53

23 0 0
                                    

*********Washegari da sassafe Gwaggo Yelwa ta shi, tana tashin sa.

"Idan kana sallahr asuba de mutum baya rasa duk abinda yake so ya kuma nema. Ai sallah rahama ce. Idan kana wannan baccin ma a haka ake raban Alkhairi a barka. Haka ka na ringa tashin ka da asuba amma baka tashi ba. Tunda ka zo baka yin sallahr asuba a masallaci sai rana ta fito".

"Ka tashi ka yi sallah. Ni zan tafi wajen aiki, na jiyo ko an kama wancan mugun mutum ko ba'a kama shi ba. Na ji de ya ake ciki".

"Ni fa Badaru ma ko? Bana so a kamashi na fi so a bar shi duniya ta faɗa masa hankali shege ɗan iska wanda iyayen sa suka ji asarar haihuwa. Allah de ya tsine masa albarka, Allah yasa ya shiga uku ya koma bara a titi ace wata nan yarinyar da ya so kashewa ta cece shi shege ɗan iska".

"Kashhh mtsww".

"Ka ga ga koko nan na dama, ni ba zan iya ci ko shan komai ba na tafi".

Ta sa kai ta fice. Tashi Badaru ya yi yana kallan ƙofar da ta fita. Kawai ita kadai ta ringa zuba tana zance?

Wayar sa dake kara ya ɗauka yaga waye zai kirashi a wannan lokacin kuma?

"Ina so mu haɗu".

"Zaka bani kuɗi ina san yin amfani da su".

"Uhm".

Kawai mutumin yace. Sannan Badaru ya tashi kawai bayi ya shiga ya fito ya rufe mata gidan ya miƙa mata makullin maƙota shi kuma ya fito bakin titi ya tari abun hawa ya hau.

A cikin Duwatsu suke haɗuwa. Inda babu kowa wajen ma kamar maƙabarta. Ya juya baya yana kallan ƙasan wajen. Yana zuwa Badaru ya bashi wata marar leda. Kana gani zaka san cocaine a ciki.

"Ka taho da kuɗi....

Tun ma kafin ya ƙarasa daga can ya Honourable Jamilu yace.

"Wait. Ni Na Ummi na sa ka, ka kashe min ba kowa ba. Yana nema ya takura min, yana nema ya shiga gona ta bayan mun rabu da shi. Siyasa ce ta haɗa mu da uwar sa, daba kuma ta haɗa mu da shi. Ya dake mu, wannan na haƙura, na fita a harkar sa. Uwar sa ta yi fice a siyar mu, na haƙura, na fita harkar ta duk dan a samu masalaha".

"Amma yana nema ya shiga hurumin yaro na. Yaro ne ke san Safna. Amma ita tace masa tana da wanda take so. Dalilin da yasa na fito da kai daga jail kenan domin na yadda da kai, aikin ka yana yi min kyau duk da cewar su Alhaji Hudu ba su san waye kai ba. Amma ni nasan ka iya aiki".

"Shiyasa nace ka kashe min shi. Ya bar duniyar nan, gaba ɗaya muddin baya da rai taya zata gan shi? Dolen ta ta auri ɗa na, ko tana so ko bata so. Ɗa ne rayuwarta. Dan haka ni bance ka sake cutar da kowa ba na shi, shi nake so, shi zaka kashe ba wata can ba ko wani can ba. Idan ka so, idan ka kashe min shi sai ka yi gaban ka".

"Idan ba zaka iya ba kuma na sa wani ya min wannan aikin. Magana ce ake yi ta ɗa na, ɗa na kuma ya fi min komai muhimmanci. Bana san jin sake maganar kuɗi, har sai ka kashe Imran a yau ɗin nan ba gobe ba. Idan ba kashe shi ba zan sa kashe min kaiiiii"

"Amma ya zaka min haka?

Girgiza kan sa ya yi yace.

"Babu yadda a mutumin da aka kama, dan idan aka sake kama ka to tabbas sunana zai fito, saboda a yanzu haka ne ake suspecting da aikatawa. Inda ace shi ka kashe ko shi ka yiwa wannan attempt ɗin da zan iya barin ka".

Badaru cike da mamaki yace.

"Amma ka bani kunya Honourable...

Dariya ya yi yace.

"Su Alhaji Hudu da Alhaji Mu'az gani suke, sune suke min alfarma amma ba su san da cewar kar nake ganin su ba. Ni ne nake yin amfani da su domin biyan buƙata ta, kamar de wannan".

IMRAN Where stories live. Discover now