shafi na biyu

638 34 19
                                    

Kallonsu nayi na kuma kalla sannan na tab'e baki irin ko in kula d'in nan,k'was k'was na ci gaba da taka takalmina ina shirin shiga gida, matar ta ce min "baiwar Allah ki wa Allah da annabi  ki taimaka mana, ko iso ai mana wajen yallab'ai tun d'azu aka ce mu zauna wani nan dan saurayi ya ce mu jira."
"Ban tanka mata ba, sai ma tab'e baki  da nai cikin kallon k'ask'anci nace "dan Allah tsohuwa ki b'acemin daga gani ku har abada bakwa rabo da  maula, mun baro canma amma seda kuka biyomu ni na rasa ma ta ina kuke shigowa inda yafi karfinku"
"Kiyi hak'uri 'yar nan yau ce ta janyo hakan, kinga wannan yaron" ta nuna dan tsamurarren yaron dake langwaɓe zaune adandariyar wajen "ciwon kunne yake da shi, tun yana jariri mun jajje
asibiti ance se an kawo dubu arabin aiki za ai mai, kullum baya bacci da dare, ita kuma wannan" ta nuna yarinyar "an koreta daga makaranra gashi zata zana jarabawar gama firamare, wallahi abinci ma gagararmu yake." Huci nai na furzar da iskar bakina 'am so tired da surutun matar nan nan, jakata na bud'e na ciro 10k na wulla mata na ce ta fita, d'an tsayawa tai ta sunkuya ta ɗau kuɗin jikinta yayi sanyi ganin kamar da wulkanci raheena ke mata."Ga dubu goma nan ki k'ara ba"
"Dan Allah yar nan ko zaki min iso da  wani yaro nan daya shiga ciki shiya ce na zauna."
"Wani abunse talaka yanzu dubu goman kika raina! karenki ne ya baki har wani neman dad'i kike, to ba zan mai maganar ba" k'walawa lawal kira nai idona a lumshe alamar gajiya nace "ka fitar da su daga compound d'in gidan nan har can wajen dan bana son sake ganinsu" na fad'a ina mai sakin tsaki na bar wajen cikin takuna mai cike da izza.
Na san dole su biyoni da kallo ko da ban juya ba kuwaDamk'e kud'in matar tai cike da tausayin kanta tana jin dama sune a rayuwar da  raheena take ciki da ko birnin sin ne sai ta kai danta ya samu lafiya.
"Iya ku fita kun daiji me aka ce, yakamata ku ringa zuwa gun wanda suka san darajar d'an a dam deyarinyar da se lokacin tai magana ta ce "umma kizo mu tafi wancen gidan kinsan de ko rabin kud'in bamu had'a ba, kuma de ai ta bamu ba fa inda aka bamu se nan"
"Hakane" uwar ta fad'a tana mai jansu suka fita lawali ya kada baki ya ce kar "kuma ku k'ara zuwa nan jibarku fa yargale yargale wai ta ina ma kuka shigone ehe?
matse kwallah matar tai "na tabbata aiki kake agidan nan amma ka dau girmankai ka d'orawa kanka, nima yau ce tasa, mahaifin yarann nan hatsari yayi ya mutu da ba dan haka ba da baka ganmu ba, ga 'yan uwa ba zumunci" Jikinsa ne yayi sanyi ya ce "hakane iya nima ba a son raina ba to wannan da ta baku kud'in bata da mutunci wallahi muddin ta lek'o taga ban fitar da ku ba rasa aikina zanyi kuma da shi na dogara nake ci da kowa nawa.
"To Allah ya rufamana asiri" ta fada suna mai barin wajen cikin sauri dan a asurce suka shigo layin saboda _security_ dake wajen.

RAHEENA 2016Where stories live. Discover now