23

27 2 0
                                    

*TUN RAN GINI TUN RAN ZANE*

Khairat Up.

Vote @wattpadkhairi_muhd.

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to like our page https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

Wattpad-https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube- https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Page 23.

   Nayi mistake din page a maimakon 22 na sa 23 to yanzu ne zamu tashi page 23.

___________📲.

"Haba Hajiya uwardakina ke kuma haka ake yi? So kike yi ya daina ganin girman ki daga shi har ya'yan ki? Wannan lokacin ai na kirsa ne ba na fadace-fadace ba gaskiya kar ki bada mata nidai ina baki shawara ki bi shi ki bisu a hankali ki sake sabon shiri tukuna sai ki dirar musu amman ta haka ai kallon wawiya zasu yi miki daga Mamin yaran har Mijin naku."

Wani irin kallo Umman tabi Iya da shi jin ta ambaci Mijinsu shi kenan yanzu da gaske mijinta ya zama na Khadija ma?. Wannan tunanin ma ya sata kuka saida tayi ta gaji tukuna ta tashi ta koma uward'a'k'a.

"Allah dai ya kawo karshen wannan kiyayyar dan matsayin annabi. Abu yaki ci yaki cinyewa tun shekaru nawa baya ga ya'ya har sun girma sun yi wayo sun yi aure amman sai abu daya ake yi."

*

Mami da Abba basu fito ba saida suka kimtsa kan su . Mami cikin kwalliya mai kyau ta fito sai kamshi take zubawa haka ma Abba yayi wani irin kyau ga annuri na fita daga fuskar shi kana ganin shi kaga sabon ango (lol).

Mami na fita tsakar gidan suka hadu da iya tana kokarin juye breakfast.

"Barka da fitowa Mamin yara."

Ba yabo ba fallasa ta amsa mata tunda ta gano munafuka ce ta daina shiga shirginta. Ta tsani mutum mai fuska biyu a rayuwarta.

Jiki a sanyayye Iya zulai ta gayar da Abba ya amsa shi ma kadaran kadahan.

"Ina ita Umman yaran?."

"Tana ciki Alhaji."

Hannun Mami ya ja cikin part din Umman ba laifi a gyare yake tsab an gyara shi ga kamshin turare  na tashi a ciki.

Mami ya nunawa wuri ta zauna tukuna sannan ya shiga d'ak'in Umman.

"Salamu alaikum."

"Wa'alaikum Wasalam." Umman ta amsa cike da fara'a tayi wanka tayi fes ita ma ga fuskar nan sai murmushi take yi masa.

Yayi mamaki sosai ganin wannan sauyin a iya wanan yan awannin da ta shigo ciki. Cike da jindadi yace "Uwargida sarautar mata kin yi kyau sosai na siyi kwalliyar nan."

Taji dadin abin da ya fad'a sosai.
"Ko baka siya ba kai aka yiwa daman barka da Safiya ."

"Toh Alhamdulilah nagode kuma naji dadi da kika saki ranki kika dauki girman da Allah Ya baki. Naji dadi sosai da na ganki cikin walwala. Ki tashi ki taho muje ku gaisa keda Yar'uwarki gata a falo."

Duk da taji wani irin kishi haka bai hana ta bi shi ba kawai ta bi shawarar yin amfani da kirsa, da kuma danne kishin ta. Saidai tana ganin kwalliyar Khadijan da kyan da ta ga tayi sai da taji bakin ciki. Nan da nan fiskarta ta sauya daga fara'a zuwa hade rai.

Mami ko cikin iya taku ta yi yake kadan tace "Ina kwana Hajiya Firdausi?."

"Lafiya lou." Ta fada da kyar.

Gyaran murya Alhaji Iro yayi sannan ya gyara zaman shi.

"Ina bukatar ku bani aron hankulanku nan.

Dukaninsu nutsuwa suka yi suka fuskance shi .

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.Where stories live. Discover now