LABARINSU 4

27 0 0
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*04*
~~~
_-*What she really craves is a wild love, from a steady pertner...*-_
***
*1987*
Alhaji Ali Wakili, babban mutum ne me tarin arziƙi. Haifaffen garin haɗejia ne, kuma ya ci gaba da zama a cikin garin har bayan lokacin da ya fara tara iyali. Kasancewarsa mutum me nasibi a harkokin kasuwancinsa, yasa shi gyara gidansu na gado, ya ci gaba da zama a ciki shi da 'yan uwansa.
Alhj Ali na da mata biyu, hajiya A'i, yaransu tara da ita mata biyar maza huɗu, matan sun haɗa da Lawisa, Fatsima, Kaltume, sai 'yan biyun gidan, Maryam da Rabi'a, Mazan kuma sun haɗa da, Abdullahi, wanda ya kasance shi ne na farko, sai Mansur, Haladu da lawan
Hajiya Kande ita ce matarsa ta biyu, yaranta huɗu da shi, kuma dukansu maza ne, Kabir, Sagir, Jamilu da kuma Jibrin.
Duka yaran gidan suna karatu, matansu da mazansu, kuma duk da kasan cewar sun taso a gidan yawa, akwai zaman lafiya a tsakanin yaran ahalin, dan iyayensu jajirtattu ne a kan tarbiyar yaran nasu.
Rana ɗaya da gaba ɗaya ahalain gidan ba zasu manta da ita ba ta kasance Asabat, inda labari ya riske su cewar an yi wa Rabi'a 'yar biyun Maryam fyaɗe.
Duk wani nau'i na tashin hankali babu wanda bai yi ba a gidan, dan da aka tambayeta ta shin san wanda ya mata fyaɗen?. cewa ta yi bata sani ba, dan hankalinta a gushe yake. Haka aka gama jajjaɓin lamarin kafin aka watsar da zancen, kowa ya ci gaba da lamuransa.
Bayan kwanaki da faruwar lamarin, Alhj Ali ya nemawa Maryam gurbin karatu a garin Suleja, dan haka ta tafi can ta ci gaba da karatunta. Watanta ɗaya da tafiya, alamun samuwar ciki suka fara bayyana tattare da Rabi'a.
Tun tana ɓoye abun har ya zo ya bayyana, har kowa na gidan ya sani. Alhaji Ali ya yi tsallen albarka ya ce sai dai a zubar da cikin. Itama kuma Rabi'a ta yi tsallen albarka kan cewar ba za ta zubar da cikin jikinta ba, hakan yasa shi kuma yace sai de ta bar masa gidansa.
“In dai har ba za ki zubar da cikin jikin ba sai dai ki bar min gidana Wallahi!...”
Haka ya faɗi, a ranar da yake watso mata kayanta ƙofar katafaren gidan nasu. Gaba ɗaya mutanen gudan sun firfito, an tsaya a bakin gate ana kallon abin da ke faruwa.
Babu yanda yayun Alhaji Ali ba su yi da shi ba kan ya yi haƙuri, amma ya ce Wallahi sai Rabi'a ta bar masa gidansa, dan baza'a haife cikin shege a gidansa ba. Ba zata ɓata masa sunan zuri'a ba.
Rabi'a ta tsugunna ta tattare sauran kayan da Abban nata ya watso mata, sannan ta haɗe su a wuri ɗaya, tana ta sharar hawaye. A hankali ta miƙe ta kalli idon Abban nata.
“Da na zubar da cikin jikin, gwara na bar maka gidanka Abba.... Ba zan roƙi ka bar ni na zauna a gidan ka ba, abinda ya sameni ƙaddara ce daga Allah, kuma shi ne zai temakeni na iya cinyeta.....Ni dai buƙa tata ita cee ka yafe min Abba!....”
Ta ƙarashe tana fashewa da kuka, babu wanda bai ji tausayinta ba a wurin, amma banda Alhaji Ali, wanda ya kawar da kansa gefe, ya gwammace da ya sallamarta, da ta ja masa a bun kunya, ace yau a gidansa aka haifi ɗan gaba da fatiha?, kuma ace 'yarsa ce ta cikinsa?.
“Na san ba lalle ka yafe min ba, amma ni dai ina meneman yafiyar taka, zan yi nesa da kai, zan yi nesa da gida, zan je na haife cikin jikina, kuma zan basu labarin abinda rayuwata ta fuskanta sakamakon fyaɗen da aka min ba tare da san rai na ba...Yaran da aka haifesu ba tare da aure ba suma 'ya'ya ne, ƙaddara ce ta hukunta zuwansu ba tare da auren ba!...”
