*K'UDIRINA*
®
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*©
*EASHA MD**Dedicated to Maryamerh Abdulrahman* (Kwaiseh)
*21*
Washegari ta shirya tsaf dan tafiya makaranta. Fitowa tayi ta samu Yaya Muhammad zaune jiki kam Alhamdulillah. Cikin natsuwa ta fara magana.
"Yaya na shirya zan tafi. Ina Sim d'in insa a wayar."
D'aukowa yayi ya mik'a mata tare da bata kud'i.
"Gashi sai kiyi amfani da wannan."
Cikin girmamawa tasa hannu ta amsa, tare da furta.
"Na gode sai na dawo."
"To Allah ya bada sa'a."
"Amin Yaya." Tasa Kai ta fice daga gidan.
Ta isa cikin makaranta, ta had'e da k'awarta Maryam.
Dubanta Maryam tayi cikin jimami na rashin zuwan Islam jiya da bata samu tayi jarabawa ba tace.
"Islam mai ya hanaki zuwa jiya? Bayan kin san exam d'in da muke dashi. Kina sane da cewar S Fulani ba mutunci ne dashi ba in dai akan harkar karatu ne?"
Ajiyar zuciya ta sauke mai nuna alamun damuwa.
"Ki bari kawai Maryam! Wallahi Yayana ne yayi accident aka kaishi asibiti. Kin san shi kad'ai gareni a rayuwata bani da kowa, dole tasa ba zan iya komai ba a kan halin da yake ciki."
"Allah sarki! Ya jikin nashi?"
"Jiki kam Alhamdulillah! Ya samu sauk'i sosai. Yanzu haka yana gida."
"Kece ai Aminatu baki da waya da za a kiraki bare har a san halin da kike ciki."
Cikin murna Islam ta ciro waya dake cikin jakarta tace.
"To yau dai na raya gorinku gashi nayi waya."
Maryam ta amsa cikin farin ciki.
"Kai amma na tayaki murna, amma ace mutum yayi ta zama ba wayar nan ta zamani. Bari nasa maki number d'ina."
Sa mata tayi had'i da saving d'inta. Tana mai cewa. "Ni na fara launching d'inta."Dariya Islam tayi, dan it's inde ta rasa abinda zata ce maka, sai dai tayi dariya.
Sanin halin da Islam suke ciki yasa ta jata, kati na MTN ta sai mata na d'ari hud'u tasa mata.
Cikin jin dad'i Islam tace.
"Na gode sosai. Ya kamata muje mu d'an k'ara zama muyi karatu kafin mu Shiga."
"Gaskiya kam."
Lokacin da zasu shiga yana yi, suka shiga sunyi exams lafiya sun fito. Har yanzu Islam na cikin jimamin rashin jarabawar da bata yi ba jiya.
Kallon Maryam tayi cikin damuwa.
"Wallahi Maryam ina jin takaicin rashin yin jarabawar jiya. Na tabbata dole sai na fad'i course d'inshi, da zai taimaka min yamin adalci ai da naje na sameshi.
Cikin tsoro da zare ido Maryam ta furta.
"Ke! Yanzu zaki iya zuwa ki tunkareshi? Ai ba zan iya ba da d'aure fuskarshi, ni kwarjini yake min bana iya magana dashi.
"Ni kaina tsoronshi nake ji, amma dole in k'yaleshi dan course d'aya da zan fad'i ba wani abu."
Tafiya suka ci gaba dayi suna d'an ta'ba fira. Tsaye yake jikin motarshi ya hard'e hannunshi, idonshi na kan Islam. D'agowa tayi suka had'a ido, da Sauri ta duk'ar da kanta k'asa.
YOU ARE READING
K'UDIRINA
FanfictionLabari ne na yaya da k'anwa da suka taso cikin maraici ba tare da sun samu mai tallafa masu ba.