Ana tashi ko ta mike tana rike da hannun amal zata dau hanyan fita nusaiba ta dauke amal ta harareta tayi waje da ita
Kawai baki ta bude tana ganin ikon Allah
Bayan ta tabi zuwa wajan motan aliyu tace nusaiba kike ko wa?
Ban yata nan
Naqi din yazaki zo da yarinya gun biki ana ta hayaniya kuma bacci take ji saboda rashin sanin ciwo kaiKai ke kar ki fadan ba suger ki daure ki haifi naki tukuna sekiyi ikon amma ba da nawa ba kina ji ko kece baki san zafin haihuwa ba da rashin ciwon ta in kin ga dama ki haifa kema sannan kizo mu kara ta kwace ta daga hannun ta har tana hankade ta.
Tanga tanga tayi zata fadi motan ta tareta
Ta bi bayan nanah da kallo yana karasowa ya bude yace muje ko ina amal din?
Seta fashe da kuka ta rungume shi tana kuka aliyu baka ce ka bani amal ba
Eh man na baki
Amma matar ka take min iko da ita wai ban san ciwon haihuwa ba har hankada ni tayi
Aliyu kar ka karya alkawarin daka minDan bazan bar garin nan ba tare da amal ba
Ya ce oya shiga mota muje kwantar da hankalin ki kinji
A ransa yana jinjina zancen bada amal dan yasan nanah ba karamin tashin hankali za ayi ba.
Kuma yasan taci sa'a bata ma zane ta ba dan kadan aikin nanah kennan ba abu ne me wuya a gunta ba
*********************
Tun hanya gaban ta ke faduwa ranta na mata suya hawaye kawai take bukata su zubo mata kuma sun qi gashi ta rasa bacin ran ma na meye?Kamal na ankare da ita se ya ja bakin sa tsuke kar bomb din ya fashe da shi
Ya kamal ka maida ni gida na
Ki bari ki kwana a cikin gida gobe daurin aure
Ni ka maida ni gida kawai akwai abunda zanyi
Me?
Ta masa banza
Haka ya juya kan motar zuwa gidan ta.
********************
Kowa maganan aliyu da nusaiba yake a dangi musamman inna talai tana ta bambanin fada Allah ya kawo mata aliyun zesan abun da yake yi ai shirme ne yaushe ze biye ma wadda bata da tarbiya suna hauka a titi mungode da zuwa bikin ai gobe za a gama ta koma garin su mu nan hausawa ne.
Umma na bata baki tayi shiru sabida umman aliyun naji
Ita kuma dama tana son nusaiba dan yadda take son aliyu kima wanda yake yi da aliyu dashi take yi dan tasan irin kin aliyu da nanah keyi kuma dadin dadawa nusaiba yar masu kudi ce kuma tana son aliyu zasu more da ita yarinyar.
Ai nanah ta gama tafiya daga rakiyan ta tunda bata son aliyu ita ma bata son ta kallon su kawai take yi munafukai.
******** *********
Zuwan su kusan tare da su nusaiban yana tsaida motan tayi waje da karfi ta kulle motab seda kamal yaji har tsakar kan sa ta na jan amal kaman ta tsinka ta
Ta tare hsnyan shiga gidan
Tana huhura hanci ita dai amal kuka tasa dan ta gaji kuma yunwa take ji
Nusaiba ta riko ta aliyu kalli amal na kuka ko dai dukan ta nanah tayi ne ?
Harara nanah ta sakar mata tayi tsaki
nanah meye haka?
Ka bude min gida na shigaIn naki fa
Ta masa shiru ka vude min na sama mata abunda zata ci ta hutaJin amal ce keda bukata yasa ya bude yana budewa ya shiga ya bar mukulin jikin kofar
Wuf tayi ta shige da amal ta zare mukulin ta na kallon nusaiba ta tura kofar ta kulle tasa key din cikin bra dinta tayi tsaki tace mayya!
Kofar ta fara bugawa nanah ki bude min kofa!
Har tayi kitchen
Shi kuma jin bugun kofa ya fito
Nanah ina mukulli?
Tsaki tayi ta juya ta cigaba da dafa indomie din amal na kan tebur a kitchen din.
Nanah ina mukuli?
Wallahi bazata kwana a gidan nan ba yau kaji ma na rantse ta nemi wani gun bazan bude ba
Nanah naga alama kin fara san raina ni ko ina wasa dake ne ko kuma ita sa'ar kice?
Sa'a?
Raini?
Ai raini ya kare aliyu tunda a gaban yarka kake aikata abun da za a raina kanSunan ya maimaita *ALIYU* ya fada ya kai sau uku
Nanah kar ki bata min rai ..ta juyo indomien ta ce amal muje kici .
Bin su yayi ya amshi amal ya kaita daki my amal kici ki kwanta kinji dady's gurl!
Ok abbana gud nyt
Ya mata peack ya fita ya ja kofan ya kunna mata fitilaTana zaune kan kujera nusaiba na zaune a kasa tana ta karkade saurayen waje dake cizon ta lallai ma wannan yarinyar
Nanah bakuwata ce fa kike son zubda min mutunci
Wani irin kallo ta masa ta yamutsa fuskarta tace mutunci ai madara ne ya riga ya zube a idan kowa bama ni kadai ba
Me kike nifi
Abunda kake tunani!A tsawace yace *nanah* duk da ta tsorata amma seta dake tace da kennan banda yanzu se a bi wani sarkin ta yi dakin amal ta sa sakata ta kulle
A gun tayi ajiyan zuciya ta dafe kirjin ta tana ajiyar hrt wai Allah na nasan in da ya kamani seya ci zalina wallahi wannan shegeyar sede ta kwana a waje badai a nan ba mayya kawai shi kuma solobiyo kawai.
Ba yadda zeyi se kiran hashim yayi yace yana ina
Ina gida
To ga nusaiba a waje ka bata gun kwana nanah ta kulle gidan
To yaya
Yayi dariya bayan ya ajiye wayan nasan za a rina wanan da kishi ina jiran wannan ranan dama
Nanah ko kin yarda ko baki yarda ba kin fara son *Aliyu hydar*
Ya aliyu girman kai nanah girman kai sun kasa gane ainihin dangantakar su kiyayya ce , ko kuma soyayya?
*#teamaliyufatima*