Ba tare da ta sake cewa komai ba ta ɗauki sauran kayanta tana ta sharar hawaye, ta kama hanyar barin unguwar tasu.
Sai da ta yi tafiya mai nisa, sannan ta ji muryar mahaifiyarta na ƙwalla mata kira. Cike da mamaki ta juya.
Da gudu ta ruga wurinta tan kuka, suna haɗewa ta faɗa jikin mahaifiyar tata tana sakin sabon kuka, Ita ma Hajiya A'in kukan take. Kafin ta share hawayenta ta ɗago da 'yarta. Hannunta ta kama sannan ta danƙa mata wata jaka.
“Akwai kuɗi, da takardun karatunki a ciki, sannan akwai takardun gidana na kano a ciki... Ban ce ki faɗawa kowa inda za ki ba.... Ni dai ina so ki je ki kafa sabuwar rayuwarki a garin kano, idan zai iyu bayan kin haifi yaranki, ki yi aure Rabi'a!.....”
Rabi'a ta ƙara faɗawa jikinta tana sakin sabon kuka.
“Aure be dace da ni ba Mama, sanin kanki ne babu namijin da zai auri macen da ta yi ciki ba tare da aure ba”
Hajiya A'i ta shiga kwantarwa da 'yarta hankali, tana haɗa mata da nasiha, har zuwa lokacin da suka yi sallama. sallamarsu ta ƙarshe kenan.
Rabi'a ta isa garin Kano lafiya, kamar yanda mahaifiyarta ta buƙata ta sauƙa a gidan da ta bata takardunsa, sai dai gidan babu kayan buƙata a cikinsa. Dan haka washe garin ranar da ta sauƙa a garin Kano, ta fita ta je ta yi siyyayar kayan da zata buƙata na amfanin gidan. Bayan ta samu sati biyu a garin, ta shiga fafutikar  neman aiki, cikin sa'a ta samu aiki a wata asibiti, kasancewar aikin nurse ta karanta.
Haka rayuwarta ta ci gaba da gangarawa ita ɗaya, kullum cikin ƙunci da tunanin gida, Allah ya sani tana kewar gidansu, sai dai kuma ba za ta iya rabuwa da cikin jikinta saboda san gidan da take ba.
Sau tari ta kan zauna ta yi tunani a kan rayuwarta, da ma haka duk macen da aka mata fyaɗe ba tare da san ranta ba rayuwarta ke kasan cewa?. Kowa ya na nuna mata ƙyama, saboda kawai Allah ya ɗora mata ƙaddara?.
Watan cikin jikinta tara dai-dai, naƙuda ta tashi mata, Allahn da ya temaketa tana asibitin da take aiki a ranar, dan ba ta wani ɗauki hutu ba. Kuma ita kaɗai take rayuwarta, babu ruwanta da kowa a unguwar da take zaune ko a asibitin. Cikin ikon Allah ta sauƙa kafiya, ta samu yaranta 'yan biyu maza.
Bayan ta dawo hayyacinta ne ta raɗa musu suna da kanta, na farkon ZAID, na biyun kuma ta saka masa ALIYU.
Ba ta yi taron suna ba, dan bata da wanda za ta gayyata, mahaifiyarta kawai ta kira a waya ta faɗa mata. Hatta da Maryam, 'yar uwarta, kuma abokiyar tagwaitakarta, wadda ta fi shaƙuwa da ita fiye da sauran 'yan uwanta bata da masaniya kan inda take. Ita kanta Hajiya A'in taƙi faɗawa kowa inda Rabi'an take ba.
Duk da wahala irin ta renon tagwaye, haka Rabi'a ta reni yaranta ita kaɗai. Sosai take nuna musu soyyaya da kuma basu kyakyawar tarbiyya. A koda yaushe tana nuna musu su so juna.
Haka yaran nata suka taso masu tsananin kama da juna, banbancinsu a hallita biyu ne, shi Zaid yana da ash ɗin ƙwayar ido, yayin da Aliyu tasa take brown, sai kuma totsiyar karen dake a bakin Zaid, wadda shi Aliyu ba shi da ita.
Haka kuma halayensu sun banbanta, dan Zaid yaro ne me sanyin hali, ga haba-haba da jama'a, amma Aliyu mugun muskili ne, babu ruwansa da yawan magana, ga masifa, da saurin fishi.
