💗💗💗💗💗
AUREN SIRRI
💖💖💖
💗💗💗💗💗AYSHA A BAGUDO
Dedicated to
HAUWA A USMAN
( JIDDARH)Page 95
Kanta ta dago ta kalleshi taga duk ya birkice ya fita haiyacinsa ta hadiye abinda taji ya tasomata ya tsaya mata a kirji. sannan ta sauke naunauyen ajiyar zuciya tace eh gidansu nace direba yakaita taga iyayenta kmr yadda nayi mata alkwarin .Amman
ummi Na dauka sai xuwa wani lokaci zata tafi yasoma mgn muryasa cike da zafin zuciya haba first love yazaki bari yarinya ta tafi wannan hargitsartsiyar unguwar tasu me cike da dowatsu alhalin kinsa halin datake ciki yakarasa fadar mgr muryarsa kmr zaiyi kuka .
Da kake wani fushin da daukar zabi akan yarinyar mutane .diyata ce nablah ko taka?
Yadda kake tunanin kana son "dan" dazata haifa maka .
itama hk iyayenta suke sonta km suke bukatar ganinta kusa dasu dan hk kmr yadda nace maka nasa direba ya ka ita gida .
ahankali jikinsa Yayi mugun sanyi zuciyarsa tashiga harbawa da sauri da sauri ya runtse rikitattun idanunshi gam yana jin Babu dadi acikin ranshi ..
tare da kamo lips dinsa na kasa yasoma cizawa da karfi can ya bude idanunshi ya zubawa ummi dake zaune bisa gado tana kallon yaninyasa da nazarinsa .
Muryarsa a sarke yace first love to meyasa kika.
kwaso kayanta ?Nakwashe km nayi hakane domin Na tabbatar da abinda nake zarge akanka deeni .
Wai meyasa Ku maza bakwa iya dannar xuciyarku akan abinda kuke so?
deeni tun ranar dana dawo daga india Na dira Daga airport Na tabbatar da ka kamu da matsanancin mugun son yarinyar nan nablah so km bana wasa ba , sosai ka nitse 'cikin kogin sonta .
" deeni kafi son yarinyar nan fiyye da zeenat sannan km kana yiwa yarinyar nan wani irin mahaukacin so .Da wani irin mugun sauri ya dago da rikitattun idanunsa ya zubawa ummi sosai yana mata wani irin kallo me tsoratarwa sannan da mamakin mgnrta saman fuskarshi .
Eh deeni bazakataba Gane hakan ba sai lokacin Yayi .
Amman ka rigada ka fada son yarinyar nan tunda har ka iya marin zeenat agabana akanta batare ko shakkata ba .
km ka rungumi matarka agabana deeni ka kwantar daita akan kirjinka hkn ya tabbatar min da bakaramin so kake yiwa nablah ba.ni dai koda zamanku zai daure daita fatana dan Allah dan annabi kayiwa diyata zeenat adalci karkaga wannan itace uwar ya'yanka itace me haihuwa sannan ka wulakanta min zeenat ko byn raina banason ka wulakanta min ita .
dan hk ka natsu ka kwantar da hankalinka da kyau akan 'cikin jikin nablah Allah ne yabaka 'cikin jikinta km shine me tsare bayinsa .
" inshallahu da kariyarsa nablah zata haifamaka abinda ke 'cikin ta.A hassale muryarsa Na rawa yace ni duk ba wannan ba tunda nace kartaje ba sai a hakura ba idan lokaci hk Yayi da kaina zan kaita uhmmmm sannu ubanta mlm salisu .......
yau wata nawa rabon yarinyar nan da iyayenta kada ka mata ita kanta nablah bazataso zama tare da iyayenta ba a halin datake ciki .
Km ma Muyi daita yau din nan zata dawo .... zuciyarsa a hassale km muryarsa can kasa kasa yace first love nidai gsky banso tafiyarta ba. sannan km mgnr wai Ina son yarinyar nan komai komai.... shima ba hk bane first love domin ni nasan zuciyata nasan abinda take so da wanda bata so . banasonta yarinya idan har. Na afka sonta ta yaya bazan gane ba yakarasa fadar mgnr tare da juyawa fuuuuuu yasoma tafiya ranshi abace ya bar gidan ummi tayi murmushi irin Nasu Na manya deeni kennan ne rikicin gangan Allah Yayi maka albarka tare da sanyaya maka zuciyarka ..Hayaniyace ta kure 'cikin gidan mlm salisu da murna da kururuwar ganin nablah gabadaya duk wanda ya kalli fuskokin ahalin gidan murna suke da farincikin ganinta ..
YOU ARE READING
AUREN SIRRI COMPLETE
Mystery / ThrillerMatar shi ce ta farko bata san haihuwa, idan ta samu ciki sai ta zubar, as ending yake yin auren sirri da mai aikin gidan