Chapter 36 ( HIS WIFE II)

39 2 0
                                    

NISFU DEENIY.......... ( A Yerwa family love triangle)

KHADEEJAH BINT ISMAIL ( DEEJASMAH )

MIKIYA WRITERS ASSOCIATION ( MWA)

In dedication to all kanuris around the globe......

Wattpad @deejasmah

Arewabooks @deejasmah15

09042522373

CHAPTER 36 (HIS WIFE II).

To my amazing better piece wish you a joyous and sweet day as you are; Allah ya tsare ki daga dukkan sharri da mugun nufi ya kare min ke daga dukkan abun k'i ya kuma k'ara miki bud'i da arziki ya k'ara had'a kanki da Habu a duniya da lahira. Ya k'ara masa bud'in alkhairi da zai k'ara kulawa da ke da duk lamuranki. Ya k'ara d'ankon k'auna mai k'arfi a tsakaninku ya kaimu ranar biki mu zo mu ci shinkafa mu yi rawa, ya kuma bamu ikon faranta miki da duk abinda muke da shi kamar yanda kike mana. There ain't no enough words that can describe all the wish i have specifically for you, but i'm wishing you a happy birthday sweet Jasmine, may you be blessed I love you😍.

Yau ban yi niyyar update ba, but i thought what will fit an amazing day like a chapter? This is also dedicated to you enjoy each and every word and remember that it was written with love and care for you🎭.

Lele ma tana cewa Happy birthday Deejasmah's paddy✌.

Kuka take yi cin-cin k'arfinta tun tana yi a tsaye har ta zame a jikin k'ofar ta tura kanta tsakankanin k'afafuwanta tana sake fashewa da mai cin rai da ciwo. Ba ta tab'a tunanin akwai zafin zuciya irin haka ba a da tayi zaton tayi kuka but yau kukan da takeyi jin shi take mai wani irin zafi da d'aci, ji take in ma bata yi ba toh zata iya mutuwa ko zuciyarta ta fashe gabad'aya. Ta kai more than 30 minutes a zaune a wurin tana kuka kafin ta tashi da sauri ta wuce ciki kashe wutan main parlor tayi kana ta shige d'akinta ta zauna a bakin gado tana mai kallon Sairah dake bacci cikin kwanciyar hankali ta shilla k'afa alamun tana jin dad'in baccin da take yi.

Wani sabon hawaye ne ya taho mata ta kai bayan hannunta ta share shi tana sake zurawa yarinyar idanu, a zahiri kamar hankalinta yana wurin but a bad'ini zuciyarta tariyo mata hotunan moments d'in su da Burhaan take yi, his sweet cool and sensational love wanda duk da ik'irarin k'iyayya da yake yi hakan bai saka shi k'in bata mad'aukaciyar soyayya a duk sanda suka kasance da juna ba. Wannan ne ma ya kan sakata samun hope har ta kai ga gasgata maganganun su Hajjah da Suleim na soyayyar da yake mata ba, don a wainnan lokutan ita kanta jin kanta take kamar sarauniyar dake mulkin duniya gabad'aya har ma ta ji tamfar tafi kowa sa'a da rabo a duniya baki d'aya.

A kuma koina zata bug'i k'irji take Islaam jarumi ne a fagen soyayya ya kuma san ta kan bi da mace har ta rasa hankalin kanta, ta koma kurma kuma makauniya mara tunani face na abinda da ya d'aurata a kai saboda tsabagen magic that is in his hand and touch. Ita kenan da yake fad'i da nuna mata bai so ina ga ita Fareesahr da ya fad'a ya kuma bayyanawa duniya girman soyayyarta da matsayin da take da shi a wurinsa, runtse idanu tayi hawaye yana zuba tana mai hangoshi da abar son na shi a cikin most intimate scene.

Yanayin da take hangosu ne yake sake triggering hawayenta wanda ta cigaba da yi tana jingina da allon gadon, ba kuma tayi wani yunk'urin tsayar da hawayen ko share su ba. Barin su tayi suna baza sharafinsu a kuncinta tana mai fatan su tafi with all her sadness and sorrow, sai dai kash sun k'i bata had'in kai balle suyi abinda take so don saukarsu daidai yake da sake d'igar ruwan dalma a k'irjinta wanda ke barazanar narkar da tsokar dake d'ankare da k'unci a wajen wacce aka bawa suna zuciya.

K'uncin dake cikin zuciya da sak'e-sak'enta a take suka fara bata shawarar da suke ganin zai iya zame mata mafita, wato ta tashi ta nemi petrol ta nufi sasanta ta balbala musu wuta su k'one su duka in yaso a rasa gabad'aya ko kuma ta tafi ta bud'e gas ta cinnawa gidan wuta duka kowa ya mutu ko a huta. Da hanzari ta mik'e da niyyar sauka don aiwatar da abinda zuciyarta ya raya mata, k'afarta ne ya tab'a na Sairah da ta mirgino gefenta tsura mata idanu tayi tana jin zuciyarta na karyewa ta koma yanda take da farko tana sakin ajiyar zuciya in ta sakawa gidan wuta 'yarta ta mutu shikenan ita ta kasheta da hannunta taje tacewa Allah mene? Ta kashe ran da bata ji ba bata gani ba gwara in su biyun ta tafi ta kashe bata da laifi saboda they broke her and its obvious that its her life they are after kuma bahaushe yace kashe makashinka kafin shi ya kasheka.

NISFU DEENIY.......!Where stories live. Discover now