🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
*🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
*ZAINAB NASEER SARKI*
*_ (ZEENASEER😘) _*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸'''Editing by : Ameerah Zarewa'''
*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-REmail:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com*121*
Dafe yaran tayi da hannu daya tare da tura kofar ahankali da shiga dakin tare da sallama.
Gaba daya suka kallo kofar jin sallamarta,hakan yasa ta shiga kallan Shi daga bakin kofar yayinda tasa hannunta ta kullo kofar.
ita kuwa Husna ganin irin kyan da Lailah tayi ga kuma wani Mayan kallo da Dizhwar din yake mata yasa ta zira hannunta daya ta sakalo nashi tare da kwanciya kan damtsensa tana ci gaba da danna wayar tata da hannunta daya.
Murmusa Lailah tayi tare da karasawa cikin dakin.
Yanzu ba'a wajan da yaci abinci yake zaune ba ya canza waje, dan haka gabansu ta karasa tare da durkusawa, cikin sanyin murya ta furta.
_"Anty sannu da zuwa? "_
Ko kallan inda take batayi ba, tamkar bata san da shigowar ta bah.
Hakan yasa ta nuna rashin damuwarta ta maida kanta ga Dizhwar din.
_"Ina yini Rouhi"_
Cikin wani mayan kallo da yake bin jikinta dashi, tamkar be taba ganinta bah ya furta,
_"Lafiya qalau mutanan kano"__"Uhm ya hanya"_
Ta kuma fada tana satar kallan Husna da ta tsaya da abunda take tana sauraran su.Mika masa Yaran tayi tana fadin,
_"Gashi"_Da sauri ya mika hannunsa tare da amsarsa ya sakashi cikin kirjinsa, kallansa kawai yake cikin so da kauna.
Tunda ya amshi yaran ya kama hannunta yana murzawa ahankali, ita kuwa Husna koda ya janye hannunsa da amsar yaran bata bar jikin kafadarsa bah.
Yana san ya ji dumin jikinta amma Yasan bazata yarda ba tunda Magajiya ta gaje wajan.
_"Husna tashi kiga yaran mana"_
Ya fada yana kallan gefanta.Bata dagoba Illah furta,
_"Naganshi"_
Kawai da tayi taci gaba da abunda take.Maida kallansa yayi ga Lailah da itama din shi take kallo.
Babu meyin magana acikinsu, hakan yasa ta amshi yaran tare da ficewa daga cikin dakin, kai tsaye inda suke ta nufa cike da kishi a zuciyarta.
Komawa tayi tare da yaran ta zauna kusa da Zahra suna hira sama sama.
_____
Bayan yan lokuta ya mike tare da daukar wayarsa zai fita daga cikin dakin.Kallansa tayi tare da fadin,
_"Ina kuma zaka"?__"Ban gane bah, dan ke baxaki shiga cikin mutane ba sai nima ki hanani, sallah zanje inyi lokaci ya gabato"_
Dadi ta danji jin masallaci zai tafi dan bata so yace wani dakin zashi dan karya gamu da Lailah.
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR page 105 to the end
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.