Shafi Na Tara

2K 144 20
                                    

A saman kujera na kwana a zaune ina ta kallon Nana tun ina kuka da hawaye har na koma ina ta rare kukan kawai babu hawaye. A kasan gurin Lukman ya kwana. Tun da asubar fari masu sharar asibiti suka tashe Lukman ni kuma suka ce na fita za su gyara gurin. Ba dan babu yadda xan yi ba da ba zan fita ba, domin ina jin kamar idan nai nisa da Nana mutuwa za tai ta barni.
A haka na fito ward din ina jin zuciyata babu dadi, Lukman kuma na ta murja ido alamar bachin be isheshi, kai tsaye gida na nufa kai tsaye domin samawa Nana abunda zata ci da ita da Lukman, wannan karon da kafa na iso kasancewar daga unguwar Clapperto zuwa uduth babu wani tazara sosai ga talaka irina wanda ya saba da tafiyar kasa. Ina janye da hannun Lukman har muka iso kangon gidan. Tsaye nai ina ta tunani ta inda zan fara, rashin lafiyar Nana ta tsaya min a rai har na so min kamar bana da wani sauran kuzari.

“Ataa ya me za mu yi?”

Maganar Lukman ce tasa na dawo daga dogon tunanin da nake rakiyar zuciyata da shi.

“Koko zan siya maka kai da Nana”

“Ni ba zan sha ba”

Ya fada yana mitsintsika ido.

“Saboda me? Ko waina kake so?”

“Aa bana son komai Nana na ke son ta samu lafiya, Ataa ai zata tashi ko? Zata ji sauki ko? Na yi mafarki ta samu sauki tana min magana”

Wani irin tausayinsa da na kaina nd ya lullube ni a lokaci daya, duk yadda na ke shakuwa da Nana nasan Lukman ya fini shakuwa da ita domin shi karamin yaro ne, kuma kusan kullum tare suke zuwa bara tsabanin ni da wani lokacin na ke zuwa wani gurin dabam.

“Zata ji sauki idan kana cin abinci,Nana tana son ta ganka kana cin abinci”

“Haka ta fada miki? Da na yi kwana ta farka?”

Na gyada masa ina hawaye, sannan na saki hannunsa na shiga neman tsohuwar butarmu kuma basasshiya cikin duhun asuba, na yi alwala na mikawa Lukman ragowar ruwan shi ma yai alwala, wani masallaci na bi na gabatar da sallah magariba bata, na yi ma Nana addu'ar neman lafiya, sai kuma na rasa wacce za yi ma Doc Asim, bana son nayi masa mummunar addu'a ya zama ba gaskiya ba ne, domin har yanzu zuciyata tana min kwankwanton cewar ba gaskiya ba ne idan ma ya cire wane amfani zai yi da ita wane amfani zata masa? Mi ma zai yi da ita? Wata kila kuma siyarwa zai gi idan ana siya, waya sani ko wani ya ce ya cire? Amman kuma wa Nana ta sani da har zai sa ayimata haka? Ko shiyasa aka Anty Shukura ta ce mu bar asibitin idan ina son mahaifiyata araye? Shiyasa ta rika girgiza min kai a lokacin da zan saka hannu a takardar nan? Gaskiya ne idan har ba cire mata koda yai ba, mi zai sa yai ta taimakonku haka da yawa magani ma kadai ya kashe mata kudi mai yawa, abinci ma shi yake siya mana, anya idan ba wani abun zai mana taimako haka mai yawa? Haka dai zuciyata tai ta min wasiwasin gaskiya da kuma akasinta a lokaci daya.
  Fitowa nai na tsinci kwanon mu a inda mugayen mutanen suka harba mana kayan cin abinci da kafa na wanke na bawa Lukman yaje ya karbo mana koko, bayan ya dawo na sake aikensa ya siyo ma Nana waina mai yaji dan nasan ita ce favorite dinta.
   Kadan na kur6a kokon shi ma dan ina jin kamar bana da kuzari ne wai ko zan dan samu karin karfi, na mikawa Lukman sauran kokon ya shanye ba ko suga. Sauran ragowar kudin na fito da su ina kargawa da na hada sai na ga ba su kai ma dubu uku ba gaba daya dubu biyu ne da dari hudu da naira talatin, haka na hada kudin guri daya, na kurawa Lukman ido ina ta kallonsa yana shan koko duk da kasancewar hankalina a gurinsa ya ke ba. Bayan ya gama na dauki wainar da ragowar canjin mu doshi asibitin ni da shi ina tafiya ina jin kamar ana turani gabana sai faduwa yake. Lokacin da muka isa asibitin sai masu gadin ward din suka hana mu shiga, wai ba a zuwa ganin marar lafiya sai da yamma haka dokar asibitin ta ke.

“Ba ganinta na zo ba, abinci na kawo mata kuma ni nake jinyar ta”

Na fada cikin muryarta ta gajiyayyu mutane marasa galihu.

Z A K IWhere stories live. Discover now

An error has occurred. We're sorry about that!