Su na shiga ya maida qofar ya rufe, tare da dora ta a saman cinyar shi kamar yanda ya saba, dogon gashin kan ta ya ke shafawa a hankali, ya na lumshe idanu, dayan hannun shi na shafar bayan ta zuwa qugun ta, Aaseeyah ba yarinya ce mai zama waje daya ba, ta na zaune ne kawai a cinyar shi, amma barnar da take da hannun ta a dakin ba qarama bace, janyo wancan janyo wannan, duk abinda ta ke son dauka ko meye a gaban shi ba ta daga wa za ta miqa hannu direct kan abun ta janyo, komai sai ya bare, a haka ta dinga zaro chocolates din da ya ke ajiye wa musamman sabo da ita da Umaimah, bude wa ta yi ta fara sha, cikin wani irin yanayi da ba ta gane wanne ne ba ta ji Yah Noor ya sauke numfashi, sannan ya kwantar da kan shi a bayan ta, murya can qasa ya daga ta a jikin shi ya ce,
"Aaseeyah kin kwashe chocolates din dika, ba za ki rage wa 'yan uwan ki ba? Kin san fa kullum ina hana ki rowa, rowa ba bu kyau,"
"Tabdijam, in su na so su tambaye ka mana, ai kai Allah bai sa ka na da rowa ba, ni kuwa kowa a gidannan ya san haka Allah ya haliccen ba na bada chocolates dina da gyada ta, kuma ka ce ba kyau mutum ya sauya daga yanda Allah ya halicce shi ko?"
Daga mata kai ya yi, ya na murmushin wayo irin na Aaseeyah, kiran sallar magrib ya ji, nan ya dau dankwalin ta ya maida mata kan ta, ya ce ta je tai sallah bari ya yi alwala.
Turo baki ta yi, ita gaskiya sai ta gama shan abin ta za ta fita, dan ta san Yesmeen na fakon ta yanzu.
Dan zaro ido ya yi, da ya kalli jikin shi,
'In ba ta fita ba ta ya zan iya tashi a gaban wannan sarkin tambayar?'
Hannu ya sa ya dakko biscuit mai dadi ya bata,
"Ga wannan da sun roqe ki ki basu, ai ba a halicce ki da rowar biscuit ba ko?"
"Eh shi ina ba da shi gaskiya, da komai ma ni fa wannan ne kawai ba na iya bayarwa ko na so bayarwa sai na ji na kasa,"
"To ba komai maza jeki zani sallah kar na makara"
Da sauri ta dauka ta bar dakin, ta na fita daga dakin nashi ta rage sauri, ta zuba ragowar chocolates din ta a rigar ta da ta dan matse ta, ta riqe biscuit din ta na budewa, ta dauka za ta sa a baki kenan Yesmeen ta kwace ta zura da gudu ta na dariyar mugunta,tare da kiran
"Ni ma na rama"
Dariya sosai itama Aaseeyah ta zauna ta na yi har da riqe ciki, duk suka zuba mata ido, dan kada kai ta yi irin na yara masu mugun iyayin nan, ta miqe ta na ci gaba da dariya ta tafi,sai da ta kai bakin qofar fita ta ce,
"Dadi na da Yesmeen muguwar doluwa ce, ba ta san me ye a jiki na ba ta ke murna ta raba ni da biscuit, a ci dadi lafiya duk na topa masa yawu, in kin cika kwadayayyiya dan Allah ki cinye na bar maki ba Allah ya isa a tsakani na dake, ai ke yar uwa ta ce"
Wani irin takaici da kyankyami ne ya kama Yesmeen ta sake biscuit din a qasa, Umaimah na ganin haka ta dauke ta na dariya, dan ta san halin Aaseryah ba wani yawu da ta sa, dan ta hana Yesmeen sarkin tsafta ci ne, kai ko da yawu sai ta ci, ai yawun 'yar uwar ta ne, Aaseeyah na ganin haka ta kece da wata sabuwar dariyar nasara ta falla da gudu bangaren su, ta na shiga ta lalleqa ta ga ba Mammeen ta a wajen, dakin ta ta fada, ta bude drower ta dinga zaro chocolates ta na zubawa, sai da ta zuba dika sannan ta rufe, ta je tai alwala ta yi sallah.
Bangaren Noor kuwa daga wanka ya fito, tare da matse wandon shi da ya cire ya shanya a kujera guda daya dake a dakin nashi, ya sauya kaya da qananan kaya sannan ya kulle dakin shi ya tafi masallaci.
Ya na zuwa ya samu har an yi raka'a biyu, bin sallar ya yi,bayan an idar ya rama biyun ya zauna azkar da karatun qur'ani, kowa na wajen ba qaramin burge shi Noor yake ba, saboda irin tarbiyyar shi, da nutsuwar shi, 'Yan biyu kuwa ana idarwa suka bar masjid din, suka nufi wata majalisa ta abokan su da ake hira, ta ball ne, ta films ne sabbin fitowa, waqoqin raps, da dai sauran abubuwan da matasa yanzu suka maidawa hankali,ba za su bar wajen ba sai an yi isha'i, in sun yi sun sallame su sake komawa majalisa, watarana sai sun ga mahaifin su na daf da dawowa ko yayan mahaifin su sannan za su bar wajen.
YOU ARE READING
TAUBASHI (COUSIN)
RomanceShin kowanne cousin ne irin Yah Noor da Yah Mahboob? A cikin Cousins din ki/ka mata ku na da kamar Aaseeyah kuwa? Ko kuma kamar Umaimah gare ku? Mahaifan ku maza halin Abee gare su? Ko kuwa ku na da mahaifiya mai halayya irin ta Ummee? Allah sarki w...