Kuma har suka yi wayo ta saka su a makaranta, a cikinsu babu wanda ya taɓa tambayarata ina mahaifinsu. Ko a makaranta ma da sunan junansu suke amfani, shi Aliyu amfani da Aliyi Zaid, Zaid kuma yana amfani da Zaid Aliyu.
Tana ƙara nusar da su cewa ba su da kowa sai junansu. Suna primary 5 ne, Zaid ya taɓa tambayarta ina mahaifinsu. Kuma bata ɓoye musu ba, a lokacin ne ta sanar musu da komai da ya danganci ita kanta da kuma su.
Suna da shekara goma sha ɗaya, wata rana sun tafi islamiyya. Rabi'a na kitchen tana girki. Bayan ta gama girkin sai ta manta bata kashe gas ɗin ba. Ta koma ɗakinta ta shiga wanka.
Ta ɗau tsawon mintuna a banɗakin. Kafin ta fito, kuma tana fitowar, ta ji ƙauri na tashi, kamar wani abu na ƙonewa, hakan yasa ta fito falo, don ta duba abin da yake faruwa, me za ta gani?. Gaba ɗaya kitchen ɗin ya kama da wuta, kasancewar a falo kitchen ɗin yake. Har ya bawa falon, yana ƙoƙarin kama ɗakuna, a lokacin hankalinta ba ƙaramin ta shi ya yi ba . Ga shi labulayen ƙofar falon sun kama da wuta, babu damar ƙarasawa jikin ƙofar bare ta buɗe.
Haka ta dawo ɗakinta ta shiga kai kawo na neman mafita. Bata ankara ba har ɗakin ma ya kama da wutar. Ta shiga kiran mutane domin a kawo mata agaji, sai de babu wanda yake ji, bare a kawo mata agajin, kamar yanda take buƙata.
Kuma a lokacin ne, Aliyu da Zaid suka dawo daga makarantar. Tun daga ƙofar falon suka ga wuta na ci, hankalinsu ya tashi sosai, suka shiga kiran sunan mahaifiyar tasu tun da sun san cewar tana cikin gidan.
Jin kiran sunanta da suke ne yasa Rabi'a ta shiga amsawa tana kiran sunayensu, bayan gidan suka zagaya, jin muryar mahaifyar tasu na futowa daga can, dai-dai tagar ɗakinta suka tsaya. Kuka suka ci gaba da yi suna faɗin ta fito daga cikin gidan kada wuta ta ƙonata.
“Zaid, ku tafi, kada ku tsaya a nan...idan kuka tsaya wutar zata iya ƙona ku... Ku tafi nace!.....”.
Fitar suka yi, sannan suka shiga neman wanda zai temaka ya  zo ya fitar musu da mahaifiyarsa.
Kasantuwar unguwar tasu babu kai kawon mutane da yawa, kuma su ba gidan kowa suke shiga ba, yasa saida suka jima, kafin suka samu wasu maza suka shiga gidan suka ga abinda ke faruwa.
Ko da aka kashe wutar har ta gama ƙona ko ina ƙurmus, ta ƙona komai na gidan, ita kanta Rabi'an haka aka fito da ita babu rai a jikinta...
*Present day.....*
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger state*
RABI'A POV.
_🎶Ramadanal kareem, ramadanal kareem!_
_Watan ramadana, wata mai alfarma......🎶_
A hankali waƙar ke tashi ta cikin radion da Habiba ke sauraro. Zaune take a kan tabarma tana dudduba kayan ɗinkinsu Mama na sallah da aka kawo daga shagon ɗinki, don yau jajiberan sallahr. Mama, Fati da Mahmud sun kewaye da ita, kowa na gwada nasa a jikinsa.
Rabi dake zaune daga can bakin murhu tana soya musu kajin da za'ayi miyar sallahr da su sai satar kallon kayan nasu suke.
Don Allah ya sani, tana kewar samun sabon kaya, kayan Mama sun fi mata kyau, ta san da cewar kuɗin albashinta na makarantar da take aiki da shi aka musu dinkunan, amma ita da take shan wahalar aikin ko fallen zani na atamafa roba ba'a samu arziƙin siya mata ba.
Ta juya kanta tana tsame kajin da suka soyi daga cikin mai.
“Salamu alaikum... Rabi wai ki zo in ji Yaya!”
Wani yaro me zaƙin baki ya faɗi yana shigowa cikin gidan. Rabi ta juyo ta kalli yaron. Yaya?, wani mutum ɗaya a duniya da yake santa a yanda take. Yake santa duk da ita ba kowa ba ce. Yake nuna mata so duk da ita bata da komai.
