_*® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S P.M.L*_ 💭💭💭
💞💞💞 💞💞💞
*BURINA*
💞💞💞 💞💞💞
©
*ZULAYHEART RANO*💞*Dedicated to AYSHA ALIYU GARKUWA*
*Sorry don Allah jiya na yi mistake din page zan sanya 27 sai na sa 26, in sha Allah yau zamu tashi daga 28*
_Ku sanyani cikin addu'a bana jin dadi._
2⃣8⃣
Wani kallo ta jefa masa wanda ya shi yin shiru, taɓa wa ta yi ta gefensa ta shiga cikin shagon tana amsan masa ta fito rai a matukar ɓace, da ido ya bita hannunsa dafe da saitin zuciyarsa ji yake kamar zata faso kirjinsa ta fito, yana kallo har ta shige cikin motar direban ya ja, jikinsa ya yi sanyi sosai yana matukar dana sanin abin da ya aikata mata, shi ko kaɗan bai ji haushin marin da ta yi masa ba hasalima kansa ya bai wa laifi domin shi ya saya. "Ke lafiya kike ta wani fushi ko ciwon kan ne?" Umma ta jefa mata tambaya tana ci gaba da kallonta. Mtsww ta ja siririyar tsaki ta ce "wannan ɗan rainin wayan ne Alhaji sai bibiya ta yake kamar tsohon maye, Ni kuma dana gaji na zabga masa mari." Ta k'arasa maganar tana juya kai.
"Mari? Alhajin kika mara?" Babu alamun dariya a fuskar Umma ta yi wa Zainab tambaya. "To Umma sai famar bibiyata yake fa." "Shi ne kika mareshi da yake baki da hankali ko? Yanzu kina nufin Alhaji bai isa ya ci darajar Fawzan ba kenan, a naki tunanin idan Fawzan ya taso ya ji kin taɓa marin mahaifinsa zai ji dadi to wallahi bari ki ji idan na kuma jin makamancin haka sai na mugun saɓa maki kina jina ko?" Sosai Zainab ta firgita da yanayin Umma, take nadama ta saukar mata sai yanzu ta ga sam bata kyauta ba a hankali ta ce "Ki yi hakuri Umma zuciya ce ta ɗauke ni shi yasa, amma in sha Allah ba zan kara ba." "Yin haka kaɗai shi zai hana ki shiga fushi na." "Bazan kara ba ki yi hakuri." "Ya wuce." Umma ta faɗa.
A haka suka isa gidansu a gyare suka samu gidan domin kullum masu aiki cikin tsaftace shi suke, wanka Zainab ta yi ta yi wa Fawzan ta sanya masa kayan shan iska domin ana dan zafi, abinci ta dauko daga kicin ta nufi falo kusa da Umma ta zauna tana faɗin "sannu da hutawa." "Yawwa." Umma ta amsa a dakile. "Inna lillahi Umma fushi kike yi da ni don Allah ki yi hakuri." Ta ida maganar hawaye na zubo mata, Zainab ta lura fushi Umma ke yi da ita domin tun a mota ta ɗauke mata wuta, ko da suka shigo da Fawzan da Usman take magana sam bata farga ba sai yanzu. "Bana fushi da ke Zainab ina dai son ki gane menene rayuwa dole sai mutum na hakuri da komai, sam abin da kika yi wa Alhaji bai dace ba ki yi masa duk abin da zaki yi domin ki kwaci yancin ki amma kada hannunki ya kuma kaiwa jikinsa da sunan duka." "Allah Umma na yi maki alkawari bazan sake ba." "To naji ki ɗauki abinci ki ci." To Zainab ta amsa tana cin abincn, bayan ta gama ne take cewa Umma ɗazun Rufaida ta yo min waya ta ce min tana zuwa." "Allah sarki Rufaida yarinyar bata da matsala Allah ya kawo ta lafiya gobe zan je wajen Hajiyarta." "Allah ya kaimu" Murmushi Zainab ta yi don tasan zuwan Rufaida mai amfani ne sosai take murna da zuwan ta, karfe biyu Rufaida ta zo bayan sun gaisa da Umma sai suka kule cikin bedroom da yake Usman ya ɗauki Fawzan sun shiga gari.
