11-20

9.8K 396 8
                                    

MATAR SADIQ*馃拺

*Na fertymerh xarah*馃挐

          11 to 20

     Sanda suka isa cikin gidan umman na xaune a tsakiyar katafaren falonta, takardune xube a gabanta tana dubawa na campany, idanuwanta sanye da siririn farin glass, sallamarsu ta katse mata rubutun da take amma bata dago xuwa dubansu ba illah ta amsa sallamar a taqaice.

zuhura ta sami wuri ta xauna a takure hade da fadin barka da aiki umma ya gida, kanta a sunkuye har lokacin bata dago ba ta amsa, yayin da sadiq ya xauna kujerar dake fuskantarta

yace mun sameku lfy umma? sai alokacin ta dago manyan idanuwanta ta xuba mishi hade da xare madubin glass dinta

tace inace kaga alamar haka,baka sameni da wata matsala ba.

cikin dakewa da nuna jarumta irinta sa a matsayinsa na babbbn soja mai rank uku a riga

yace haka nake buri a koda yaushe na sameki lfy, ta tabe bakinta bayan ta kauda kallonta garesa tana kallon takardun gabanta

tace munyi dakai xakaxo jiya a friday ko miye dalilinka naqin xuwa sai yau saturday ko umarnine uwargidan taka bata baka bane?

ya juya yana kallon xuhura a raunane data tsurawa umman ido cike da takaici

yace ba haka bane umma,meeting ne ya tsaidani kan sojojin da xaa tura iraq aiki,a matsayina na babba dole ina wurin shiyasa yau nayi sammako nabiyo ta jirgi amma ayimin afuwa umma.

tayi shiru kamar baxatayi mgn ba sai kuma tace bansan dalilinka na qauracewa hajiya sadiya ba tun wasu shekaru da suka wuce ynxu haka bakasan yarinyarta alhali tana qanwarka

ya sauko daga inda yake xaune ya xauna dirshan gabanta

yace umma ke yakamata ki baiwa sauran mutane bayanin aikina kinfi kowa sanin banida lokaci na kaina akoda yaushe ina qasashe sannan ita kanta momy nayi mata bayanin haka sau da yawa mukan gaisa ta email ko a waya amma yau xnje na ganta faruq yaxo ya kaini.

tace itama yau tabar qasar taje india domin neman lfyr jikinta sai adduar Allah ya dawo da ita lfy.

ya amsa da amin yana kallon xuhura a fakaice ba annuri ko kadan a tare da ita duk sai yaji ba dadi duk sanda xasu xo kaduna hr su koma batada walwala,

mgnr umma ta katsesa wadda tayi masa dirar mikiya a kunne bashi dake xaune a qasa ba hr xuhura dake kishingide kan kujera sai data sumulyo qasa

tace aure xnyima sadiq......ya tsura mata idanunsa danayi jajir lokaci daya xaiyi mgn ta katsesa

bana son duk wata magiya da xakayimin wannan karon,domin baxasuyi tasiri a gareniba aure xnyima ko kanaso ko bakaso cikin wannan satin inaso naga jikokina,inaso naga jininka,inaso naji jikokina xagaye dani shekarunka a ynxu yaci ace kana da ya'ya uku ko biyu.......

yace umma haihuwa da kike gani nufin Allah wata qila matsalar da.......kul ta katse sa cikin tsawa

qarna qara jin wannan Abubakar sadiq, dangina da dangin mahaifinka ba inda mukayi wannan gadon,ko kanaso kanunamin kafini sanin Allah ne?ya girgixa kansa da sauri

tace alfarmar ce baxan samu ba kenan,
yace umma kitausayamin ki cnxamin da wani abu inason xuhura, xuhura *matar sadiq* ce itakadai baxan iya hada soyayyarta da wata ya'mace ba kome kikeso a duniyar nan kigayamin xnyi makishi

cikin daga murya da bacin rai ta miqe tsaye
tace jikoki nakeso xaka iya bani su nan da wata tara ne kome? ashe hr akwai ranar da xan nemi alfarma kaqimin ita sadiq kagayamin mena rasa a rayuwa,tun kafin na haifeka nakeda abina dan haka bbkada abinda xaka bani a duniya bayan biyayya da kulawa, duk soyayyyta gareka da kulawata gareka duk kamantasu yau sadiq,duk dawainiyar danayi dakai tun kana qarami hr kawo ynxu duk kamanta na tabbata da faruq naxowa da buqatata baxai musanyamin ba zai amincemin, ta fashe da kuka mai tsanani,

MATAR SADIQWhere stories live. Discover now