23

1K 86 0
                                    

☄☄☄ *'YA'YAN ASALI* ☄☄☄
                    ☄☄☄☄☄
                           ☄☄☄
                                 ☄

          *ωяιттєи вY:*
     Aisha Muhammad
         *(Mzzdaddy)*

                    &
         Shamsiyya Salis


*ELOQUENCE WRITERS ASSOCIATION*


              2⃣3⃣

  Suna zuwa ya sake ta tareda cewa "waye wannan?", cikin fushi yake magana, idonshi yayi ja, jijiyoyin kanshi duk sun tashi gabadaya ta tsorata dan bata taba ganin dis side of him ba.


     Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa ya riko ta tareda jijjigata yace " nace waye wannan wanda ya saukeku yanzu?", baki na rawa tace "ya...ya ba kowa bane".



     Hannu ya daga ze wanke ta da mari tayi sauri ta runtse ido, shikuma kome ya tuna seya sauke hannunshi yana huci, jin ba'a mareta ba yasa ta bude ido tana kallonshi yace " dis is the last time I will ask u, who is he?".


    Kanta kasa tace "yaya cousin din Zainab", kallonta yayi yace " me kukeyi a mota har Marwiyya da Zainab din suka fito kina ciki?". Shiru tayi dan batasan me zatace ba, yace "dake fa nake, koh baki da baki ne". Cike da shagwaba tace " yaya bazaka mun komai ba inna fada ma", kallon ta yayi yace "go ahead ina jinki".


    
     Cikin shagwaba tace " yaya bakai bane dazu kamin ihu ka sani kuka ba, saboda kawai banyi sallama ba, shine nima nace sena sa ranka ya baci, shine da muka dawo na hango ka senaki fita daga motan saboda kayi tunanin saurayi na ne", tana gamawa ta matsa baya da sauri saboda gudun duka shikuwa mamaki ta bashi tareda ganin yarinta karara tartare da ita, hannunshi yasa a aljihu ya kada kai yace "yanzu tinda kinyi nasara zoki fita", " yaya dan Allah kayi hakuri, bazan sake ba", dago jajayen idonshi yayi yace "not now pls, zoki fita", turo baki tayi tayi gaba tana kunkuni ta fita shikuma ya dafe kanshi tareda zama kan gado yace " dis girl is going to kill me".



       Marwiyya gabadaya hankalinta ya tashi saboda tasan yayanta yayi fushi gashi yaja Amatullah, "Allah kadai yasan wani irin fada ze mata", ta fada a zuciya tareda kai kawowa a compound tana jiran fitowan Amatullah.



    " is something wrong , y are u pacing up and down" taji muryan Abdul a bayanta, juya tayi direction dinshi tace "Ama is in trouble", " trouble like how?", ya tambaya confused, nan ta bashi lbrn abinda ya faru shikuwa me zaiyi banda dariya, Marwiyya tsayawa tayi tana kallonshi kyau yakeyi in yana dariya amma a halin yanzu bataga abin dariya ba.



    "Dariyan me kakeyi haka?", ta tambaya ya kalleta yace " Ama mana, bataji kuma ai duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka saboda haka ba ruwanki, ki kyalesu they will settle their differences, yanzu zo muje kiga wani abu".



    Da haka ya jata se dakinshi ta zauna kam couch shikuma ya dauko laptop dinshi ya kunna ya fara nuna mata hotunan gidan da zasu zauna, angama saura furnitures se kayan electronic gadgets, sosai gidan ya mata kyau. Suna cikin haka taji alaman Amatullah ta dawo da sauri ta mike tace "yaya zan leka Ama daga nan zanje na kwanta", yace " ok, slp tyt", da haka ta fita daga dakin  Amatullah tagani zaune se cika take tana batsewa ita a dole tayi fushi.



     "Sisto ya kuka kare dashi, meya miki?", kallon Marwiyya tayi tace " wlh yaya ya cika zafi dayawa", Marwiyya ta zauna tace "meya faru", nan Amatullah ta gaya mata duk yanda sukayi Marwiyya tace " alhmdllh tinda be tabaki, amma gobe ki bashi hakuri ni bari naje na huta", da haka ta fita Amallah tace "hakuri my foot".




TEAM AISHAMS🤝🏻

'YA'YAN ASALIWhere stories live. Discover now