Chapter 39-40

146 11 1
                                    

💝💝 *MAHMOUD*
   💝

Written by F k Ahmad

*PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*

*_We don't just entertain and educate we touch the hearts of the reader's._*


WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*
*#IG PML WRITERS*
*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035*
*#http://maryamsbello.blogspot.com*

*_Follow me on Wattpad @ Fkahmad_

39 - 40

       Su Jannat da sauran jama'an main house nasu Jannat suka wuce. Wasu daga cikin Anty's d'inta suka zayyana wa Mummy da sauran wa anda basu je ba abun da Antyn su Mahsin tayi.

       Ran Mummy ne ya b'aci ta d'aga waya tayi dialling number Mamar Mahsin. Bugu biyu ta d'auka suka gaisa sama sama cikin b'acin rai sannan tace da ita "abunda y'an uwan ki suka mana ban ji dad'in sa ba, daga mantuwan abu shikenan sai a tada hankali?"

      Hak'uri Hajiya Halima tashiga bata sannan Mummy ta huce da kuma fad'a mata akan "tunda abun haka ne ma baza akai ba ai kuma yanzu baku mayar da ko dardumar koran kunya da ake ba ai ko atampa daya ne yaka mata amayar".

     Hajiya Halima ma bata ji dad'in maganar Mummy ba dan haka kawai kaste wayar tayi. Mummy taci gaba da masifa a d'akin tana fad'in " haba jama'a ni dama tun farko wannan mutanen basu mun ba kawai abu da Daddy'n su ne babu abunda na iya ga kuma shi Mahmoud d'in bansan me zayyi da wancan abar da suke k'ira Mahsin ba, ni tun farko bata kwanta mun a rai ba nace masa ga Salma k'awar Jannat ya aure ta tunda tana son sa amma shi yaki wai baya son ta gashi yaja mana masifa shi da uban sa".
     Hak'uri kannanta suka bata a d'akin nan ta nutsu ta zauna.

      Hajiya Halima ma tana saukar da wayar wancen Antyn su Mahsin d'in tajuya tana kallon ta. H. Halima tace da ita "me yasa kukayi haka Hauwa'u? kinga kun haifar mana da magana yanzu".

      Hauwa'u ta d'aga murya tace " oh shine uwar tasa takira ki wai meye tace?" H.Halima tace "fad'a tayi mana akan bataji dad'in sa ba". "Lallai kam d'an Adam butulu" cewar Hauwa'u taci gaba "akan wannan shine zasu ta da hankali sun manta cewa mu y'ar mu muka d'auka muka basu? Ni ina mamakin yaya ma da ya d'auki y'ar cikin sa ya danka wa mahaukacin d'an su da ko isashen hankali baida shi, in akayi magana wai shi jihadi yayi mtsw". Ta juya ta fita.

       Jannat da Mufeedah suka bar gidan zasu gidan su Mufeedah saboda dare yayi. Suna tsaye a bakin titin gidan suna jiran abun hawa sai ga Mahmoud a motar wani abokin sa da yakawo shi gidan.

      Sauka yayi yagan su a tsaye fuskar Jannat kad'ai ya gani da yake ta gefen ta ya taho.

      Sunan ta ya k'ira " Jannat". A sannan tajuya ta gansa cike da jin dad'i tace "laa ya Mahmoud, kadawo gida ne?" Mufeedah ma juyowa tayi da murmushi d'auke a fuskar ta, had'a ido hud'u suka yi da Mahmoud, gaban sa ne ya fad'i jikin sa ya d'au rawa kallon ta yake sam babu kyafta ido har sai da itama Mufeedah taji wani abu akansa.

      Horn suka ji akayo musu daga inda suke Musty ne ya dawo gida. Ganin y'an uwan sane a wajen ya sauk'o da murnar sa. Jannat ta iso wajen sa tace "yauwa ya Musty dan Allah ka kaimu gidan su Mufeedah kaga bamu samu abun hawa ba", Musty yace " naki d'in sai dai in ke kad'ai zan kai tunda ita bata iya cewa na kaimu ba".

      Nan Mufeedah ta matso tana dariya tace "haba besty na yi hak'uri ka kaimu". Shima dariyan yayi yace to ku shigo mu tafi.

      Mahmoud da ke tsaya ya zuba musu ido yace " erm Musty idan ka kaisu kazo ina neman magana da kai yanzu kar ka jima", Musty yace "toh Ango sai na dawo", suka shige motar suka tafi.

      Mahmoud kuwa abun nan ya dame sa sosai tunanin ina yasan yarinyar nan a da yake kuma ya akayi ya ganta tare da Jannat kodai k'awar tace bari dai ya jira Musty yazo ya ansa masa tambayoyin nan.

     Cikin gidan ya shiga ya wuce side na Mummyn su dan su gaisa.

      Bayan Musty ya kaisu ya dawo gida ya k'ira Mahmoud a waya ya tambaye sa inda yake nan ya gaya masa  d'akin da yake ya je ya same.

      Shigo wa yayi ya zauna gefen sa yace "gani nazo". Tun d'azu babu abunda Mahmoud keyi sai tunanin Mufeedah, ji yayi kawai sonta da sha'awar ta na shigar sa tun kallon farko da yayi mata d'azu ya kasa daina tunanin ta.

     Musty ya dafa kafad'ar sa yace " ya Mahmoud tunanin me kake haka?". Ajiyan zuciya Mahmoud yayi ya juyo yana kallon Musty yace masa "wacece wacce suke tare da Jannat?" Musty yayi murmushi yace "Mufeedah ce ai". Gaban sa ne ya sake fad'uwa a d'an razane yace " wace Mufeedah'r?" "Y'ar Daddy Ahmad mana har kamanta da ita koh". Wani sanyi yaji a ransa wanda baisan dalilinsa ba yace "that small girl, wow! Ta girma".

     Dariya Musty yayi. Sai kuma Mahmoud ya canza yanayi. Musty ya tambaye sa "meya faru kuma yaya? Yanzu kake cikin farin ciki", Mahmoud ya daga idanun ya kalle sa yace " Musty gobe aure na da Mahsin amma ji nake like she's not a perfect match to me". "But why?" Cewar Musty da d'an damuwa.

      Mahmoud yace "bansan ta ina zan fara zancan nan ba, tun farkon had'uwa ta da Mahsin ban tab'a jin abunda nake ji ba akanta sai Mufeedah da d'azun nan nake kallon ta, i have never go through such pain sai lokacin da nake tare da Siyamah and now ina experincing akan Mufeedah, does that mean am in love with her?" Murmushi yayi ya kuma cewa "oh yes am right Musty ka taimake ni ka fad'a wa Daddy Mufeedah nake so".

       Musty ko baki galala ya sake yana kallon Mahmoud da mamaki. Sannan ahankali yace " but what about Mahsin gobe fa d'aurin auren ku", Mahmoud yace "yes yes i knew it, can't I get married to both of them at that very tomorrow?".

      Stammering Musty ya fara yace "ha ho hw how will I know, kafasan Daddy ta ya zaiyu?". Mahmoud yace "ok then zanje na fad'awa Mummy nasan zata saurare ni". Nan ya mik'e ya nufi d'akin da Mummy take.

_Team Mufeedah_
_Team Mahsin_
      Am on Mufeedah's side😜

Urs Fannah😘

MAHMOUDWhere stories live. Discover now