KYAN DAN MACIJI.........
By Zulaihat Aliyu Misau
Part 5
Wattpad@zulaihatualiyumisau
🐍. 🐍
No comment, no vote, no update on time, eheee...
His brother,Big Dog He is mafian. Duk wani bad boy daya kwana ya tashi a garin nan shine ogansa. Yanada daurin gindin manyan kasar nan, ina nufin manyan yan siyasarmu, musamman na nan Lagos, don yana musu aiki sosai. Ina nufin duk wani aiki na taaddanci daya taso, shi ake ba, shi kuma yasa yaransa. Shiyasa ko an kamashi baya daukan lokaci an sakoshi, haka yaransa. Kannansa biyu jimoh sai Ajibode (Don). Big Dog naji da Ajibode sosai, wannan yaba Ajibode cin karensa ba babbaka. Kowa na tsoron taba shi, saboda haduwa da Big Dog."
Kallon Florence khairat tayi " kuma kikace he's dengerous, how?" " in ka taboshi you'll see, waya kawai zai yi, yanzun nan zaki ga yaran Big Dog, sun iso, don school din nan akwai yaransa sosai, in kuma ya tsani mutun to ka shiga uku, in bakayi wasa ba sai dai ka bar school din. Differen dinsu da Victor kawai shine, victor kowa yasan he belong to cult. "
" I'm very scared." Khairat ta fada tana kallon Sabrina dake duba text book har lokacin.
Dariya Florence tayi " my only advice for u, shine Ku fita hanyarsu. Koda yake naga kawarki nada farin jini sosai, tunda in just few weeks ta kama zuciyar 2 dengerous. And some others. Just make friend with Don, hakan zai baki kariya daga sauran dangerous guy's din school din nan, San nan nasan victor ma zai yi nesa dake, in ba haka ba Gaskiya I'm sorry to say u a in big trouble." Wani kallo Sabrina tabi Florence dashi, alamar " baki da hankali." Dariya Florence tayi ta mike tana gyara zaman mini skirt din dake jikinta. " I said my on woo!!!!." Ta tafi
Khairat ido ta zubawa Sabrina kana kallonta kasan bata cikin natsuwarta " sab ya zamuyi ne wai? Nifa har school din ta fita a raina, tsorona Allah tsorona guy's din garin nan, most of them a bad." Mikewa Sabrina tayi ta fara tattara kayanta cikin wata cute bag " let go in sha Allah ba abinda zai faru. A bu daya na sani duk wanda yace min kule zan ce masa cas, don ni basu isa inji tsoronsu ba, wallahi sunyi kadan." " aa sab! Please try to understand. " katseta sab tayi, ta hanyar daga mata hannu. Shiru tayi, ta dau Jakarta suka fito.
Suna tsaye a dai dai inda suka saba hawa cap, wata hadaddiyar black jeep data sha tilted ta faka, ga music na tashi kamar zai tsaga motar saboda yadda aka kure volume. Hannun khairat taja suka kara matsawa gaba kadan. Kofar driver aka bude Don ya ziro kafafunsa da sukasha wasu kofta- koftan White combos masu matukar kyau, da wandonsa three quarter dayasha tsage- tsage shirt fara mai yankakken hannu kamar singlet ga uban sarkoki wuya da hannu, abun baa cewa komai. Cikin takun kasaita da niganci ya tako zuwa inda su Sabrina suke tsaye." hy!!! Beb.!!." Ya fada yana gyara zaman P- cap dinsa. Khairat ce tayi karfin halin amsa masa da " hy!!!" Bayan ta hadiye wani busashshen yawu.
Sabrina kam kallo daya ta masa ta kauda kanta. " in ba damuwa muje inyi dropping naku, kun wuce tsayawa a nan." Ya fada yana karewa wurin da masu tsaye a wurin kallo. " take your poking car and live that place, we are not interested. " Sabrina ta fada tana banka masa harara. Murmushi yayi yana dafe kirjinsa " what a melodious voice😍!" Harara ta kara aika masa. Ta ja hannun khairat suka kara gaba, da sauri yabi bayansu. " don't be stubborn mana,." Cab ta tsayar da sauri suka karasaDriver Cap din beyerabe ne, so Sabrina bataji abinda Don ya fada masa ba, sai gani tayi ya figi motarsa yayi gaba. Haka tayita tsaida Cap yana korarsu har gari ya fara duhu. Cikin gajiya da kaguwa khairat ta ce " please sab let him drop us, I'm totally tired of all this. " ita kanta Sabrina hankalinta ya fara tashi, ga phone dinta ya mutu ba charge balle ta kira azo a dauketa, tasan yanzu haka yayanta ya dade da komawa gida, hakan na nufin hankalinsa ya tashi tunda bata taba dadewa haka ba, kuma ga ba phone. Khairat ta manta da phone dinta a gida balle suyi anfani dashi. Da phone dinta sukaita amfani shi yasa charge yayi saurin karewa. Don ta kalla dake jingine da motarsa yana danna waya lokaci - zuwa lokaci yakan dago ya kallesu. Shi mamakin taurin kanta yakeyi, sai dai abu daya ya Sani ya fita taurin kai da kafiya, tunda yasa ransa kaita gida baiga abunda zai tsaidashi kan kudirinsa na kaita gida. Tsaki Sabrina ta ja ta kalleshi cikin kallo mai cike da harara da takaici.
Kofar gaba ya bude mata, yana murmushi
Khairat ta bude baya ta shiga. Sai da ya tabbatar ta zauna da kyau, ya rufe kofar ya zagaya yaja suka hau titi sosai. Cikin karfin hali irin na Sabrina, hannu tasa ta rage music din, tare da gyara zamanta. Shiru ne ya biyo baya na wani lokaci, kafin ya juyo yana kallon Sabrina " I'm Ajibode layemmi fayo." Tabe baki tayi, tare da fari da idonta, ba tare da ta kalleshi ba, balle yasa ran samun amsa. " Bonkole oki street lakki phase 1, I hope u known the place?" Ta fada tana kallon window.
YOU ARE READING
KYAN DAN MACIJI ( Completed )
Romanceyana dauke da fada karwa, nishadan tarwa, ilmantarwa, soyayya. akwai sakonni da yawa a cikinsa. in bakya comments ko vote! please don't read my story.