Kuma ita ma ba za ta yaudari kanta ba, tasan cewa tana sansa, dan ba ta ga wani bayan shi ba, to ina ma za ta samu ?, waye zai so ta a haka ?, ta sani cewar ita ba mummuna ba ce, tana da kyau dai-dai nata, amma ai hausawa ma sun ce idan kana da kyau ka ƙara da wanka.
“Je ka ce ba za ta zo ba!”
Muryar Habiba ta katse mata tunani, juyawa ta yi suka haɗa ido, a take ta watsa mata wani mugun kallo. Rabi'a ta yi saurin ɗauke kai, wani abu na taruwa a maƙoshinta.
“Rabi! Ɗan siyo min kati dan Allah”
Muryar Saratu ta faɗa, a sanda ta fito daga ɗaki, sai da Habiba ta harareta sannan tace.
“Ba zata je ba, ba ki ga aiki take min ba?”
“To tunda ba za ta je ba, Mama ko Fatima wani ya siyo min a cikinsu”
“Ba ta ta siyo miki, ba inda za su fita”
Habiba ta faɗi a dake. Saratu ta sunkuya tana kallon Rabi'a cikin murmushi, da ido kawai ta mata alamu da ta tafi.
Rabi ta miƙe har da murmushinta ta fita, dan dama da hijabinta a jikinta.
“Mama ta shi ki ƙarasa suyar nan...”
“Wallahi Umma ba zan iya ba, ga Saratu nan, sai ki sa ta ta soya”
“Eh kuma haka ne, Saratu, tun da kin tashi ita me suyar, ke sai ki ƙarasa”
Saratu ba ta ce mata komai ba, ta girgiza kanta tana takaicin halin mahaifiyar tasu da ƙanwarta, ta zauna ta ci gaba da suyar.
“Na yi zaton ba za ki fito ɗin ba ai...”
Sassanyar muryar Yaya ta faɗi, yayin da yake kallon fuskar Rabi'a. Ta ɗan yi murmushi kaɗan tana sinnekai.
“Umma ce ta sa ni aiki, shi yasa”
Ya langwaɓe kai gefe yana faɗin.
“Allah ya bani kuɗin da zan aureki Rabi'ata, dan na gaji da ganinki kina wahala a banza, Gwara na aureki ki je can gidana ki yi bautar me lada!...”
Ƙwalla ta taru a idon Rabi'a, amma sai ta shanyeta, don ko kaɗan bata so ta zubo.
“Gobe sallah, me kika tana da min ?”
Ta ƙara sunkuyar da kanta. Warin wannan bolar na cika hancinta, don Allah ya sani bata san zama a ƙofar gidansu.
“Babu komai”
“Na sani ai, shi yasa ni na samu na ɗan ɗinka miki kala ɗaya da hijabi, ki yi haƙuri ba yawa Honeyna!”
Abubuwa biyu ne suka karya zuciyar Rabi'a lokaci guda, ɗinkin da yace ya mata, da kuma sunan Honeynsa da ya kirata da shi, wannan ƙwallar da take ta ƙoƙarin riƙeta ta sauƙo mata.
Ta ɗago da kanta ta kalli fuskar Yayan, sannan ta kalli kedar da yake miƙa mata.
*
Tsabar murnar samun sabon kayan da take ranar kasa bacci ta yi, daga ta ɗan jima a kwance sai ta miƙe zaune ta janyo ledar kayan ta duba su, ta kuma mayar wa.
Allah ne kaɗai yasan yanda ta yi farin cikin samun kayan, shi yasa a har kullum take taya Yayyan da addu'a kan Allah ya buɗa masa, har ya samu kuɗin da zai kawo a aura masa ita. Duk lalacewr auren yafi zaman gidansu.
“Ka zo?!...”
Kamar daga sama ta ji muryar Mama, hakan yasa ta buɗe idonta dake a lumshe, ta cikin net ɗinta ta hangi fuskar Maman, wadda ta yi kwalliya a cikin daren Allah ta ala.
Wasu tsukakkun riga da wando ne a jikinta, ga kitson attachment ɗin da takanas ta tashi ta je aka mata shi, ta zube shi a bayanta, ta caɓa wata uw*r kwalliaya, kamar me shirin zuwa gidan bikin, gidan bikin ma irin na kece rainin nan.
