*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_*Alkaluman:*✍️
*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕*Wattpad:* *Janafnancy13 or Aisha Alto Alto.*
_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_
*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*
*BABI NA UKU*
*ASALIN LABARI*
*HAKIMI MANSUR ƊANBATTA* Shine asalin sunan mahaifin Tahir wanda gabanshi da bayanshi haifaffan garin Ɗanbattan ne kuma ya fito daga tsatson Hakimin Ɗanbatta ne daboda haka sarautar Hakimi daya samu ba haye yayi ba gadon gidansu ne.Tun suna samarinsu lokacin tasowarsu basuyi karatun boko ba lokacin bai yawaita ba sosai sai dai karatun allo wanda yabi gari lokacin inda ake ɗaukan yara dawaya daga kowane yanki suna zuwa karatun allo cikin Kano da sauraran garuruwa basu dawowa har sai sun sauke alqur'ani wasun suma har sai sun fara sana'a, sunyi ƙarfi kafin su waiwayi gida, toh hakan ne ta faru da Mansur wanda ɗane ga mai garin Ɗanbatta, lokacin dayake da shekara tara a duniya aka tafi dashi cikin garin Kano aka damƙashi hannun wani malamin addini mai suna Malam Haruna wanda amini ne yake ga Hakimi Hayatu.
A lokacin ba dan talaka ko ɗan mai kuɗi ba ko yaron gidan sarauta a'a lokacin ilimi bai yawaita kamar yanzu ba shiyasa zaka samu yara daga mabambantan garuruwa ankawosu wajen Malam Haruna karatun allo duk kuma daya ke iyayen yara a lokacin basu sake kamar na yanzu da in suka kawo yaro sai sun manta dashi a'a su kowane bayan wattanni suna zuwa ganin 'ya'yan nasu kuma suna musu aike akai-akai.
Wannan shine dalilin haɗuwar amintakan Hakimi Mansur da kuma Alhaji Ibrahim Kwatano wanda shima iyayensa suna da hali suka kawoshi nan makarantar Malam Haruna domin ya sauke Qur'ani lokaci ɗaya haɗuwar jini da abota mai ƙarfi ta haɗasu kuma Allah yayisu hazikai masu kaifin ilimi wanda har iyayensu duka suka shaida amintarsu ahaka suka shafe shekara bakwai kafin suyi sauka murna ba'a magana Malam Haruna ya shirya musu walima duka iyayensu suka zo suka tayasu murna, kafin kowa iyayenshi su tafi dashi gida.
Ibrahim yayi sa'a dama already kafin yazo makarantar allon ya gama Primary Sch ɗinshi suna komawa gida iyayensa suka mai cuku-cuku ya koma makarantar SS1, ayayinda shi kuma Hakimi Mansur koda ya koma sai ya fara daga Primary 1 duk da lokacin yana da shekara goma sha biyar ne toh kafin ya gama Secondry tuni Ibrahim yana BUK inda yake karantar Business Admistration, shi kuma Mansur yana gama Secondry karatunsa ya tsaya saboda rasuwar Hakimi Hayatu wanda dama Mansur ne kaɗai ɗansa namiji sauran duk mata ne so sai aka ɗaura ƙaninshi ya cigaba da riƙon sarautar maigari.
Mansur da Ibrahim suna ƙoƙarin ziyarar juna duk wanda ya samu dama Ibrahim na shekarar ƙarshe mahaifiyar Mansur ta matsa mai sai yayi aure kafin ta mutu taga kwanshi aduniya shine dalilin daya sanya ta nema mai auren ɗiyar ƙanin mahaifinshi Zainabu Abu, wanda cikin lokaci akayi komai aka gama akayi biki lafiya sai bayan bikin ne Ibrahim ya tafi service shi kuma Mansur yana zaune agidansu ɓarayin gadon mahaifinsa shida matarshi Zainabu Abu mai kunya da kawaichi shekararsu ɗaya da rabi da aure ta haifi kyakkyawan ɗanta mai kama da ubansa sak aka sanya masa suna Tahir to bayanshi ta yi haihuwa biyu duka basu zo da rai ba, lokacin ne kuma itama mahaifiyar mansur Allah yayi mata cikawa, wanda har iyayen Ibrahim sunzo gaisuwa shi baya ƙasar yana ƙasar Ughanda yatafi haɗa Masters ɗinshi, tun kuma bayan rasuwarta sai Abu ta shiga ɓari data samu ciki baya zama sai tayi barinshi kamar bazata rayu ba abunda ya fara damunsu har suka fara neman mata magani amma kuma sai cikin yayi kamar zai zauna sai kuma tayi ɓarinshi.
Sai da Tahir ya shekara 9 aduniya kana Ibrahim yayi aure bayan ya daɗe da dawowa ya haɗa Masters ɗinshi Babanshi ya bashi kuɗi sosai ya ɗorashi kan kasuwancinsa dayake dama shi ɗin motoci yake saidawa 'yan kwatano shiyasa yake amsa wannan laƙabi bikin da Zainabu Abu ita da Mansur da Tahir sukaje suka kwana uku suka dawo domin Mansur da Ibrahim basu yarda zumunci ba.
YOU ARE READING
NANNY(Mai Reno.)
FanfictionMARAINIYACE BATA DA UBA..SAI UWA..SUN TASO CIKIN WAHALAR RAYUWA...KWATSAM TA TSINCI KANTA AGIDAN WANDA TAKE KALONSHI AMATSAYIN UBA A MTSAYIN NANNY..YAZAMA GATANTA GABADA DA BAYA..RANA TSAKA YA ZAME MATA BAKIN KADDARARTA.