25

38 2 0
                                    

*TUN RAN GINI TUN RAN ZANE*

Khairat Up.

Vote @wattpadkhairi_muhd.

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to like our page https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

Wattpad-https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube- https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Page

___________📲25.

"Bayan sallar la'asar aka gama kimtsa Rauda. Su Gwagwo suka yi rakiyarta har gidan ta. Saidai da aka kaita gun Umma babu yabo babu fallasa ta amshi Rauda fusjar nan murtuk kamar (kunu). Saidai suna tafiya ta kira Aliyu.

Bakin ciki kamar zai kasheta ganin irin adon da ya ca'ba daman zuwan shi cikin birni ya kara wayewa sosai ya iya daukar wanka.

Hararshi ta fara yi sannan tace mishi "Na gani an fi karfina an kawo Rauda gidan nan saidai ka sani ban yarda ba ina nufin ban yarda ka kaita wancan gidan da zaku zauna ba ka zauna a nan dani a bangarenku zan bawa Sadeek wani d'ak'in sannan in har ni nan ni Firdausi ni na tsuguna na haifeka , na shayar da kai, ban yafe maka ba in ka kuskura wani abu ya had'a ka da waccar yarinyar ba Wallahi in ko naga sabanin haka Wallahi sai na d'aga maka nono." Ta karasa fad'a tana huci irin nan an zuciya din nan.

Wani irin sanyi jikin Aliyu ya yi yaji kan shi ya sara masa kafarshi ta sage daga tsugunon da ya yi ya koma kasa sharaf ya zauna ya dafe goshin sa da yake yi masa ciwo a lokaci guda Umma ta rusa masa farin cikin da ya shigo da shi wannan babbar ranar da ya tanadarwa shekara da shekaru Umma mahaifiyarshi ta rusa masa shi Innallilahi wa inna illahir rajun ya dinga maimaitawa.

"Sauran inji zancen nan a gun ubanku in yaso in ya sakeni sai kaji dadi ka kashe min aure sai ka zauna da Khadija da yarta Rauda tashi ka bani wuri na gama da kai."

"Umma...."

"Dakata min Malam! Dakata min, kar ka kuskura ka fada min komai na gama yanke hukunci ka je ka na gama magana da kai ina nan ina nema maka mata wadda nake so ka aura dai dai da ra'ayina."

Tashi ya yi jikinshi har rawa yake yi baya ma gane komai kawai ji yayi ma kamar zazzabi na damun shi wani irin tashin hankali yake ciki wai Umman shi ce tayi mishi sanadin farin cikin shi ko kallon gaban shi baya yi wajen ma bai koma ba dakin nasu ya shiga ya kwanta kan gadonsu kamar an jefa shi haka yake fad'a kan gadon.

Wayarshi ya laluba cikin aljihun shi ganin kiran Amira ne ya sa shi sakin wani irin tsaki ya yi wulli da wayar.

*

Awanni biyu tsakani da kawo ta gidan Aliyu a wannan ranar tana cike da farin ciki da annashuwa yau zata kasance inuwa d'aya da sahibinta masoyinta wanda suka jima suna son kasancewa taren cikin inuwa daya na har abada ko gaban abada.

Saidai har karfe daya bata ji alamar Aliyu zai dawo ba sai wani irin tsoro ya lullubeta ita kad'ai a wannan gidan mai girma bata saba kwana ita kadai ba ta saba dasu Gwagwo da Mami amman yanzu ita kwal. Wayarta ta dauko ta kunna wadda tun da aka fara sabgar bikin bata kunnata ba.

Number din shi tayi dialing bai dauka ba a wannan lokacin ya kai makura wajan ciwo ta yadda ko idanuwan shi baya iya budewa.

*

Sadeek ne ya dawo daga inda yaje ya shiga dakin nasu sanin cewa an kawo amaryar Yayyansu ya sa shi fadawa kan gadon da karfin shi sai jin shi ya yi kan mutum shi ihu Aliyu ihun wahala.

   "Wayyo Allah na kayi hakuri ban san da kai a wurin ba ka sani ku kuke ganin mu bamu ke ganinku ba ayi min afuwa wannan rashin sani ne Wallahi akas....."

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.Where stories live. Discover now