BABI NA ASHIRIN DA UKU

3.3K 150 12
                                    

🤡HANJIN JIMINA.. Akwai naci akwai na zubarwa🤡

Billy Galadanchi

HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert & perfect writer's).

Vote me on wattpad@68billygaladanchi.

Sadaukarwa ga Aminiyata Hafsat Ilham.

23
*Bayan shekara daya*

Zamane na Amane tsakanin gidajennan guda uku cike da kaunar juna,bangaren Haj juju dai juna Biyu ne harna tsawon watanni biyar,yayinda Amal take da nata kusan 6 month, amma fa khairiyya shiru shiru har yau ba labari abin kuma yana damunta ga rigimar Hauwa kazama kullum ta yau daban na gobe daban,yauma kamar kullum a parlor suke zaune ita da Khameel tayi Matakin kai da cinyar kameel yayinda yake watsa da kananun kitson da aka yarfa mata,dan d'agowa tayi cike da shagwaba tace "Yaa kameel dan Allah kabari muje asibiti wlhy na damu" ran kwafowa yayi ya saukar mata da Sumba a goshi, "Baby haihuwa fa ta Allah ne bazamu janyo ta da karfin tuwo ba dole ne semun jira har sanda me bayarwa ya bamu" dan tsuke fuska tayi tashiga yarfe hannaye tna shura kafa "Allah ni yaa kameel so nake muje,kaga fa juju da adda Amal nikadaice kumama bansan mesa kake haka ba baka ma wani damuwa" dagota yayi gaba daya "yan matan kameel ki fahimceni ba wai bana so bane ina sone ki riqa yarda kaddara" shiru tayi tana nazarin kalamansa batada lavarin an sanar masa dawuya ne ta kara aihuwa tun a asibiti kasancewar a wancen lokacin sun zata shine mijinta acewar Su an dakawa mahaifarta wani abu kuma ta huje abune mawuyacin abu ta kara iya daukar ciki,be sanar wa kowa ba,Wannan dalilin yasanya bayaso suje asibiti kar ta gane,a hankali ta kalleshi,tace "yaa kameel dan Allah da manzan sa kabarni inje Inji takameme meyake damuna inaji ajikina cewar banida lapia,Idan har kanasan kwanciyar hankali na ka barni naje" tausayinta ne ya kamashi yace "ki shirya gobe muje kinji yan matana" makalkale shi tayi Sega Hauwa a Kansu

"Banza jaka dakika gama wofintar da yayanki atitim ? Wlhy keda haihuwa har abada Banza jaka,ayi dai mugani Idan tusa zata hura wuta" Idan da sabo tariga ta saba kallon shi tayi tayi kokarin danne damuwarta da shagwaba tace

"Yaa kameel en matanka zata kwanta ka kaini daki plss" Murmushi yayi yana yaba jarumtarta ya tashi ya ciccibeta aikam basu ankare ba se ganin Hauwa sukayi har janyo kujerar dining daya,da karfin tuwo ta bugawa kameel a baya da sauri ya ajiye khairiyya yana kokarin kareta Amma ina sanda Hauwa tayi nasarar kwala mata a cikinta,take ta zube a wurin hauwa se banbami takeyi

"Ni zaku nunawa lalata yayan iska Shegu wlhy baku isaba" juyawar dazeyi yaga jini nabin kafafun khairiyya, dagata yayi yaga sam bata motsi yace..

"Hauwa wlhy duk abinda ya faru da yan matana sena wulakanta ki wlhy wawiya kawai jaka kazama" daganan yayi waje da khairiyya

"Ba yan matanka ba yan mazanka Banza na mamajo" Banza ya mata,asibitin data haihu can yakaita koda suka duba cikine da ita na watanni Biyu kuma yana ta zubewa duk iya taimakon dazasuyi sunyi amma ina seda yafita,ga Wannan abin ba karamun kara bata mata mahaifa yayiba,kwananta Biyu bata san inda kanta yakeba,koda ta farfado ma ba lapiya daga nan aka fara zancen cire mata mahaifa inda asibitin sukace Idan ba'a cire ba ze iya zame mata cancer!!!!! Kameel yayi kuka lokaci daya ya sallami Hauwa saki daya,jin Wannan maganar ya furgitar da karamar yarinya khairiyya har yau shekarunta basu kai sha takwas ba,kameel da aka baiwa takarda ya sanya hannu zaman dirshan yayi ya saka kuka dakyar dadynshi ya lallabashi ya sanya hannu, bayan Kwana Biyu aka Shiga da ita tiyata ana shirin farawa wani doctor abokin daddy dake London yace kar ayi azo masa da ita London ze yi gyaran mahaifar,hakan kuwa akayi batare da bata lokaciba aka shirya tafiyar visa ce kadai ta tsaidasu,suna samu kuwa suka wuce,ita da kameel kawai suka tai Alhamdulillah anyi aikin successfully komai ya dawo normal,soyayya ce me karfi akaci gaba da zubawa a London itada kameel,wanda basu dawo gida ba se da ciki karami dan wata wanda basu masan dashi ba ajikinta murna fal aran kowa,koda suka diro se ganin sashin Hauwa sukayi abude Ashe daddy ya dawo da ita,dama ya kudirta hakan aranshi,be nuna komai ba yaje gareta ga mamakinshi gidan qalqal an gyarashi ga kamshi gashi kuma an musu girki,haka dai zamansu yaci gaba da kasancewa ka daran kada han...... Amal ta sauka lapia ta samu yaronta kyakyawa aka saka masa suna kabeer,mahaifinshi naji dashi sosai da uwarshi....

