34

32 2 0
                                    

*TUN RAN GINI TUN RAN ZANE*

Khairat Up.

Vote @wattpadkhairi_muhd.

*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION📚*
_[Karamci tushen mu'amula ta gari]_
Visit to like our page https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp

Wattpad-https://my.w.tt/RXazzM0MY7

Youtube- https://www.youtube.com/channel/UC1cigRjL8UfjxSLNtt-x4MQ

Page

___________📲34.

Zabura ya yi ya tashi da sauri ya zari key din motarshi ya fita da d'an gudu-gudu. Hanyar Zaria ya d'auk'a bai tsaya ko ina ba sai a cikin makarantarsu inda suka saba haduwa nan ya yi parking ya d'auk'o wayarshi ya latsa Numbers dinta.

Amira na zaune daga ita sai yar shimi da karamin shot gashin nan a baje tana dana wayarta kamar a cikin mafarki ta ga kiran Aliyu wani irin dad'i ne ya ratsa mata kwakwalrta "na sani zaka zo, dole ka zo ko ba ka zo dan komai ba zaka zo dan k'ullin da nayi maka. Murmushi ta saki ta gyara zamanta a karo na biyu har ta kuma tsinkewa daga karshe dai a karo na hudu ta daga kiran cike da yanga da yauk'i.

  "Hello!."
"Ki fito ina so muyi magana da ke ina inda muka saba had'uwa a makaranta."

Dariya tayi sannan tace "ok!."

Yana kashewa ta saki ihun murna sannan ta tafa hannayenta guda biyu tace a fili "So soon Aliyu Ibrahim gaskiya na ciri tuta."

Abaya kawai ta zura bayan ta fesa turare ta shafa powder ta dauki flat din takalmin ta tayi waje bayan ta kulle d'ak'in saboda Aayan bata nan taje unguwa.

*

Kananun kaya ne a jikin shi yayi mata mugun kyau duk da ya rame amman kyansa bai buyu ba. Jingine yake a jikin motar shi yana kallon kasa tunani kawai yake yi a kan rayuwarshi da Rauda idan taji wannan maganar ai ya kad'e har ganyen shi dan Wallahi bazata kula shi ba iya wannan tunanin ma in ya yi yana sa yaji kirjinshi na dokawa.

"Salamu alaikum!."

"Wa'alaikum salam!."

"Amira! ...."

"Aliyun-Amira dai". Ta fad'a tana murmushi har wani lilo jikinta yake yi dan dadin ganin Aliyu saboda yazo ganinta.

"Mu samu guri mu zauna Ina son zamu yi muhimmiyar magana dake saboda yau nake so na juya na koma gida."

"Ok! Muje."

Zamansu keda wuya ya gyara zaman shi ya fuskance ta.

"Amira ban san me yasa kika yi min haka ba ke kin sani ina da mata kuma ina sonta kuma bazan iya had'a ta da wata ba saboda kwatankwacin kalmar adalci ma a tsakaninku bazan iya ba saboda sonta a jinina yake , sonta ya gama shiga ko ina da ina na jikina Wallahi Amira bazan iya aurenki ba. Kin sani na sani abin da ya shiga tsakaninmu kuskure ne sharrin shaid'an ne kuma sau daya ne bamu kuma ba....."

"Tsaya Aliyu wai dama kazo ne dan ka gaya min maganganun nan? Ni fa Na dauka kazo ka sanar min da zancen auren mu ne tayaya zaka bata min rayuwa kuma kace wai bazaka aure ni ba? A ina ake yin haka? Wallahi bazan risina ba sai ka aure ni ban ce dole ka soni yadda kake son matarka ba ni ina sonka kuma naji na gani zan zauna da kai koma a ina ne ko da kuwa a daji ne babu gida gaba babu gida baya."

"Amira ki gane mana bana sonki bazan iya auren ki ba."

"Aliyu to ya kake so ayi da wannan abin da ka k'unsa min?" Ta fad'a tana nuna cikinta.

