👭MATA MA ABUN
ALFAHARI NE👭👭📝Ummu Asma'u(Sa'adatu)
Sadaukarwa Ga Mahaifana, Allah yayi maku Rahama.
Bismillahi Rahamanirrahim.
Page3⃣0⃣
Mumy na kwance daki, Fatima tayi sallama ta shigo, Mumy tace bak'on ya tafi? Fatima baki ta turo tace Mumy na bar sa Falo, in na fadawa yaya da Anty bana son sa wallahi, haushi ma yake bani.
Mumy dariya tayi, yanda Fatima tayi magana k'urciya zalla, tace ki kwantar da hankalin ki Fatima, ki rok'i zafin Allah kin ji.
Fatima tace to Mumy, zafin ya Ak shine zafina duk wanda yake so, shi zan zafa, yayi min gata rayuwa ta.
Mumy shiru tayi, a ranta tace, da wani ne ya zafa maki Fatima abin zai zo da sauki, matsalar shi ya zafa ma kansa, nasan ko ke ki ka fahimci nufinsa zaki tsane sa.
Fatima littafan ta dauko zatayi karatu, don lokacin baifi wata biyu ta rubuta SSCE ba, ita ma anyi mata jumping kamar Hauwa'u, suna da k'okari sosai, baiwar da Allah yayi masu, mahaifin su ya kasa ganewa.
Mumy ma bata k'ara cewa komai ba, wani lokacin takan rasa sanin wane irin tunani zata yiwa wanan lamarin, zata fadawa Allah ya kawo mafita ta alhairi.
Fatima na karatu text din Ak ya shigo, da num da batasan ko waye ba, murmushi tayi, don ta haddace num tsab a kanta.
Tun abin na bata tsoro, har ta kai tana responding text din, baya kira, ita ma bata tafa kiran num ba.
Tana murmushi tana karanta text din, kallaman sun mata da'di, ina ma zata gan sa ido da ido.
Tura masa tayi 'same to me'.
Ak na aiki kan laptop sakon ya shigo, ido ya bude yana karantawa, sai da ya kara diba num ya tabbatar na Fatima ne, wani da'di yaji a ransa, ta fara son sa kenen.
Fatima rike take da littafi, tana, tunanin ina zata ga mai num nan, kallamansa na birge ta, tana son ganin sa a ido, ko zata yi masa magana su hadu?
Matsalar ina zasu hadu, batasan ko lagos yake zama ba, ko ina ne? In tace yazo school din kar su hadu da Ak.
Akwai wani park nan kusa ga gidan su, zata ce su hadu wajen, zata yiwa Anty Hameeda k'arya zuwa gidan su joy yar class din su ta aro littafi sai taje wajen.
Gefen da Mumy ke kwance ta kalla, Mumy har tayi bacci, num ta turawa text, tana son su hadu.
Ak na rike da wayar wani text ya shigo, yaga Fatima tace tana son su hadu, dariya yayi yace zamu ko hadu my fati.
Tura mata yayi ina take son su hadu?
Jin karar sako da sauri Fatima ta diba, ganin yace ina zasu hadun.
Ta tura masa in yana lagos su hadu a pack din dake kusa ga jewell internation school victoria iland, gobe d karfe hudu.
Ak yana karanta text yana murmushi yace zanje ko, zaki gani Fatima.
**** ****
Malan Garba ya iso cikin garin sokoto sai zancen zuci yake yi, yasan duk abinda yasa Inna Fatima barin gidan Mamman ba k'aramun abu ne ba.
Saukin abun Malan Mamman yace bai sake ta ba.
Gefen hanya ya sauka, ya hau achafa zuwa gidan Gwaggo.
Koda ya isa gidan, Gwaggo ta dawo zata kintsa ta koma asibiti, Tabawa tayi, ta zauna gida, ita zata kula da Khadija Gwaggo tak'i.
Dole suka barta, taje gida ta kintsa ta dawo asibitin, Tabawa ta bari da Hauwa'u.
YOU ARE READING
Mata ma Abun Alfaharine completed
FanfictionGirl child descrimination Gender Inequality Passion