Hilal Na kwance yana sharar baccinsa nakuda ya tashi juju, madam duk da kasancewar ta me tsananin raki seta kasa koda kwakwaran motsi taso sosai ta tasheshi sedai kamar yanda bakinta ya mutu haka bayanta ma ko kadan kasa motsi tayi Allah ne ya taima keta rigar baci kawai ce acikin ta aikam wata azabace ta ziyarceta me tsanani jitayi tamkar ta mutu gashi kamar za'a tsaga mata mara haka taji wani yunkuri tayi zata mike Sega baby ya fado tare da uwar lokaci daya yaro ya cancara uwar kara a razane Hilal ya farka a zatonsa mafarki yakeyi,fitila ya kunna a gigice yaga Wannan abin ficewa yayi ba shiri ya kwankwasa wa Hauwa gidan kameel daya,aikam akayi Sa'a kameel na gidan itace ta yanke cibiba da kanta yaro sak uwarshi blacky dashi,kuma ko tear bata samuba gwanin burgewa,Hauwa da Khairiyya ne suka gyara gidan tsaf da wurin tun da asuba Sega Amal Sallah kawai a ka idar,murna awurin Hilal ba'a magana yama rasa me zeyi....a daki ya tadda jawaheer tafito wanka bushewa yayi da dariya yace
."blacky wai kinga katon hancinki kuwa duk kin wani kara hawa,gashi kuma baki kamar zunubi" Murmushi tayi tace "Ga blacky nan Allah ya baka zan nuna maka bolar da ake kai baqaqe seka kaishi" dundu ya d'aka mata a baya yace "Dan gwal din kike cewa nakai bola,cikin shawaga ba tace

" Asshhh yaa Hilal da zafi wlhy" Murmushi yayi yace "yau dai Su madam anji practical ba theory ba,to sannu da kokari Allah saka da alkhairi ya baki lapiyarki yakuma raya mana Al-ameen" Murmushi tayi tace "Ameen abokinka kayiwa takwara kenan?" Murmushi kurun yayi yace "Aminina zakice"......ranar suna an darji naira ba laifi,kasancewa khairiyya tasha jikila gashi bata masan da cikinba yasanya tafara bleeding dole aka kaita asibiti take suka bata bed rest,ahaka taci gaba da rainon cikinta har lokacin haihuwar shi yazo, cikin ikon Allah ta sauka lapia baby girl sosai take kamada kameel se murna yake,matsala daya ne dole sanda aka cire mahaifar gaba daya Wannan lokacin kasancewar barinta a jikinta babban matsala ne. Dolensu suka rungumi kaddara,yanzu Hauwa ta zama ta gari zamansu suke lapia lau,bayan shekara daya kameel ya kara auro Deena,khairiyya bata saka komai a ranta ba ta dauki Wannan amatsayin tsarin Allah kuma mijinta na sonta gashi maryama Deena tana ganin girnan khairiyya sosai,a haka Hauwa tazo haihuwa awurin haihuwa Allah ya mata rasuwa,tabar yaro namiji Su khairiyya sunsha kuka komai ya dawo musu ba dadi,a haka suka dauki kaddara suka ci gaba da zaman aminci dajuna,khairiyya ce ta shayar da yaron da hauwa tabari.

Tammat bi Hamdilla.

Ina godiya agareku

Duniyar makaranta
Taskar billy Galadanchi
Hanjin jiminas fans
Sophe G novels
Mimei bee novels group
Huguma novels group
Haske writers Association
Pherty zahra novels
Hajja ce novels
Littafan hausa zallah

Da sauran daban anbaci sunayensu ba,nagode da dinbin kaunarku ga Wannan book din.

Mom Nu'aiym ce.

Hanjin Jimina...akwai Naci Akwai Na ZubarwaWhere stories live. Discover now