Mr & Mrs Fawaz

32 4 0
                                    

Mr&Mrs Fawaz
❣❣❣❣❣❣
https://my.w.tt/2PpalXNbG0

16.

Da faduwar gaba fawaz yayi sallama cikin gidan nasu fahad yana bayansa amsa musu dady yayi tare da tambayarsu ya mai jikin dan sun sanar da iyayen nasu da suka hadu a masallaci da sauki fahad yace fawaz kuwa tuni ya masa sallama ya dau hanyar dakinsa shima fahad sallamar yayi masa sannan ya wuce nasa dakin daka kai daddy yayi yace kamarsu irinta ta mahaifinsu ce marigayi aliyu mai nagge amma haske da yanayi irin na mahaifiyarsu ne har zafin kan fawaz din na mahaifiyartasu ne ba abinda ya bari sai dai akwai su da kyan zuciya duk da halin ko in kula da rashin kyautawar da mairo take musu basu taba tankamata sunyi hayaniya ko su sanar dashi ba duk da shi din yana sane da komai ni indo nace hmmmm rashin sani aikuwa fawaz yana tqnkawa.

Umma naje sunce bataxo ba cikin mamaki umman tace ni bata cemin zata je ko Ina ba gashi har an fara kiran magriba bata dawo ba kallon mariya tayi tace dau buta kiyi alwala kiyi addua Allah yasa lafiya kinji autar ummanta to Mariya ta amsa tare da daukar butar alwalar tayi kamar yadda umman tace itama alwalar umman tayi tare da yin sallar nan ta dinga addua Allah yasa alkhairi ya kuma dawo mata da diyarta lpy ranar dai umma tana cikin tashin hankali.

Bayan sallar isha'i kawu bello ya shigo gidan kallon Mariya yayi yace ke ina saadatu cikin rawar murya tace bamu ganta ba muma nemanta mukeyi dariya ya kwashe da ita yace yanxu iskancin nata har ya kai bata dawowa gida tab Allah ya kyauta Allah kuma ya raba danginmu da abin kunya wallahi Aminu baiyi dacen mata ba balle kuma yaya nan dai ya kare musu tatas ya fita daga gidan,umma ranar kasa bacci tayi cikin dare tana zaune tana addu'o'i Allah ubangiji ya kare mata yarta a duk inda take dan ita dai tasan ba lafiya haka kuma jikinta yana bata akwai damuwa cikin hawaye tace Allah ya tsare min ke saadatu ya dawo min dake lafiya yata.

                Wacece saadatu

Ayshart sani
Wattpad@ayshartuh

Mr&Mrs FawazWhere stories live. Discover now