LABARINSU 9

30 0 0
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*09*
~~~
*Someday, you will get everything you deserve, and it will be beautiful*
***
*Shekara ta 2000*
*Kano...*
“Aliyu!, Aliyu! Wai kana ina ne ?!”
Zaid ke ƙwalawa Aliyu kira, bayan da ya dawo gidansu bai tarar da shi a inda ya barshi ba, sanye yake da wannan uniform ɗin islamiyyar da ya rage musu.
Babu datti a jikin kayan, kasancewar ya na ɗaukowa ruwa a tuƙa ya musu wanki, sai haske da yadin kayan ya fara, alamun ya na jin jiki.
Hannunsa na dama riƙe da ledar ƙosan da ya samu ya siyo, bayan ya je ya yi bara a bakin titi, Bara?!, a yanzu ita ce abin da yake dan ya samu ya kawowa ƙaninsa abin da zai ci.
Sati ɗaya kawai Maman Naufal ta yi tana basu abincin da ba ya ƙosar da su, daga nan idan ya shiga gidan sai ta ɗaure fuska, har ta kai da ta ce masa kada ya ƙara shigowa gidanta.
Ga shi su kuma babu gidan da suka sani a unguwar, da ma gidan nata ne kawai suke ɗan shiga, ganin yunwa za ta lahanta masa ƙani ne yas sa ya fara barar, sai ya tafi bakin titi ya tsaya yana roƙar jama'a. Da haka yake ɗan samun abun da zai kawowa Aliyun ya ci.
To yau da safe ma ba su tashi da komai ba, hakan ta sa da wur-wuri ya fice ya tafi barar, sai da ya shafe sama da awa uku. Sannan ya samu na siyan wannan ƙosan...
Tunaninsa ne ya katse, a sabda ya ɗora idonsa a kan Aliyu dake durƙushe a bayan gidansu. Hankali tashe ya yi cilli da ledar ƙosan ya yi kansa yana kiran sunansa.
“Aliyu! Aliyu! Kai Aliyu me ya ke faruwa da kai haka ?”
Ya tambaya a sanda ya ɗago shi, ya na kallon fuskarsa da tai jawur, kasancewarsa me farin fata, ga idanuwansa sun yi ja, kuma a 'yan kwanakin Zaid ɗin ya gano cewa dukansu sun rame. Sannan ya san ba komai ba ne face yunwa, musamman ma Aliyu da sam ba ya iya jurewa yunwa.
“Yunwa kake ji ?”
Zaid ɗin ya tambaya yana miƙar da shi, da ƙyar Aliyu ya iya gyaɗa masa kai, a hankali Zaid ɗin ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya miƙar da Aliyun gaba ɗaya.
Kama shi ya yi har suka shiga cikin ɗakin da suka saba kwana, ya zaunar da shi a bakin katifarsu, sannan ya koma bayan gidan ya ɗauko ledar ƙosan da Allah ya temakesu bai zube ba, ya haɗo da wani plate da suka saba cin abinci a ciki, sannan ya ɗebo masa ruwa.
Ya dawo ya zauna kusa da shi, ya juye masa ƙosan a plate, tare da tura masa shi gabansa.
“Ka ci Aliyu”
Aliyu ya kalli ƙosan, sannan ya kalli yayansa, ƙwarin gwiwarsa, farin cikinsa, uwa, ubansa duka a halin yanzu Zaid ne.
Sai ya kai hannu ya ɗauko ƙosan guda ɗaya, me makon ya kai bakinsa, sai ya kai setin bakin Zaid.
Zaid ya kalli ƙosan, sannan ya kalli Aliyu, wata ƙwalla me ɗumi ta sauƙo masa, a hankali ya buɗe bakinsa, Aliyun ya ƙarasa saka masa ƙosan, yana taunawa hawayen na ƙara kwaranyo masa.
Ya kai hannunsa ya ɗauko ƙosan shi ma, sannan ya kaiwa Aliyun baki, Aliyu ya karɓa ya na murmushi, da haka suka cinye sannan suka sha ruwa. Sai kuma suka zauna suna biya tilawar islamiyyarsu, dan bayan faruwar iftila'in nan sun ɗan je.
A lokacin biyan kuɗin wata ne malaman suka korosu, makaranatar safe kuwa l ba su kusanceta ba, dan sunsan babu me barinsu su shiga basu da uniform, kuma ga shi term ya kawo ƙarashe. Karatun ƙur'anin dai shi suke ɗan taɓawa da ka.
Bayan sun yi sallahr azahar, Zaid yace zai fita ya nemo musu abin da za su ci na rana.