"K'awata ya kwana biyu wallahi duk na kosa ku dawo domin mu san mafita, saboda na samo wani waje kuma zaki ji dadin wajen sannan zaki samu abin da kuke so fiye da tunani." "Um Rufaida kenan Indai kan maganar nan ce ki barni kawai yanzu a halin da nake bana jin zan kuma rayuwar farin ciki na rasa Ik mai sona ina cikin wani hali." "Haba ki bar yin wannan maganar Please, IK ya mutu yanzu dole mu fuskanci gaba ina son ne ki zama babban mace mai class Wacce duk wanda ya kalleki sai ya kara musamman Alhaji yake kowa?" Murmushin takaici ta yi ba tare da ta ce komai ba tana dai ci gaba da sauraron bayanin Rufaida, ci gaba da bayani ta yi har sai da Zainab ta amince "yawwa yar gari kinga gobe sai mu shiga kasuwa ki sayo kayan da za ki yi amfani da su, kuma na sama maki wajen da za ko yi kwalliya duk kalar da kike so." "Ina godiya." Sosai Zainab ta ji dadin bayanin Rufaida domin a duniya babu wanda take son ko yawa hankalin kamar Alhaji don taga take taken sa.
Rufaida yarinyar yayan Umma ce, budurwa ce kyakkyawa mai nutsuwa da hankali, Macace yar gayu wacce ta iya kwalliya, tun zuwan Zainab Allah ya haɗa jininsu duk kusan wayewar da Zainab ta yi Rufaida ke koya mata wani shigar, a lokacin da cewa take tana jin kunya amma yanzu tunda ga burinta sai ta aje kunyar a gefe domin ta kwatowa kanta yanci.
Aiko washegarin suka tafi kasuwa sosai suka jido kaya basu shigo da shi cikin gida ba sai da suka biya wajen tela suka bashi dinkin, a gajiye likis suka koma gida a falo suka zube suna fadin "washhhh! "Ai dole ku yi washhhh tun fitar safe sai yanzu?" Umma ta yi tambayar tana tsare su da ido. "Wallahi Umma tunda muka fita muna cikin kasuwa sai shagon tela kaɗai da muka biya." "Sai ku tashi ku yi wanka ga abinci can a dining." Tana gama faɗin haka ta yi gaba. Abinci suka soma ci sannan suka yi wanka bayan sun yi salloli suka shiga bude kayan da suka sayi, kaya ne masu shegen kyau da tsada gyaluluwa da takalma dogayen riguna kai kaya dai masu kyau gefe guda kuma costimetic ne dangin su turaruka mayuka pawdar da sauransu.
A lokaci ƙalilan Zainab ta kara canzawa ta yi wani irin kyau na musamman, har wani class ta yi duk inda ta gitta sai an kalleta, da yake har rejista ta yi a makarantar koyan kwalliya aikam ta iya, babu abin da Ya dameta tama manta da wani Alhaji harkokin ta kawai take yi.
****
Bangaren Alhaji kuwa da kyar ya iya kai kansa gida, lokacin Daddy na zaune yana karatun jarida a razane Daddy ya kalli Alhaji ganin a yanayin da ya shigo "kai Alhaji lafiya?" "Zainab! Zainab!! Daddy." "Wacece Zainab?" "Dadd kirjina please ka danne min zai fito." Da kyar ya iya karasa maganar numfashin sa ya yi sam, sosai Daddy ya firgita da halin da Alhaji ya shiga wayar yayanshi ya kira baya ya sanya Alhaji cikin mota yana tallafe da shi, yana zuwa yaga halin da yake ciki bai tsaya tambaya ba yaja sai asbiti, cikin gaggawa aka shiga da shi likitoci suka duk'ufa kansa don ceto ransa amma ina abin ya gagara. Iya tashin hankali Daddy ya shiga sai kaiwa yake yana komowa.Likitocin ne suka fito suna niyyar wucewa, cikin sauri Daddy ya bi bayan ɗaya daga ciki yana tambayarsa ya jikin Alhaji "sai godiyan Allah, amma tabbas yaronka yana bukatar addu'a." "Allah ya bashi lafiya." "Amin zuwa anjima idan ya farka sai musan yadda zamu yi." Jiki a sanyaye Daddy ya shiga dakin da Alhaji ya ke yana kwance kamar babu rai babu inda ke motsi a jikin, girgiza kai ya yi ya ce "Allah ya baka lafiya kai kuma wannan ita ce irin taka jarabawar Allah yasa ka iya cinye wa."
*Ku yi maneji da wannan wallahi bana jin dadi sam, zazzafan zazzaɓi ne ya rufeni.*
*RANO*✍

YOU ARE READING
BURINA COMPLETE
Romancelabarin BURINA labarin Zainab (Zee) da Khalil ( IK) da Abdallah (Alhaji) labarin soyayya ban tausayi da nishaɗi.