“Ka ɗan ƙara matsawa gaba... kasan ni bana san sa ido, kar ka ga dare ya tsala, akwai munafukai masu bacci da ido ɗaya”
Ta kuma faɗi ta cikin wayar da take.
“Ok to bari na fito...”
Kuma daga haka Maman ta sauƙe wayar da ke riƙe a hannunta, ta gyagyyara jikinta, sannan ta kashe wutar ɗakin ta fita.
Rabi ta ƙara dunƙuƙunewa a cikin bargonta, don bata ma so Maman ta san cewa ta farka. Abin da ake zarginta da shi, shi ne 'yar mai zargin nata ke yi.
*No.181, Garki 2, Abuja....*
*10:00pm*
KULIYA POV.
A hankali ƙafafunsa suka taka cikin falon gidan. Abu na farko da ya yi shi ne kunna wutar gidan gaba ɗaya.
Kafin ya ƙaraso cikin falon, ya sauƙe ledojin da ya shigo da sua kan sofa. Sabbin kayan da ya siya zai saka idan zai je idi. Kuma kafin ya taho gidan nasa sai da ya biya ta gidan Anna, ya kai mata nata kayan idin. Sai ledar da Annan ta saka masa abinci a ciki, don haka tace yana buƙatar ya riƙa cin abincin gida, ba na kanti ba.
Kuma haka ɗin ne, bayan farin ruwan sanyi da ya sha a office lokacin da aka yi buɗa baki bai saka komai a cikinsa ba. Dan shi ba iya girka abinci ya yi ba, idan har ba gidan Annan ya je ba to sai dai ya yi order a wani restaurant da ya saba siyan abinci.
Idan kuma aiki ya sha masa kaibama ya samun damar cin abincin. Dan bai damu da shi ba, shi yasa ulcer tai masa kamun kazar kuku.
“Ayra!, Ayra!....”
Muryarsa ta shiga kiran sunan a hankali, kamar ba shi ba, yana yi yana dudduba ƙasan kujeru.
Da gudu kuliyar tasa ta fito daga ƙasan wata kujera, sannan ta iyo kansa. Wata hallita ɗaya a duniya bayan Anna da take iya ganin farin haƙorinsa cikin murmushi ko dariya. Shi kansa yaan cewa ba kasafai yake murmushi ba ma balle a je ga dariya. Murmushin ma baya yi sai idan ya yi nasara a aikinsa.
A ƙasa ya zauna, sannan ya kamo kuliyar tasa yana shafa kanta.
“Kina jin yinwa ko ?”
Ya tambaya kamar yana magana da mutum, don shi ɗaukarta yake kamar ƙawa, saboda bayan me gadin gidan, sai wata tsohuwa dake zuwa tana masa shara a gidan duk sati, babu wani abu mai rai dake rayuwa a gidan sai ita.
Ledar da Annan ta saka masa abinci ya janyo, sannan ya fiddo da abincin da Annan ta zuba masa.
Ya buɗe flask ɗin, ya zubawa Kuliyarq a murfin flask ɗin, ya tura mata gabanta, nan take ta hau ci.
Shi ma gefe ya koma ya zauna ya fara cin nasa abincin. Yana tunanin yanda ayyuka za su masa yawa a satin nan, dan abokinsa kuma abokin aikinsa ya ɗauki hutun bikin sallah. Saboda haka duka ayyukan Abubakar ɗin shi ne zai ƙarasa. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama. Yana kai lomar abincin bakinsa, idonsa a kan Ayra, yadda take ta famar cin abincin ne kaɗai zai nuna maka cewar a matse take da abincin.
Bayan sun gama cin abincin, ya ɗauki Ayra tare da ɗorata a kan kafaɗarsa, sannan ya ɗauki sauran kayan nasa na ledar, ya shiga ɗakinsa.
A kan gado ya zube ledojin, kafin ya aje Ayra kusa da ledojin, Ya juya zuwa walk-in closet ɗinsa. Bayan ɗan wani lokaci ya fito, ya shiga banɗaki.
Wanka ya yi, ya fito bayan ya sauya kaya. Daga suit ɗin da ya shigo da ita zuwa wasu baƙaƙen shirt da wando na pyjams.
Ya dawo ya zauna a kan gadon yana fitar da kayan idin nasa. Kamar yanda ya saba duk shekara, baƙar shaddace guda ɗaya, sai wani baƙin voil, hulunan ma baƙaƙe ne babu ratsin wata kala ko guda a jikinsu. Haka takalman ma baƙaƙe ne guda biyu, dan shi ba wasu manyan kaya yake sawa ba, sai lokaci irin wannan idan ya zo, hatta da sallar juma'a ba da manyan kaya yake zuwa ba.
