page 42

114 6 0
                                    

Gaba d'aya hankalin su ya koma kan wacce ke haurowa sanye take da bak'ar abaya ta yane kanta da jan mayafi ta rufe hancin ta da face mask Wasila zare ido tayi sosai don taso ta gane ta amman dake akwai mask bata ida gane ko wacece ba.

****

Kaiwa da kawowa kawai take cikin d'akin ta, ta kasa zaune ta kasa tsaye  sai duba wayan ta, takeyi jira kawai take taga ankira ta awaya shiru babu kiran ,kiran wata number tayi yana ta ringin ba'a d'aga ba, tsaki taja ta cilla wayan kan gado ta nemi gurin ta z'auna kam gadon tana rik'e da kanta dake mugun sarawa bata san sanda ta furta .

"Baku da amfani dana san haka zakumin daban saku ba awa guda harda wani abu".

Ta kuma jan wata tsakin ,Yesmin ,ne ta turo kofa ta shigo fuskar ta d'auke da murmushi ta k'araso gaban Ammin ,nata ta zauna.

"Ammi sannu da gida Albishirin ki?".

Ammi danne damuwar ta, tayi tad'an sake fuska ta dubi yar tata .

"Goro yau me kika samo mana a school d'in?".

Yesmin seda tad'anyi shiru sannan ta dubi Mamartata.

"Ammi yau naga me kama da Anty Wasila 'a kofar makaran..."

Kafun ta k'arasa taji an buge mata baki har jini na fita.

"Kincin ubanki dake da Wasilan , nikam Wasilarnan uwar kice ko yar uwarki da kikabi kika dameni da ita mak'i yiyar tawa kike so tow ,Wlh daga yau kika sake mun maganar Wata ,Wasila a gidanan sena yanka ki tashi ki bani guri".

Yesmin, na kuka ta ,tashi ta fice ita kuwa 'Ammi idan banda tsaki babu abin da takeyi abun duniya duk yabi ya ishe ta Abi d'inma rabon shi da gida yau sati guda kenan gashi tunda Hajiya turai tasa k'afa tabar gidan bata sake jin taba, kota kira wayan ta bata samu komai ya kara jagule mata, ta ,tura akashe mata Wasilan ma har yanzu shiru wanda ta, tura babusu babu labarin su .

******
"Cire mask d'in tayi Wasila seda ta razana bakin ta na rawa tace.

"Mahnoor ".

Mahnoor cikin tsatsar tsanar Wasila tace.

"Karki ,kuskura ki sake kiran sunana idan ba hakaba walahi yanzunan zansa su farke ki ,su kashe banza jaka ,kwartuwa kawai ke tsabar iskancin ki har da ubana zakibi ke kin isa kibi ubana dan ubanki ".

Duban kallon ta, tayi zuwa ga mutanen tace.

"Ku kuma waya saka ,kuzo ku kashe ta?".

Ogan sune ya dubi Mahnoor yace.

"Alhaji Matawalle ne yace muzo mu kashe ta".

"Alhaji Matawalle ".

Shine Abun da Wasila ke nanatawa cikin zuciyar ta, mutumin da suka rabu yanzu shine yasa azo a kashe ta ,tow me tayi masa kode ya gane wayon tane.

Ita kanta Mahnoor Abun ya bata mamaki duban su tayi cikin ,nutsuwa tace.

"Sunana Barr Fatima ni d'iya ce ga Alhaji matawalle ina son ,nabaku umarni karku yarda ku, kashe ta ku sauka, k'a kujira ni zanzo muyi magana daku zan ninka muku goman kud'in daya biya akan ku, kashe ta, kuje kujira ni ina son zanyi magana da ita, cikin murna suka sauka don jiran ta ita kuma ta dubi Wasila cikin tsana don aduniya idan akwai halittar data tsana tow Wasila ce.

Fuskar ta a sake ,kamar mutuniyar arziki .

"Wasila 'abubuwan da suka faru abaya don Allah kiyi hakuri wlh duk bansan haka abun yake ba sai yanzu ashe Abi shine sanadin mutuwar Zahra yaso mu lak'aba miki lokacin da naji wannan bak'ar zancen nagirgiza saboda duk d'iya ta gari baza taso ace mahaifin ta ya aikata haka ba, nayi godiya ga Allah da ba'a kashe kiba da yanzu ankashe ki naji wannan labari ina zan sameki in nemi yafiyar ki. Kiyi hakuri ki yafe min".