“Zaid ka tafi da ni... Ba na san zama ni ɗaya”
Cewar Aliyu ya na miƙewa, Zaid ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya, sannan yace.
“To muje”
Aliyu ya ɗaga ƙafaɗarsa ɗaya yana kama hannun Zaid. Har suka fito daga cikin gidan, Zaid ya ɗauki wani ƙyallen tsumma ya ɗaure ƙofar gidan, kana suka kama hanyar bakin titi.
Idan daga nesa ka gansu za ka ce mutum ɗaya ne, kasancewar komai nasu kala ɗaya ne, farin fatar, kyan fuskar, hatta da takunsu iri ɗaya suke, na Zaid ne kawai yafi nutsuwa. Idan wannan ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sai ka ga wannan ma ya ɗaga, abun nasu gwanin ban sha'awa.
A sanda suka fita titin, Zaid ya nunawa Aliyu wuri yace masa ya zauna, shi kuma zai je ya na barar.
Aliyu ya zauna yana kallon yayansa, yanda yake miƙa hannu yabna barar sai da ya sa shi kuka. Wai yanzu su ne rayuwarsu ta koma haka, su ɗin da suke da gata, suke da uwa, wadda ta ɗauke musu kewar uba, su ɗin da ba su nemi komai sun rasa ba, amma cikin ƙiftawar ido, komai ya sauya, LABARINSU ya sauya, rayuwar ma baki ɗayanta ta sauya.
“A taimaka mana sadaka fi sabillilahi...”
Cewar Zaid yana miƙawa wani me shago hannu, mutumin ya miƙe a fusace.
“Kai! Ba ɗazu ma ka zo ba?!...”
Kafin ya ƙarasa yaron shagonsa yace.
“Jiya ma sai da ya zo”
“Sh*ge, da ma da irinku ake haɗa baki ana mana sata, bar nan wurin!”
Ya ƙarashe yana hankaɗashi, har sai da Zaid ɗin ya faɗi ƙasa, da yake hakan ba komai ba ne a wurinsa, sai ya miƙe yana bawa mutumin haƙuri, don ba yau aka fara masa irin hakan ba.
Kamar wucewar walƙiya haka ya ga tahowar Aliyu da gudu, kuma kafin ya fahimci abun da Aliyun ke ƙoƙarin yi, har Aliyun ya yi tsallen albarka, ya kifawa me shagon nan mari.
“Kut!, Babbar buhun ub*ncan!, kayyasa! Ni ka mara yaro ?!”
Cewar me shagon yana kama baki. Aliyu da ya gama fusata a sanda ya ga an hankaɗa masa ɗan uwa yace.
“Eh ɗin, na mareka, ko akwai abun da za ka iya?”
Ya faɗi idonsa ƙyam a kan mutumin, babu wani alamun tsoro tare da shi, ji yake ma kamar zai iya kikkifa masa marin da ya fi haka, ga shi dai ba shekaru gareshi masu yawa ba, amma zafin zuciyarsa ya fi na ɗan shekara ashirin, ji yake a kan yayansa babu abun da ba zai iya ba. Ko dan sunansa Aliyu ne ?, Oho.
Zaid ya kamo hannunsa ya na jansa baya.
“Zo mu tafi Aliyu...”
“Rabu da ni Zaid, sai na nuna masa martaba da kimarka a wajena”
Nan fa me shagon nan ya shiga zage-zage yana masifa, har maƙotan shagunansa suka fito. Ɗaya daga cikin masu shagunan ne ya kamo hannunsu Zaid, ya ja su zuwa gefe.
“Ni kuwa yara ku ba 'ya'yan wannan likitar ba ne ta bayan layi ?”
Mutumin ya tambaya, yana ganin kammanin customern tasa a fuskar kowannensu. Aliyu bai iya bashi amsa ba, kasancewar zuciyarsa na tafarfasa, har yanzu ji yake marin da ya yi wa me shagon nan bai wadatar ba, kamar ya na buƙatar a ƙara masa, soboda abinda ya yiwa Zaid ɗinsa.
Zaid ne ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan yace.
“Eh, mu yaranta ne”
“Kwana biyu ba na ganinta, fatan dai lafiya ?”
Zaid ya sunkuyar da kansa ƙasa.
“Yau wata biyar kenan da rasuwarta, gobara ce ta kama a gidanmu, kuma a lokacin da gobarar ta kama tana cikin gidan...”
“Innallillahi wa inna ilaihi raji'un... Wallahi yara ban sani ba.... To yanzu ku da wa kuke zaune?”
“Ba mu da kowa, mu kaɗai ne”
“Subhannallahi, shi yasa kuke bara ?”
Zaid ya gyaɗa masa kai, don da ma shi ne yake bashi amsar.