Miƙewa ya yi ya koma closet ɗin. Wani  abun mamaki shi ne, gaba ɗaya kayan cikin closet ɗin baƙaƙe ne, kamar na mai shirin zuwa jana'iza.
A rayuwarsa ba ya saka wani kaya mai kala, duka kayansa a duniya baƙi ne, motarsa baƙa, kayan sakawarsa baƙaƙe, hatta da case ɗin wayarsa baƙi ne.  Bayan ya aje kayan, ya fito ya zauna a kan work table ɗinsa, ya shiga yin sauran aikin da ya dawo gida da shi.
*Dambuwa road, Maiduguri...*
MISHAL POV.
Zaune take a ɗakin da yake a matsayin nata. Don ba yau suka saba zuwa Maidugurin ba, hasalima suna zuwa akai-akai. Kuma idan sun zo ɗin a babban family house ɗinsu suke sauƙa.
Duk da kasancewar gobe sallah, amma gidan har yanzu be rabu da zuwan baƙi ba. Tun daga hayaniyar dake tashi a gidan za ka gane hakan.
Ba su dameta ba, Don Kullum ba ta fita, tana ɗaki, bata san ta fita su haɗu da Yazid. Yazid?, wani mutum da ya so lalata mata rayuwa, wannan mutumin da duk duniya bata tsani wani mahaliƙu kamarsa ba.
Shi ne wannan mutumin da a sanadiyyarsa ta gamu da ciwon hysterian da take da shi a yanzu. Kuma dan abun a family ya faru, haka aka rabu da shi ya ci gaba da yawonsa. Yana shiga cikin 'yan uwa kansa ɗage a sama, kamar bai aikata komai ba.
Ita kuma da aka yi ƙoƙarin cutarwa ita ce ke ɓuya, ita ce ke ɓoye kanta da barin shiga dangi, har yanzu gani take kamar idan ta idan ta shiga cikinsu suna ganin wannan tabon a jikinta ne. Duk da Allah bai sa ya haike matan ba, amma tana jin zafin abinda ya mata a ranta. A duk sa'ar da za ta ganshi ji take kamar ta fasa ihu, a wasu lokutan ma ganin nasa kawai shi ne ke tada mata ciwonta.
Ta ɗan ja gutun tsaki tana ci gaba da buɗe littattafanta. Ita ta tsani aikin makaranata, dan de ba ta san ɗan uwanta ya yi asarar kuɗin da yake kashewa a kan makarantar ta a banza, amma da ba za ta na maida hankali ba.
Gashi dai hutun sati ɗaya a ka bayar, saboda ba ƙarshen term ba ne, a tsakiyar term aka basu hutun, amma sai da suka haɗo su da holiday project.
Kuma tun barowarsu Abuja abun da take ta ƙoƙarin yi kenan. Amma har yanzu ta kasa gamawa.
Ta kuma jan wani tsakin tana ture littatafan, duk aikin ya gundureta, fita take san yi, bata san zaman gidan gaba ɗaya. To amma ta fita ta je ina ?, ta san in ma fitar ce ba za'a barta ta fita ita ɗaya ba, dole za'a haɗata da wani.
“Baby!”
Kamar daga sama ta ji muryarsa yana kiran sunanta, sunan da kaf duniya babu me kiranta da shi sai 'yan gidansu. Tasan da cewa za su zo, amma ba ta san cewa yau za su zo ɗin ba.
Da sauri ta miƙe ta fita daga ɗakin, a falo ta same shi yana ta nemanta. Yana ganinta ya sakar mata wani kyakkyawan murmushin. Da gudu ta ƙarasa kusa da shi, kuma tana zuwa jikinsa ta ɗale shi, duk tsayinsa amma saida ta riƙe masa wuya.
“Tun sanda muka zo nake ta nemanki”
Wannan dakakiyar muryar tasa ta faɗi. Ta yi kewarsa da ma duk wani ɗan gidansu, dan za ta iya cewa duk familynsu babu wanda take so kamar 'yan gidansu, duk da su ma a Abuja suke da zama,amma bata gajiya da ganinsu.
Sunansa Arman, ɗa ne a wurin cousin ɗinta Nimra, wadda ta kasance soja me riƙe da muƙamin general na nigeri. Yaranta uku Arman, Iqra sai Ijaz, kuma gaba ɗaya yaran nata sojoji ne. Wani abu dake ƙara burgeta da gidansu kenan.
