Mai Nasara 170-175

1K 69 3
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 170 ➡ 175

Washe gari koda suka tashi atare suka fita masallaci. Baffajo da Maina da suka gansu sai da sukayi mamaki. Baffajo ne bayan an gama sallah suna gaisawa yake tambayar su ko a wajen Baffa Barkind'o suka kwana? Baffa Barkind'o yace  ai kuwa nine nace amun kwanan bankwana kasan yau Mai Nasara a gidanshi zai kwana.

Murmushi Maina yayi aranshi yace lallai kama kwanan bankwana sukayi maka,  dan kai dasu iya na yau ne kawai. Mai Nasara yace Hamma jiya ba'a tashi wasa da kai ba kuma. Maina yace wallahi kuwa,  ina cikin kallo wani abokina da mukayi makaranta dashi ya kirani akan yazo,  shine fa naje muka gaisa, mun dad'e dashi muna fira kafin muka taho dashi dan yana so yazo yaga wasan,  muna zuwa kuma muka iske an tashi,  shine yace wucewa zaiyi.

Majidad'i yace gaskiya kallo ya barka. Baffajo yace amma yau dai ai baza'ayi komai ba ko?  Mai Nasara yace Baffajo ai ya isa haka kuma gara kowa yaje ya huta. Murmushi Baffa Barkind'o yayi yace kai dai fad'i gaskiya.

Baffa Lamid'o ne ya iso wajen su,  nan suka gaishe shi shima ya gaishe dasu Baffa. Majidad'i yace Baffa jiya kuma sai kajimu shiru ko?  Dariya Baffa Lamid'o yayi yace ai dama nasan jiya bazan samu 'yan fira ba shiyasa kawai muka kwanta.

Mai Nasara yace ai Kaku's nasan sai tayi k'orafi akan rashin zuwan mu. Majidad'i yace ai Kaku's akwai son labarai. Baffajo yace dama tunda lokacin biki yazo ai dole kowa yayi hak'uri har sai komai ya wuce sannan.

Tab'e baki Maina yayi yace Baffajo nidai nayi gida kafin gari ya k'ara wayewa nad'an runtsa. Baffa Barkind'o yace ba dai zaka dena wannan baccin asarar ba ko?  Nasha fad'a maka baccin bayan asuba baccin asara ne,  gara kazauna kayi karatu ko kuma kayi lazimi. Sosa kai Maina yayi yace zan dai na Baffa Barkind'o. Baffa Lamid'o yace ai gara adaina, sam baida amfani.

Nan suka wuce suna fad'in bara mushiga ciki. Baffa Barkind'o yace shikenan har kun tafi kuma?  Majidad'i yace Baffa wani aiki zamuyi ne. Baffajo yace aifa,  aiki ya samu.

Kai tsaye gidan Baffa Lamid'o suka wuce. Zinatu (Kaku's)  tana kok'arin dama fura suka shigo,  Majidad'i ne yace haba Kaku's,  yanzu haka zanyi aure na kaiki gidana kirik'a tashi tun kafin gari yawaye kina damun fura?  Murmushi tayi tace ja'iri,  ko Uwarka Ammah da fura take karyawa duk safiya,  lokacin tana yarinya tana tashi furarta tana gefe.

Dariya Mai Nasara yasa yace Kaku's ki rabu dashi,  ko budurwa baida ita yake maki maganar mata. Kaku's tace ka barshi inaji da Khalcume zan had'ashi. Turo baki Majidad'i yayi yana fad'in haba dai,  ai Khalcume tamun k'arama,  kibar ma fad'i kada taji ta rainani.

Dariya sosai Mai Nasara yasa yace amma wallahi Kaku's kin iya zab'i,  kinga dole yarik'a bani girma. Majidad'i yace kunga kudaina fad'in wannan maganar tun kafin Yusuf ya jiku,  sanin kanka ne shine yake sonta.

Kaku's tace lallai abu yayi dad'i. Majidad'i yace amma fa kisama bakinki sakata koshi bai fad'a mata ba,  yace sai ya kammala karatu sannan. Kaku's tace ai kaima kasan bana cikin masu surutu,  sai dai muyi fatan zuwan lokacin. Mai Nasara yace tashi muje naga kana had'iyar miyau kuma ba baka zatayi ba. Majidad'i yace Allah ya kyauta nasha Fura tun da safe. Fita sukayi suna dariya.

Haka suka zagaya duka gidan suka gaishe da matan gidan,  daga k'arshe suka nufi wajen Hajjo. Sun dad'e suna fira har abinci acan sukaci tare da Maina sannan suka nufi b'angarensu sukayi wanka saboda abokansu duk sun taho na nesa saboda d'aurin auren na k'arfe biyu ne.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now