Page 11 to 15

92 1 0
                                    

    

*January 2017*

*WANENE SS TAFIDA*

""Ss tafida shararren d'an siyasa ne, mai ji da dukiya, asalin sunan sa Alhaji sulaiman salisu tafida shine ake kiran shi da Ss tafida ya samo sunan ne tun yana k'arami abokan sa a school suke kiran shi da haka,shine kawai sunan ya bishi har girma

Yana da mata guda d'aya mai suna khadija hajiya khadija cikakkiyar y'ar kasuwa ce, bata cika zama sosai a gida ba, suna da yara guda 5   hud'u mata d'aya na miji sai cousin brother d'insu mai suna fadil,
Fatima itace babbar d'iyar ss tafida tana saudiya tana aure sai fahad mai binta shi kuma yana ingala yana masters d'inshi sai noor ita ke binshi sai nabiha su kuma suna neal universty dake garin abuja sai autarsu kausar wadda keda shekara 3""

""Ss tafida yana da k'azamin kudi don shi kanshi bazai iya lissafa irin dukiyar shi ba yana da kamfanin guda biyu da ake jakunkuna masu kyau da tsada a kogi state snn yana da kamfanin da ake wayoyi a dubai snn ana kawo masa motoci yana saidawa yana kuma da gidajen mai na kanshi guda uku d'aya a bauchi d'aya a kaduna d'aya a nasarawa state""

""Ss tafida yayi governor yayi sanata shekarun baya da suka wuce yanzu yana neman shugaban k'asa
Kuma ya tsani talaka baya son talaka ko na minti d'aya
tow readers kunji ko wanene ss tafida ku biyoni gaba zakuji ko wacece malika nd ambassador Binta""

""Malika ce zaune a d'akin da aka bata ita kad'ai ce ba'a had'ata da kowa ba kayan ta ta soma cirewa a cikin gana masgo d'in ta tana jerawa cikin wardrobe wani book d'an  karami naga ta d'auko tayi ticking da red biro tana wani shu'umin murmushi,

"""Jin k'aran bude k'ofa tayi  sauri ta rufe book d'in tasa a wadrobe, Asabe tagani mai girkin gidan ta shigo rik'e da abinci a hannun ta, da murmushi malika ta k'araso ta kar6i abincin tare da cewa dakin bari na zo na d'auka da kaina,a'a babu komai Diyana ai ance bak'on ka Annabin ka , haka toh na gode ,babu  komai barin je kar hajiya ta nemeni, ta fice tana fita malika ta aje abincin kan table taci gaba da gyaran kayan ta,
Sai da ta gama duk abun da zatayi snn tayo alwala tayi sallar magrib snn taci abincin ta gama ta haye gado ta fara dailing numbar din ummi bugu d'aya ta d'aga, sunyi hira sosai sannan ta kashe tayi addu'a ta kashe light d'in d'akin ta fara bacci
cikin bacci taji kamar ana kiran  ta bud'e ido tayi taga ahlam tsaye a kanta zumb'ur ta mik'e tace ya akayi fuska a tamke tace ki tashi 6am tayi hajiya na neman ki kuma dokar gidanne duk wata yar aiki 6 nayi tagama bacci, wani mahaukacin kallo malika ta jifeta dashe toh fa ni ai lokacin da nazo hajiya bata sanar dani haka ba don haka banga wanda ya isa ya sani tashi 6 ba,to nidai na sauke hak'k'i idan yaran gidan suka miki wani rashin mutuncin babu ruwana, ta wuce ta fita murmushi malika tayi, rashin mutunci lallai ko zasu d'aukowa kansu dala ba gamma ai ni nafi k'arfin rashin mutunci don ni harda na saidawa ina dashi ,
amma zan musu uzuri na kwana biyu taja bargo ta koma baccin ta""

10:30

""Nabiha ce ta sauko daga sama tana k'walawa ahlam kira jiki na rawa ahlam tazo,"na'am anty gani"  yawwa ina wannan yar aikin da aka kawo jiya Diyana take ko wa?" Inda inda ahlam ta fara yi nabiha ce ta daka mata tsawa "badake nake ba",au ......am ......tana d'aki tana bacci ",bacci kuma baki sanar da ita dokar gidan nan bane? ", kanta a k'asa tace na fad'a mata" ,ok kin fad'a mata shine tayi kunnan shegu lallai yau zata gane kuren ta".

kitchen ta shiga ta d'auko ruwa mai k'an kara tayi d'akin malika, tana shiga ta watsa mata a firgice ta mik'e tana fad'in subhanallah wani d'an kutumar uban ne ya zubamin ruwan sanyi a jiki.,"yar masu gida ce ta zuba miki" nabiha ta fad'a a tunzure ,kallon ta malika tayi kawai tayi murmushi a zuciyar ta tace yarinya baki san ko ni wacece ba amma muje zuwa ta mik'e ta shige toilet ,tabar nabiha gurin a tsaye kuma bata bata hak'uri ba,
mamaki abun ya ringa bawa Ahlam a zuciyar ta tace lallai Diyana yar tasha ce ,rai a b'ace Nabiha ta fita tare da cewa "ahlam idan ta fito kice mum na kiran ta kuma ki kawo min tea d'aki ina jiran ki, " toh kawai Ahlam ke cewa.

FANSA RIVENGWhere stories live. Discover now