Ita de Wasila cikin rashin yarda da magan ganun Mahnoor itama ta murmusa tace.

"Babu komai ni ban rik'e kowa acin kuba".

Murmushin da iya kacin shi fatar baki ne Mahnoor tayi ta dubeta tace.

"Nagode zan temaka miki na fitar dake daga tuggun mahaifina kijirani ,nan da bayan sallar magrib".

Ita de Wasila tsoro da Mamakin Mahnoor kawai takeyi macen data nuna mata kiyayyar kuru kuru yanzu kuma lokaci guda ta nuna mata soyayya anya kuwa bubu wani abu a k'asa da suke son shirya mata, tow koma de miye Allah nan ze kare ni.

"Tow nagode Anty Mahnoor nakuma gode Allah da kuka gane gaskiya ".

Dariya Mahnoor ta kuma saki ta rungume ta ,tana wani irin dariya , ita de Wasila poto copy ta zama don abubuwan da Mahnoor d'in keyi mata sun fara bata mamaki macen da ko hanun ta bata tab'a tab'awa ba lokacin tana gidan su, saboda tsananin kenkemin ta, da takeyi yau itace harda rungumar ta lalle akwai damuwa .

"Ciwan ya mace naya mace ne kinji Wasila insha Allah ako wani hali zaki shiga a yanzu ina bayan ki zan wuce zuwa anjima zan dawo".

Ta sake ta, ta sauka k'asa fita sukayi a gidan ita da mazan tasasu amotar ta sukabar haraban unguwan sannan ta kashe motar ta, ta dubesu tace.

"Nasan ba Alhaji Matawalle bane ya turo ku kashe ta ku gaya mun waye ya turo ku?".

Seda suka d'anyi jim sannan ogan su ya dubeta yace.

"Gaskiyar magana bashi bane matar sace ta, turo mu sannan ta gargad'e mu dako an kamamu muce shine ".

Girgiza kai tayi tace Ammi wannan wacce irin k'iyayya ce da har kike son ki jefa mahaifin mu cikin matsala zan dede taku insha Allah koda hakan zesa ni nashiga cikin matsala farin cikin ku shine nawa.

Duban su tayi tace.

"Idan kuka kashe ta, ta haka akwai matsala akwai hanyoyi da dama da zaku iya salwantar da rayuwan ta batare da kun shiga wata matsala ba".

Duban ta ogan yayi yace.

"Tow ta yaya kike gani?".

Dariya tayi tace.

" ni Barreste ce nasan hanyoyi da dama da za'a kashe ta kuma har duniya ta nad'e baza a tab'a ganewa ba kawo kunan ka kaji yadda za'ayi".

Rad'a ta masa a kunne dukkan su ,suka shek'e da dariya ,yace.

"Hajiya gsky kina da basiri ".

Dariya ta sake, saki tace.

"Kasan kalan karatun da nayi kuwa? Najima ina karatu a duniya zan k'ara muku dubu d'ari shida akan kudin da Ammi ta baku bayan sallar magrib nake son ku aiwatar da aikin ".

Godiya sukayi sosai suka rabu kowa da abun da yake sak'awa.

*****-

Wasila tun fitar Mahnoor ta kasa zaune ta kasa tsaye kwata kwata sai taji bata yarda da Mahnoor ba ,saboda lokaci guda ta rik'id'e ta dawo mata mutuniyar arziki kuma da ba haka take ba, anya kuwa babu abun da take shirya mata na mugun ta, kuwa haka ta d'inga sak'awa tana kwance wa, duba agogo tayi taga shida saura da sauri ta haye sama .


Kuyi hakuri da wannan abubuwa sunyi min yawa insha Allah da komai yayi daidai zaku cigaba da samun read more me yawa ina jin dadin yanda kuke son littafin kuma kuke nuna kulawan ku akan shi Wasila na gaishe ku lol.

Muje zuwa..✍️

RASHIN GATA Where stories live. Discover now