“Ina Iqra da ijaz?”
Ta tambaya tana sakinsa. Kanta a sama wurin kallon fuskarsa, sbd tsayin da ya fita. Kasancewar shi dogo ne, ita kuma gata ba wani tsayi gareta ba.
“Suna waje, har da su Ammy muka taho”
Zuciyarta kamar ta fito waje don murna, Allah ya dubeta yasa ba za ta yi bikin sallah lami ba, dan tunda har duka mutanen gidansu suka zo, to shikenan, matsalarta ta zaman kaɗaici ta yanki.
*Unguwar Madallah, Suleja, Niger State*
*07:44am*
RABI'A POV.
Ba ƙaramin farin ciki take ciki ba, kallo ɗaya za ka mata fahimci hakan, saboda daga kun haɗa ido za ka ga ta maka murmushi,  duk da dama ita gwanarsa ce. Amma na yau ya fi na kullum. Jin kanta take kamar kowa, yau Allah yasa ita ma ta saka sabon kayan da za ta tafi idi da shi.
Saɓanin sauran shekarun da ta shafe a gidan, a da sai dai Saratu ta bata kunce ta saka. Amma yau ita ma gata da nata sabon kayan, sai dai duk da haka bata da takalmin sakawa, shi yasa Saratu ta bada ɗaya daga cikin nata, Da murnarta ta zangari takalmin ta saka.
Tun da ta fito daga wanka ta saka kayan Mama ke binta da kallo, amma ba ta ce komai ba, har suka shirya suka fito dan tafiya wurin idi.
Rabi ba ta san sanda Mama ta dawo gidan ba, ita dai kawai ta farka ta ganta. Kuma ba ta ce komai ba, ta ja bakinta ta yi shiru, tun da har uw*rta tasan abin da take.
A bakin ƙofar ɗakinsa suka ga babansu, kowa a cikinsu ya wani ɗauke kai babu ma mai shirin gaishe da shi, sai Saratu da ita, kuma shi ma bai wani amsa musu da mutumci ba, sama-sama ya amsa su.
Ita kuma Rabi ba ƙaramin mamakinsa take ba, kusan kwanansa huɗu baya gidan, ko jiya har suka kwanta ba ta ga dawowarsa ba, wata ƙila ma da asuba ya dawo, don ba ƙaramin aikinsa ba ne. Mutumin da ya taɓa kawo karuwa cikin gidan matarsa ta auren sinnah, ai fiye da haka ma zai aikata..
“Ah-ah, Karfa, a ina kuma kika samo sabon kaya ?, in ji dai ba sata ki kai ba?”
Muryar Habiba ta katseta, hakan yasa ta juyo da sauri ta kalleta. Rabi ta tsorata, dan jiya basu san an bata wani kaya ba, tana shigowa da ahi ɗaki ta shige, Anti Saratu kawai ta nunawa.
“Saurayinta ne ya kawo mata, ba sata ta yi ba”
Saratu ta bata amsa.
“Sh*iya munafuka! Ashe jiya da kika je siyan katin tsayawa ki kai a lungu ya gama lalube ki sannan ya baki kaya?”
Habiba ta faɗi cikin kama baki.
“Ai ni na jima banga baƙar munafuka irin wannan yarinyar ba, kin ga fa jiyan da ta dawo, ɓoye kayan ta yi a cikin hijabinta, dan kada mu gani”
Mama ta faɗi tana aika mata harara.
“Ya isa haka dan Allah, to duk sharrinku a ƙofar gida ya bata, da za ku ɗorawa marainiyar Allah shari, dan Allah Umma ku riƙa duba baya, idan an giram a san an girama”
“Kan abu ta kaza-kazacan!, Saratu! Ni ki ke faɗawa irin waɗanan maganganun ?.....”
Sararu ta juyar da kanta gefe daga barin kallon Umman, ta kalli Rabi wadda hawaye suka wanke mata fuska tun a sharin farko da aka laƙa mata.
Hannunta ta ja suka fita daga gidan, dan ta ga kamar su basu da niyyar zuwa idin, su da suke da niyya gwara su yi sauri, don kada su rasa.
Da sauri Ɗan Lami ya bi bayansu, dan ko ba komai yasan akwai 'yan kuɗaɗe a hannun Saratu, shi kuma kuɗaɗen da ya ara sun ƙare kaf, bai ta shi da ko sisi ba. Kuma gashi yana san zuwa idin, ko ba komai Saratun za ta masa kuɗin babir.
