7️⃣1️⃣➖7️⃣5️⃣

172 14 0
                                    


💞PRINCESS JAWAHHIR 💞

Wattpad
Mk_princess✍

7️⃣1️⃣➖7⃣5️⃣

Kawai sai yaga ta dan runtse ido ta bude ta kalle shi kamar me koyaon magana tace da zafi fa....

Ay kamar wanda akai ma albishir da aljanna ya wani rikice da sauri ya kama hannunta yace so sorry baby da zafi...

Kai kawai ta gyda mai....

Wata ajiyar zuciya yayi turo kofar akayi S I ne ya shigo yace dama nasan kana nan kamanta kanada cs ne anje office dinka baka nan...

Kallon S I yayi da murmushi yace Alhamdulillah baby ta min magana...

Kallon sa kawai SI yayi girgiza kai a zuciyar sa yace Allah sarki bawan Allah ya kamu har wuya bai sani ba zuwa yayi gabansa ya dafa shi yace haba maza kana abu kamar ba dr ba ganin bata magana ay dama ba wai ta dena magana gaba daya bane kuma dan tayi magana bawai zai zama sabon abu bane any way Alhmdllh haka ake so dama kuma in sha Allah komai zai zama daidai....

Kuma dama ina so na gayama result dinta na ECO da ECG da mukayi Alhamdulillah shima mun same improvement sosai Dan haka Dan Allah ka rage damuwa abokina be a man mana haba namiji ya hada yana Dan tsokanar sa....

Murmushi kawai yayi ya juya yana kallon ta kofa aka bude su khalil ne suka dawo khalil ne yace basaraken dr number ka ta fito ana nemanka kai naga alama idan kana gaban babyn nan taka baka ji baka gani ya fada da sigar tsokana....

Dariya salma ta ke kasa kasa harararta yayi yace meyasa bakya san yi mata hira...

Zare ido tayi tace yaya hira kuma bayan kasan bazata kula ni ba bama zata saurara ba shiyasa nikuma sai naga kamar ina takurata idan ina mata magana bata ko kallona bare ta nuna tanajin me nake cewa..

Nasani amma gashi ni yanzu tamin magana kuma ta amsamin da na mata magana....

Da expression tace da gaske me tace maka cikin jin dadi yayi murmushi yace tace min da zafi ya fada yana mike wa kallonsa kawai suke dan su basu gane me yake cewa ba ganin yadda suke kallonsa sai ya basu labarin yadda sukai da ita khalil yace Alhamdulillah wannan ay abunda muke nema ne ya samu gaskiya ne basaraken dr salma ki rinka kokarin yi mata magana ko bazata amsaki ba wata rana zata amsa kai kuma oga tunda an samu cigaba sai ka rinka kokartawa duda dai naga patiant din nan taka tana so ta hanaka aykin ka....

Murmushi kawai yayi ya fita be basu amsa ba.....

Wannan kenan 📝

✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Meerah ta gama hada kaya yau jirginta zai daga abuja suna zaune a parlo mama tace ki bude kunnan ki da kyau ki jini in kinje mun gama magana da mommy ki a kayanki na hada miki da wani sako ki kai mata sanan meerah ki Kama kanki kinga dai yaron nan ta karfi akai masa ba a sanransa yake son auren nan ba duda dai Akwai abinda zamuyi kafin aure kuma zaki sha mamaki zai soki fiye da du wata mace a duniya ke dai du abinda mommy ki tace kiyi Kwai kiyi kinjini....

Cike da murna tace an gama hajiya fulani me babban daki wlh ina son ki uwata....

Dariya take tace ja'ira ba dole ki soni ba nima ina sonki diyata.. Tashi ki tafi karki makara idan kin isa ki kirani ki gaida mommyn...

Ma aykatan gidan ne suka kwashi kayanta aka kai mota driver ya dauke ya kaita airport jirginta ya daga abuja....

✴✴✴✴✴✴✴✴✴

Yau Aunty sadiya ta iso garin soyaki ita da yaranta muhd, Afrah, da Arif.. An dakko su daga airport suna zuwa place yaran da murna suka shiga bangaren ummah suna murna da murna ummah ta tare su sunata zuba mata suruta Aunty sadiya ce ta shigo tace yanzu kai Muhd ba zaka dena wannan halin ba ji yadda ka barni ina ta neman waya ta a mota ashe kai ka dakko min ko bani wayata....

JAWAHIRWhere stories live. Discover now