BABI NA BAKWAI

4.6K 330 8
                                    

Badiyya cikin dare haka taita maimaita sunan Sultan, ita Firdausi abun har ya fara bata tsoro, kardai yarinyar nan har soyayyar Sultan ta shiga ranta? Abunda yake tsaya mata a rai kenan.

A bangare Sultan kuwa; kwana yayi abun ya tsaya mashi a rai, domin shi bai taba kawo wani abu cikin ranshi ba, hasalima ya dauki Badiyya a matsayin kanwarshi, saidai dukda matsayin daya bata; yasan ta taba wani bangare a cikin rayuwarsa, wanda saida Kamal yayi magana sannan ya fara realizing.

Da sassafe Firdausi ta tada Badiyya, bayan tayi mata wanka ta shirya ta, suna breakfast; wanda Firdausi ce ta bada aka siyo masu koko da kosai, domin Musaddiq kadai ke zama cikin gidan, babu kayan abinci.

"Nikam Musaddiq, ya zanyi da Dutsin-ma? Ko zuwa zan rikayi kullum ina dawowa?" Firdausi ta fada, yadda tayi maganar yana nuna ta rasa mafita, batasan me zatayi ba.

"Ayi haka kuwa, Adda Fiddi?" Ya amsa tambayarta da wata tambayar. "Kudin mai ai zaiyi yawa, kuma yaushe kika tashi har ki isa Dutsinma." Ya kara fadi, hade da juya kanshi.

"Nima ina tunanin haka Musaddiq, amma yanzu ya za'a yi? Kaga yau zanje Katsina in karbo transfer, sai in karbo transfer letter Badiyya." Ta fada, tana satar kallon Badiyya, domin batasan ya zata dauki maganar chanza nata makaranta ba.

"Yauwa!! Akwai wani gida da aka bani cikin gado na, sai kije ki zauna." Musaddiq ya fada, yana murmushin gano mafita. "Gidan yana Unguwar Rimi."

"Lahh! Ni nama manta da gidannan wallahi." Ta fada, murmushi bayyane kan fuskarta. "Nagode, Allah ya bar zumunci Musaddiq."

"Kai Adda Fiddi, miye na godiya kuma dan Allah? Miye a ciki danna baki gida ki zauna? Dan Allah ki daina." Musaddiq ya fada, fuskarshi na nuna alamun baiji dadin godiyar data mashi ba.

"To Musaddiq, Allah yabar zumunci." Ta fada tana murmushi, hade da patting cinyarshi alamun jin dadi.

Musaddiq mikewa yayi, ya kalli Badiyya; wadda tayi shiru tana kallansu, domin ita yanzu burinta daya; ta ga Sultan. Chanza mata makarantar da za'ayi bai wani daga mata hankali ba.

"Badiyya, zo muje ki rakani bakin kasuwa." Musaddiq ya fada, yana mikewa tsaya.

Badiyya bata furta komai ba ta tashi tayi entwining hannayensu, daga haka suka fita.

"Kuyi sauri fa, yanzu zamu tafi." Firdausi ta fadi da yar kara, domin suji abunda take fadi.

Suna fita da Musaddiq yaje ya siya ma Badiyya chocolates, da kayan zaki, domin ya lura she need someone to vulgarize her back into her jovial self.

A haka ta nuna mashi farin cikinta, wanda har dariya tai mashi, abun ba karamin dadi ya mishi ba. Suna komawa gida suka iske Firdausi ta fito, harta handbag dinta na hannunta.

"Badiyya taho mu tafi to, tunda baza'a mani tayin chocolates dinba." Firdausi ta fada da sigar wasa, tana me jan hannunta.

"Kai Momy, kinsan fa ina baki, ko Dady idan ya siyo man ina baki ai." Badiyya ta fada tana zumburo baki.

"Kyaleta kinji Badiyyar Uncle, ku tafi kar kuyi rana." Musaddiq ya fada, yana shafa kanta alamun tayi shiru.

"Bye Uncle, zance Sultan am ya turo mani pictures dinmu wayar Momy sai ka gani ko?" Ta fadi tana washe baki, domin a ganinta dole Momy ta kaita gidansu Sultan am.

"Yauwa My Bady, kice ya kara daukarki wasu ma." Musaddiq ya fada yana murmushi, domin ya lura maganar Sultan kadai ke sakata farin ciki.

"To Uncle karka damu." Ta bashi amsa, tana me shiga motar.

"A gaidaman da Sultan am." Musaddiq ya fada da karfi.

A haka suka tafi tana ta shan chocolates dinta, itadai Firdausi kallonta kawai take.

RAYUWAR BADIYYA ✅ Where stories live. Discover now