ƊAN DAUDU 👳🏾♀️
*©️AuntiMamee*
_Page 23
Janye kallon ta itama Anmin ta yi tare da Ƙarasowa cikin palon
"Sabira sakko ki ci abinci kin kwaso yunwar hanya" Ammi ta faɗa sanda ta ke zubawa Sabira abinci a plate
Wani ɓoyayyen ajiyar zuciya ta saki tare da nufar ɗakin ta cikin ɗan ɗingishin da har zuwa lokacin ƙafar bata gama warkewa ba duk da an ja mata shi a gidan su.
Lumshe idanun sa ya yi tare da buɗesu ya sauke su kan Ammi da take kallon shi
"Ammi" ya faɗa cikin ɓata fuska tare da sakkowa dan cin abinci
"Ikon Allah! Sabira ko kinji na ce wani abun?" Amma ta tambayi Sabira da ke ƙoƙarin kai abinci bakin ta cikin zaro ido
Murmushi kawai Sabiran ta yi dan ba ƙaramin sanyi jikinta ya yi ba ganin Mumtaz da ta yi, ita a tunanin ta tun samuwar Lafiyar Ammi an sallame ta ita da Madam Dija daga cikin gidan.
Shiru su ka yi ba wanda ya sake magana har suka ƙarasa cin abincin, tattare kayan sabira tayi duk da Ammi ta hanata amma ta rantse kan ita za ta tattaren dan hakan Amma ta barta da mitar ita da ta kwaso gajiya.
"Ita matarka ba zata ci abincin ba" Ammi ta jefo masa tambayar bayan shigewar Sabira ɗakin Anmin
"Tasan hanyar kitchen ai, idan tana jin yunwa zata fito ta nema" ya faɗa tare da maida hankalin sa ga wayar sa dan ma kada Anmin ta sake wata maganar a kanta
"Har yau Imam a zuciyata ina jin samun lafiya ta ya ta'allaka ne da zuciyata da Allah ya ke dubawa, ban taɓa ƙullatar wani ko in ruƙe abinda ya yin ba, ban taɓa bari haƙƙin wani ya hau kaina ba, ko da nawa ya hau kan wani ina mai yafiya gareshi da fatan Allah ya yafe masa. Ka manta silar auren ku da dalilin, ban ce lallai kuma sai ka ƙaunace ta ko ka sota ba, dan ba'a taɓa tursasawa zuciya hakan amma ka yi ƙoƙarin sauke haƙƙin ka matsayin ka na miji koyaya ne, ina mai yi ma rantsuwa Imam ba zaka wulaƙanta ba, auren ka da wannan yarinyar itace Babbar jarabawar ka, ban sani ba ko ita ce kenan ko akwai wata jarabawar da Allah zai yi naka a gaba, amma ka daure ka amshi wannan nasan da ciwo da kuma matuƙar wahala wajan tursasa zuciya aikata hakan, amma fa ka sani Imam taka jarabawar ko rabin nawa bai kai ba da haka nake roƙon ka kada ka bari haƙƙin aure ya kamaka Imam ba zanyi farin ciki da hakan ba, Ni na cinye tawa ta farko ga kuma kyakkyawan sakamako na samu, ina kuma fatan idan akwai ta biyu ta kasance min mai sauƙi wadda zan iya cinyeta fiye da wannan wannan" tana gama faɗa ta miƙe ta bi bayan Sabira.
Ajiye wayar da ke hannun shi ya yi tare da ɗora kanshi saman kujeran da ya jingina bayansa jiki yana fuskantar silin.***
Saida ta tabbatar ba ta jin motsin su a mainpalon sannan ta fito ta nufi ɓangaren Madam Dija.
Kusan kiciɓus suka yi a bakin palon daga ciki. Kallon kallo aka shiga yi yayin da kowacce akwai abinda ta ke saƙawa a zuciyar ta game da ƴar uwarta.
Madam Dija da ke neman bayani da son sanin wasu abubuwan ita ce ta saita yanayin nata kallon ta maida shi zuwa murmushin yaƙe da faɗin
"Ai na san dole ki nemeni dan ni ba irin wadda ake takawa a ƙasa bace a wuce dole sai an waigo anga ya na takun ko akasin hakan, amma duk da butulcin da kika min zan manta na sake baki wata damar mu ƙulla wata sabuwar harƙalla" ta faɗa tare da komawa kan kujera ta zauna tana fuskantar Mumtaz da wani irin shu'umin murmushi
Ƙara takowa Mumtaz ta yi cikin palon itama ta samu hannun kujera ta ɗosana ɗuwawunta a kai haɗi da harɗe ƙafafunta waje ɗaya tare da girgiza su tana kallon Madam Dija