"Na sani kin sani karya kike yi baki da wani ciki amma tunda kin ce haka kuma kin gani kina son asirinmu ya tonu a idon duniya shi kenan. Watan cikin nawa?."

Duburburcewa tayi jikinta ya yi sanyi bata ma san me zata ce ba kawai sai ta bige da borin kunya ta ce " kamar ya? Ni ban je nayi scanning ba tukuna."

Dariya ya yi irin dariyar nan da ake kira ta rainin wayo ya tashi tsaye ya gyara tsayuwarshi ya bita da wani irin kallo ya ce "Shi kenan Amira zamu yi waya dake tunda kince wasan kike so muyi zamu yi naji kina da ciki kuma naji nawa ne naji zan je gidanku kuma iyayena ma zasu je gidanku zamu san yadda zamu yi ki shirya tarbarmu ni da dangina muna nan zuwa."

Duk da ta tsorata da abin da ya fad'a da kuma yanayinsa haka bai hanata ji dadin abin da ya fad'a ba. "Nagode Aliyu da ka yarda zaka kasance dani a cikin rayuwata nagode. Zan yi wa Mummy na magana zata fadawa Abbana in ya dawo zan gaya maka sai kuje da maganar ko?."

"Allah Ya kaimu."

Bazaka tsaya in yi maka girki ba.

"Aa , nagode matata tayi min." Daga haka ya tafi gurin motarshi.

*

Rauda ko tana asibiti suna kwasar kaya dan an sallamesu jikin ta duk ya yi sanyi ashe Aliyunta zai iya yin irin wannan kwanakin bai nemeta ba ? Ko yana ina yanzu? Tayi kewarsa tayi kewar komai nasa gaba daya jikinta ya yi sanyi so take ta gan shi amma bazata nemeshi ba tunda bai nemeta ba shi ma.

Mami da ta gama lura da ita ta nisa sannan tace "Rauda, na ga alama akwai abin da yake damunki amma ban san abin da ya ki ba kuma ko baki fada ba na gama karantsrku keda Aliyu ne . Bana so ki shiga fadan da babu ruwanki a ciki abin da yake tsakani na da Firdausi daban ne babu ruwanki a ciki kar ki sake ki ce za ki shiga har ya shafi aurenku keda Aliyu tun kan a haifeku ake wannan kishin kuma bazai kare dan ku ba saboda haka ki maida hankalinki ita rayuwar nan komai dan hakuri ne marar hakuri baya da nasarar komai a rayuwarshi muddin ki ka kasance mai hakuri to kina tare da nasarori da dama a rayuwarki. Ki zamto mai biyayya da hakuri a ko ina a rayuwarki bazan kuma gaya miki ba ki kama kanki ki koma ki kula da mijinki in ba haka ba zaki rasa shi a banza a wofi domin kuwa yan'mata rubibinshi suke musamman ma shi da ya ke a birni yake haduwa da yan'mata goggagu wayayyu da suke da ilimin da yafi naki Allah ne Ya baki ki rike shi gam. Ki tattara kayanki ki koma gidanki."

Hawaye suka zubo min nace "Mami ni Wallahi Ummanshi bata sona baki ga abin da take min ba shi kuma sai ya dinga yi min fad'a a kanta ni ban yi mata komai ba....."

"Ashe baki da wayo to zai ki uwarshi ne saboda ke? Har yanzu ke yarinya ce baki san komai ba ai ita Firdausi haka take so ke yanzu baki da wayon komai? Kamar ba mace ba amma na san me zan miki so nake Allah Ya bani lafiya inji saukin jikina sai na gyara miki zama komai sai na koya miki."

"Mami kiyi hakuri ki daina magana dan Allah ."

Hararta tayi ta muskuta "Haushi kike bani Wallahi komai baki sani ba sai kace wata doluwa ni haka kika ga ina yi komai bazaki koya ba ashe kuwa za ki zama bora Wallahi."

Ta san Mami da mita shi sa bata kuma cewa uffan ba har Abban yazo suka dauki hanyar gida tare.

TUN RAN GINI TUN RAN ZANE.Where stories live. Discover now