Hajaratu............page 28

79 7 0
                                    

*Hajaratu*.....................page 28

Wannan page sadaukar wa ne ga dukkan masoya labarin Hajir, ina jin dadin comments d'inki da add'uoin ku gareni, inayin ku sosai Allah yabar k'auna......🤲🏻

6:am kaisah ta farka daga baccin da ba wani dad'i cikin shi, ahankali ta bud'a idon ta, mama ta gani kwance saman daddumar data barta zaune jiya, wasu irin hawaye ne suka sauko mata, aranta tace " I have found my mummy in u, Ashe akwai sauran mutane masu imani a duniyar, wayasan iya adadin kwanakin dana d'auka akwance SANADIN KANIN UBANA" dakyar ta lallab'a ta dafe gadon ta tashi zaune, mike'wa tayi tsaye jiri ya d'ibeta ta zube k'asa mama ce ta ta farka daga dogon baccin daya d'auketa, "subhanallah kaisah meyasa baki tasheni ba" tashi tayi ta nufeta, kamata tayi ta tasar da ita, tana fad'in "next time if u need something ko ina bacci ne ki tadani kinji" kai kaisah ta d'aga alamar toh, mama ta kaita toilet tayi wanka da brush had'ida d'oro Alwala, mama ta fito da ita kayan ta data wanke jiya ta d'auko mata tasa, Sallah tayi a zaune, dakyar ta d'an sha tea da mama ta had'o mata, mama tace "kaisah kidaure kisha sosai kinji, zanje in shirya  in fauwaz ya shigo zamu je akaiki hospital for checkup, " toh" kaisah tace, mama ta fita.

Sanyin ruwa taji yana sauka ga fuskarta wani raunannen numfashi ta sauke had'i da fad'an "Hazbunallahu wa ni'imal wakil" tsohon yace "masha Allahu Hamisu kaga ikon Allah koh, d'anneman matsoraci matso kusa ba gawa bace da ranta" hamisu dake cen nesa dasu yana rabon idanu ya shek'o yana fad'in "ikon Allah, daranta Ashe" tashi tayi zaune tana kallon jejin, ta kalli tsohon tana fad'in "Na gode baba, nan ina ne haka?" tsohon yace "Allah shine abin godiya, nan kina cikin k'auyen gazo, kinga bukkokin cen da kike tsinka da gidaje nan muke" mik'ewa tayi tsaye tana kallon gidajen dake cen nesa dasu, tsohon yace mutai in kaiki gidana ki huta, kafin a nemi iyayenki" tsohon yace "Hamisu ka isa gonar zan kaita gida in dawo" d'an tsohon mashin d'inshi ya buga, yace "zo muje kinji yarinya" sai alokacin taji k'afarta tayi mata nauyi ga wani azababben ciwo da takeyi, ga hannun ta da ya kumbura sosai shima sai tiririn azaba yake fitar wa, tace "wash Allah nah" tsohon yace subhanallahi targad'e kikayi?" tace "eah" matsowa yayi da mashin d'in kusa da ita tahau, sai da ya kaita gidan sarkin d'auri aka ja hannun da k'afar yayi mata addu'a akai, sa'an nan ya d'aure, suka isa gidan shi, matarshi mai kirki ga tsafta gidan laka ne amma an shareshi tsaf ga k'atuwar bishiyar dogonyaro a tsakiyar gidan,  har cikin gida tsohon ya shigo da mashin d'in yayi parking had'i da fad'in " Fati d'auko tabarma, ki shimfid'a" da saurin ta ta d'auko tabarma tana fad'in  "malam ina kasamo yarinya?" Yace "kedai zo ki kamata tasauko" tace "toh" cike da al'ajabi ta kama Hajir zuwa shimfidar datayi mata k'ark'ashin bishiyar ruwa ta d'ebo mata a randa ta bata, Hajir ta karb'a ta kurkure bakinta sa'an nan tasha, godiya sakeyiwa dattijon, sa'an nan ta juya tayiwa matarsa godiya, zaune suke jugum suna kallonta, ta kwashe labarin rayuwar ta har zuwa inda Uncle Hashim ya kawota jejin ya shak'e mata wuya ya jefar, daga innah Fati har Baban sai da sukayi hawaye, baba ya jijjiga kai had'i da fadan "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kai jama'a duniya ina zaki damu, mutum sai Allah, yanzu ace d'an uwanka uwa daya uba daya shine zai iya yimaka irin wannan, to dawa zaka aminta?" Inna ta sauke ajiyar zuciya tace "wallahi malam na tausayama yaran nan, yanzu ita kaisah ko a wane hali take ciki?" Hajir ta sauke ajiyar zuciya had'i da fad'in itama nasan bazai barta ba kasheta zaiyi ko kuma yama kashe ta d'in"  zuciyar Hajir tariga ta bushe hawaye sun riga k'aurace mata, malam yace "insha Allahu itama Allah zai kub'utar da ita kamar yadda ya kub'utar dake" sauke numfashi Hajir tayi, malam ya tashi yace Fati ungo ga wannan ki aika asiyo mata abinda zata iya ci ki sarrafa mata" filo innah ta d'auko mata ta kwanta  tace bari in dafa miki ruwan zafi kiyi wanka. godiya Hajir tayi ta kwanta, a zuciyar ta tana tunanin her next plan".

Uncle Hashim  ya gama shirinsa tsaf na tafiya Niger, yayi sallama da inna da sauran yaransa, sai mu'utaseer dake kwance cikin bedroom d'inshi yana fama da fever, Uncle Hashim ya tura k'ofar ya shiga ganin mu'utaseer k'udun dune cikin bargo yasashi k'arasawa inda yake, yace "mu'utaseer me yake damunka" mu'utaseer  ya d'aga mishi hannu had'i da fad'in "baba karka tab'ani, kabarni in mutu kawai, inaga haka nake buk'ata" baba yace "bangane abinda kake nufi ba" mu'utaseer yace " baba akaro na biyu ina tambayarka ina ka kai su Hajir? ".................

Leemert A Rufa'i......✍🏼

Hajaratu Where stories live. Discover now