kada ki ɗaga hnkln ki, kawai kiyi addu'ar Allah Ya sassauta mana jarabawar mu kin ji?" Ya faɗa min cikin rauni, lallai na yarda wannan jarabawar ta kai jarabawa tun da har Baba ya ke cikin damuwa haka, don a sanu na da shi ko yana cikin damuwa ko jarabawar rayuwa baya yarda ahlin sa su sani. Fitowar Mamma da shigar ta motar da isar Fa'iza baki tagar motar ta na cewa "Baba pls zan je" "A'a Fa'iza yara ba sa zuwa wurin" ta kalle shi in disbelief tace "Baba am 20 fa ni ba yarinya ba ce" kafin ma Baba ya ce wani abu na ce "ni kuma am 19, in dai za a je da ita, ni ma sai na je" shigar Mamma motar kawai sai Baba ya tada motar ya ce mu duka mu jira a gida...

********

     "Aslm Alkm Yaya brk da wannan lkc" "yawwa ambasada ya iyalin?" Bayan gaisuwa kawai ya koro dalilin kiran na shi "dama kan zancen auren yaran nan ne, Madinah da Babangida, ina ganin ya kamata a hanzarta kafin azumi tunda gashi har ya gabato" Amb Wazata ya yi ajiyar rai ya ce "Toh Yaya duk yadda ka gani, ai ƴaƴan ka ne ka isa da su" "yawwa tunda hakan ne na yanke nan da sati uku za a ɗaura musu aure kaga kafin azumi kenan ko?" Yace "Toh Yaya hakan ma yayi, Allah Ya kai mu da rai da lfy, Ya sa kuma a ƙulla alkhairi" ko amsawa bai yi ba ya kashe wayar sa. Saukar da wayar Amb yayi daga kunnen sa yana kallon matar sa Haj Bilkisu da ta ƙura masa ido don ta riga ta san da waye ya ke wayar don tun da ta ji ana zancen ƴaƴan ka ne ta san kan zancen, ba ta ƙin auren hakan nan ba ta son auren, sosai a ran ta wallahi Rahma ta ke son ya aura, kuma tana kan bakan ta na raba wancan auren, don takwarar ta ta fi ƙarfin makaho. Ba ta nemi jin komai ba shi ma Amb bai ce mata komai ba bayan sanar mata yaya ya tsaida sati 3, Allah Ya kai mu kawai ta ce ta yi shiru. Sai kuma tunanin ta ya kai kan ɗan ta tun da ya kira su a daren jiya ya ce ya kama su, su ke ta zuba ma Allah godiya da kirari, sannan yau suka tashi da azumin gode ma Allah da Ya tsare ma ta ɗan ta da tsarewarSa.

********
    Duk yadda ya so a ce a yau an wuce da su kotu abin ya faskara sbd matakan da ya kamata a bi ɗin bai iya bin su a daren jiya ba, dole sai yau ya ƙarasa shirye-shiryen tura su kotun, sai dai shi ya ɗauki ragamar tsare su da kan sa, sannan ya tabbatar inda ya tsare su ba su ikon guduwa ko gudanar da wani tsafin su, don wurin tsare yake da ayoyin Allah, ganin hakan ne sai koma gefe ɗaya yana kallon duk abin da ke wakana da yadda suke neman kashe kansu ta hanyar CCTV ɗin da ke nan ba tare da sanin su ba, haka kuma suka dinga tone-tonen asiran juna, in da kowa ke kula da Sammani don da alama ya tabbatar musu da ba za a taɓa kama su ba ne, gashi kuma ƙaryar ta ƙare da alama, don duk ƙoƙarin uwargijiyar su don yin ƴan siddabarun ta abin ya ƙi, sai kawai matasan ciki suka zuciya suka hau kan su da duka kafin ka ce me sun musu jini da majina. Ita dai Atumbulash kawai zaune ta ke tana kallon su, don ai ita kam gani ta ke kashe su za ta yi huce irin asarar da suka tafka mata, da ƙuruciyar ta za su sa ta ƙare rayuwar ta a prison, dole ta nemi mafita amma ta ya?

RAHMATULLAH Where stories live. Discover now