🌀🌀🌀🌀🌀
*HIDAYAH NOOR*
🌀🌀🌀🌀🌀*Story~Written~Edited*
*_By Mss Xerks_*🌺*Devoted to Ummi Aisha*
*_2018/2019_*
بسم الله الرحمن الرحيم...
*AISHA TAWAJENA XUMUNT@ NOVELL@ Kema ganaki..tnx alot 4ur love,care and support...*
*25*
Washe gari tinda wuri Inna tace su tashi a fito da kaya kar masu aiki suzo ana ɓata masu lokaci.
Kamin rana ta fito sosai duk sun fito da komi nasu nan tsakar gida,akwatunan Hidaya kuma aka miƙasu gidan Umma Zakiya.
Ƙarfe goma masu aiki sukai sallama ƙofar gidan Inna.
Inna ce tace da Hidaya ta leƙa tace masu ana zuwa .
Kasancewar jiya Ammar bai samu yay isashshen bacci ba hakan yasa yau bai tashi da wuri ba.
Sai ƙarfe 9:30 tukunna ya farka,yana zaune da ƙur'ani yana karatu wayarsa tai ƙara.
Miƙa hannu yay da sauri ya ɗau wayan ya ɗaga kiran ganin sunan Hidaya jiki.
Da sallama ya kara wayar a kunnesa.
"Awali jam Hamma na""sai jam"
"afini jam"
"saijam noi Inna'ƴan""bejandi,pelem kan komayi'i minoduma wadobe gollar wari"
"To to giaimo imiwara mi ummaki lallau wari kan watti mijottaki"
Daga haka suka katse wayan ya miƙe ya shiga wanka.
Sauri2 yay ya fito ya shirya cikin milk ɗin yadinsa ya fita.A ƙofar gidan ya sami masu aikin zaune kan dakali suna jiran zuwansa.
Sallama yay masu tare da miƙa masu hannu suka gaisa.
Kuyi haƙuri dan Allah na tsaidaku bara musamu mai napep yaje ya ɗauko mana katakwayen ko.
Ba damuwa bari ma kawai muje da kanmu tinda ba nisa.
To Ammar yace dasu ya shiga cikin gidan.
Ƴar dariya yayi ganinsu Inna curko a tsakar gida.
Tsugunawa yay ya gaida Inna da Adda.
"yana ganku tsaye Inna"
"umm kai muke jira dama da tini ma mun tafi gidan Zakiya...Kaga mutanen sunzo da wuri babu daɗi mukuma mu tsaidasu"
"wlh nima ban tashi da wuri bane shiyasa"
"to yanzu mudai bari muyi can gidan Zakiya in suka gama sai mu dawo ko...Allah sa kar ai ruwan sama ya ɓata mana kaya"
"amin dai..dake ma suna da saurin aiki yanzu zasuyi su gama insha'allahu"
Tinda ya shigo idon Adda ke akansa.sosai take jin ɗan'uwan nata aranta ko kaɗan bata ƙaunar ganinsa a damuwa.
Tinani take mai yasa lokaci guda Ammar yay wannan ramar haka gashi tayi2 ya faɗa mata maike damunsa yace ba komi tsananin faɗuwar gabane kawai.
Inna ce ta katse tinanin nata da"kinga Halima miƙo masa furarsa da fanke"
to Adda tace ta ɗauko wani kwanon shan ruwa da Furar ke aciki sai fanke dake aleda.
Inna ta miƙama ta amsa ita kuma bayan ta daɗa juya furar ta miƙawa Ammar.
"gatanan yau ba'a samu anyi kunu ba nasan kana sonta shiyasa nace adama"
YOU ARE READING
HIDAYAH NOOR completed.
Historical FictionHidayah Noor labari ne daya ƙunshi soyayya, butulci, sakayya da kuma ɗaukaka.