P46

600 43 4
                                    

💕 *NOORUL* 💕
      (Haske nah)

By
*Salmerh MD*

*_Marubuciyar littafin CAPTAIN ABBAS_*
 

*Wattpad @*
*Serlmerh-md*

💫 *DA BAZARMU* *WRITTER'S ASSOCIATION*
💫
We are here to make you happy,smile,educate and to realized that we are the best among all.....
*DA BAZARMU* *MUKE TUN'KAHO*

*Bismillahir* *Rahmanir Raheem*

🅿 *46*

*Bayan wasu kwana ki da komawar su makarantar*
       Komai ya gama dai-dai ta tsakanin su, rayuwar su suka cigaba da shimfi'dawa son ransu duk sun manta da damuwoyin da suke ciki kowa ya saki ransa..musamman ma Deen da dama shi abin yafi tsaya masa a rai.

*****
    Ranar ya kama ranar Monday ne kuma lecture 'daya yake da shi na safe...yayin da Husnah sai 12 take da lecture, hakan yasa ta tattaro kayayyakin ta masu bu'katar wanki kafin cikar lokacin danta 'dauraye su, tana kan haka Mu'een yayi mata sallama ya fita makaranta cikin shirin sa mai 'daukar hankali kamar yadda ya saba.

Ba ita ta kammala 'daurayar ba har sai kusan 10:23...sannan ta koma ta na hutawa, bata jima da zama dan hutun ba sai kuma tayi wani tunani dan haka sai ta tashi da niyyar zuwa kitchen ta 'dan dafa musu ko  indomie ma, harta shiga kitchen 'din amma sai ta fasa ganin dacewar yin wanka kafin shiga kitchen 'din cuz sam bata jin da'din jikin ta a haka, wannan dalilin ne ya sanya ta fita daga kitchen 'din ta wuce 'dakin ta dan ta watso ruwa sannan ta dawo kitchen 'din.

Kafin ta kammala komai har 11:38 tayi hakan yasa a 'kagauce ta shirya ta fita bata ko kwashe kayan ta dake shanye gaban gidan ba ta bari akan sai ta dawo kawai...gidan ta kulle da yake tasan yana da nashi keys 'din a hannun sa shiyasa bata damu ba.

Tana fita sai ta tari adai-daita ya wuce da ita makarantar.

Su Mu'een kuwa 12 cif suka fito daga lectures, shi da Ishaq da Imam suke tare harma Ishaq nayi masa 'korafin wai yau 'din sun ganshi wani iri ya babu sakin fuska kamar kwanakin da suka gaba ta..lokacin kafin su gama dai-daita wa da Husnah ne kowa mugun hali ya ringayi musu...bayan hakan kuma sai ya 'dan dawo dai-dai, and still gashi yau ma halin ya dawo.

Tsaki kawai ya saki ciki-ciki jin Ishaq zai fara takura masa da tambaya, shi ka'dai ya san damuwar da yake ciki shi kam, cuz tun jiya da Uncle J ya sanar da shi ya taso hankalin sa ya kasa kwanciya sam, tsoron abinda zai biyo bayan tattaunawar Alhaji da Uncle J yake yi...ko 'dazu da sassafe ya 'kirashi sunyi waya sai dai yace da shi yana Gombe amma suna shirin tasowa da yake acan ya kwana saboda doguwar tafiya ce.

   Yanda yake jin ransa cikin 'kunci ne ya sanya bai 'kara ko da mintina goma tare da su Ishaq ba kawai yayi musu sallama ya wuce gida abinsa...da tunanin ko zai 'dan samu nutsuwa, sai yanzu yaga wautar sa, da tunda Husnah ta tabbatar masa da cewa babu komai ta 6angaren ta sai ya saki ransa da tunanin ba itan bace Alhaji ke hari, shab ya manta da cewar Alhajin jiran zuwan Uncle J yake yi suyi magana, ya manta ashe isowar Uncle Ja'afar da abinda zasu tattuna shine babbar damuwar sa, duk dama dai yana tunanin Uncle J zai goyi bayan sa ne amma idan Alhaji ya sanar da shi komai fa...shikenan kashin sa ya bushe kenan...da wa'dan nan tunanin ya isa gidan nasa ya bu'de ya shiga bayan ya sallami 'dan sahun da ya sau'ke shi.

Akwai research 'din ma da yake son yi ga kuma damuwar da ta dame shi  shiyasa yafi bu'katar ke6ancewa shi ka'dai batare da an takura shi ba...addu'ar sa kawai shine Allah yasa tattaunawar ta su ta kasance masa alkhairi...amma sam baya wani son aure yanzu inda ace ra'ayin sa za'a bi...dama lokacin da Nanne ke raye ne zazzafar soyayyar da yake yi mata ya sashi tunanin auren ta a lokacin batare da ya ko dubi 'karancin shekarun sa ba, yanzu kuwa da babu wata cikin ransa sai yake jin yama tsani zancen auren, in kuwa ya zama dole sai an masa ne ma to Allah ya sa ba da Husnah Alhaji zai ha'da shi ba..sam ba zai iya kallan ta matsayin matar sa a cikin gidan sa ba shi kam.

NOORUL✔️Where stories live. Discover now