“Umma da alama fa sai kin ɗau mataki...”
Cewar Mama.
“Ni kuwa na ga hakan, kada ki damu, zan ɗau ƙaƙƙwaran mataki kuwa”
“Ke Fati, uw*r me kike a ɗakin ne?, dallah ki yi sauri ki fito”
Mama ta faɗi cike da masifa tana kallon ƙofar ɗakinsu, Habiba ta shiga soshe-soshen ƙeya.
“Amm, Mama na ce Alhajin jiyan nawa ya baki ?”
Mama ta juyo ta kalleta tana haɗe rai.
“Ni ba na san bita da ƙulli, dubu hamsin ne, ya ce babu kuɗaɗe a hannunsa, zan baki dubu biyar kawai...”
Habiba ta yi murmushin yaƙe.
“Haka ne, amma dai an kinsa dai ko kuɗin ɗinki shaddara da na ɗinka miki a sallar nan ya fi dubu biyar...”
“Ni fa Umma na gaji da gorin da kike min!, kawai dan kina min ɗinki sai ki kafa bina da bita da ƙulli?... Da na ce dole sai kin min ɗinki?... Idan ba ki min ba ma samari na za su min ai!”
Kamar Maman ita ce uwa haka takewa Habiban faɗa.
“Haba Mama, abun fa ba na ɓacin rai ba ne, ki kwantar da ranki mana”
Mama ta ƙara juya kai tana huhhura hanci.
Ƙarshen zamanin kenan, dama an sanar da mu cewa; baiwa za ta haifi uwar gijiyarta,to ga kyakkywan misali nan Habiba da Mama.
Sannan an ce abun da ka yi shi za'a maka, hakan ce ke faru da rayuwar gidan Ɗan Lami, amma shi sam bai lura da hakan ba, dan ba iyalan nasa ne a gabansa ba.
(Allah ya fihsemu turba mai kyau🙏).
Bayan an sauƙo da ga idi, Saratu da Rabi gida suka dawo, in da Mama ta wuce yawon gantalinta, Habiba da su Fati ma gidan suka dawo.
Kuma tana dawowa ta laftawa Rabi aikin abincin sallah, haka Rabi ta cire sabon kayanta ta hau aikin ba ji ba gani, duk da Saratu na tayata da wani abu.
Da haka har suka yi suka gama, kuma bayan sun gama ba'a bawa Rabin abincin ba, sai kusan la'asar aka ɗan zuba mata kaɗan a kwano, wai duk dan a ƙuntata mata.
Naman da kajin data soya ma ba'a saka mata ba, sai wanda Habiban ta ci ta bari, kuma ita hakan bai dameta ba, don bata damu da cin kaza ba, tafi san kifi, kaza bata birgeta a rayuwa.
Duk da haka sai da Anti Saratu ta ɗiba mata naman ta bata, tace mata ta ci, ai da kuɗin da ta nema aka sayi naman. Bata san yi mata musu shi yasa ta ci ɗin, ba wai don naman ya mata daɗi ba.
Da la'asar Zara ta shigo gidan tace ta zo su je yawon zaga gari, da farko sai da Habiba ta hana, amma da Saratu tayi uwa tayi makarɓiya sai ta haƙura ta barta.
A wurin Rabi wannan sallahr ta musamman ce. Saboda tana cikin farin ciki, komai na tafiya mata dai-dai. Har ta fara ganin kamar wahalarta ta ƙare a rayuwa.
Abun da ba ta sani ba shi ne; wasu abubuwan ma yanzu ne suka soma, wata wahalar ma bata shigeta ba tukkuna, wani ciwon ma bai sameta ba har yanzu!.
Wani sabon kukan ƙunci da damuwa na nan tafe a gaba. Akwai ƙunci da baƙin ciki a rayuwa, akwai damuwa da iftila'i a rayuwa, akwai damuwa a akan wata damuwar.
Ƙaddarar kowa da ban ce, kamar yanda Labarin kowa yake da ban. Labarinta yanzu zai soma, haka mahaifiyarta ta faɗa.  Kuma yanzu zai soma ɗin.
Don ba ayi komai ba ma, labarinta zai sauya tare da faruwar wata ƙaddara mai zuwa nan da 'yan kwanaki masu zuwa, ƙaddarar da za ta sauya komai, ta tarwatsa komai, sannan ta gyara wasu abubuwan.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#Taurariwriters*LABARINSU*

#Taurariwriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now