“To kunga, ku zo ku zauna a shagona, na sai muku abinci ku ci, da yamma idan Allah ya kaimu, zan kaiku gidan marayu, ai za ku iya zama a can ko ?”
Da sauri suka kalleshi, sannan kuma suka kalli juna, ba musu suka gyaɗa masa kai. Mutumin me suna Ila ya yi murmushi, har wa yau ya na tuna irin alkairin mahaifiyarsu gareshi.
Domin akwai wata rana da ta taɓa zuwa shagonsa ta iskeshi ya yi tagumi, ta tambayarsa; lafiya? shi ne ya shaida mata da matarsa ce ta shaihu, ga shi ko na yanka ba shi da shi.
Har wa yau ya na iya hango murmushin da ta yi a lokacin, sannan ta lale maƙudan kuɗaɗe ta damƙa masa, tare da faɗin a sha hidumar bikin suna lafiya. Har da kukansa a lokacin, don Allah ya sani yanda yake a cikin buƙatar kuɗi. Da ma  jarin nasa ma bai taka kara ya karya ba.
*
“Na ji buƙatarka Malam Ila, sai dai a gaskiyar batu, ba mu da gurin zaman mutum biyu, yaro ɗaya kawai za mu iya karɓa, saboda yanzu haka ma gidan nan a cike yake da yara, yaro ɗayan ma za mu karɓeshi ne kawai dan ka dage”
Cewar shugar gidan marayun da Malam Ila ya kai su Zaid, zaune take a kan kujera, yayin da take kallon Malam Ila dake tsallaken kujerarta, Zaid da Aliyu kuma na tsaye daga bayansa.
A yau sun ci abincin da rabonsu da cin irinsa tun watanni biyar da suka wuce, wato ranar da Mommansu ta rasu, Malam Ila sai da ya tabbatar da sun ci sun ƙoshi, sannan ya kawo su nan wurin. Cike da fatan zuwansu wurin zai sauya rayuwarsu, amma maganar da matar ta yi ita ta murmushe wannan fatan nasu har garinsa.
“To yara kun dai ji... Yanzu mecece mafita ?” Cewar Malam Ila yana juyowa ya kallesu.
“Malam Ila mun gode da temakonka.... A gaskiya ba za mu iya rabuwa da juna ba, gwara kawai mu haƙura...”
Cewar Aliyu. Bai ko rufe bakinsa ba Zaid ya ɗora da:
“A'a Malam Ila, ba za ayi haka ba, ku ɗauki Aliyun kawai, ni na haƙura!”
*
Tsaye suke a harabar gidan marayun, yayin da Malam Ila ke kallonsu yana sharar ƙwalla, Aliyu kuma na kuka, Zaid na bashi baki.
“Hey! Don't cry, na ce maka zan riƙa zuwa ina dubaka...”
Shi dai Aliyu hankalinsa bai kwanta ba, dan ba ya jin zai iya zama a wurin nan. A kan idonsa Malam Ila da Zaid suka fice daga wurin.
Ashe ƙarshen ganawarsu kenan, ahse ba za su ƙara ganawa ba sai bayan wasu shekaru masu tarin yawa. Dan a cikin kwana uku kawai ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.
Malam Ila da Zaid na fita, Malam Ilan ya kalli Zaid.
“To Zaidu, tun da ka zaɓi ka koma gidanku ka ci gaba da zama, sai ka koma can ɗin, amma duk safiya, rana kuma dare, ka riƙa zuwa kana karɓar abinci a wurina”
“Na gode Malam Ila, Allah ya saka da alkairi”
“Kai ai ba komai, ku yaran kirki ne, 'ya'yan mace ta gari, Allah ya maka albarka”
*Present day...*
*Room No.45, National Hospital, Abuja.*
KULIYA POV.
Daga kan gadon marasa lafiya, Abubakar ne kwance, yayin da na'urar oxygen ke maƙale a kan fuskarsa, kasancewar ba ya iya numfashi me kyau.
Daga gefen gadon kuma, Kuliya ne tsaye, riƙe da hannunsa, hawaye ya ke sharewa akai-akai. Idan zai iya tunawa, rabonsa da kuka tun ranar da ya bar garin kano, ranar da ƙaddarar da ta sauya LABARINSU ta afku.
Amma a yau sai ga shi ya na kukan tsoron rasa amininsa, babban abokinsa, wanda idan ka ɗauke Anna, kaf duniya babu me iya jurar halinsa in ba shi ba, kuma ba ma haka ba, a yau ɗinan Aabubakar ya sadaukar da rayuwarsa don ceton tasa rayuwar.
Shi ɗin da bai aje kowa ba bayan Annan, shi kuma da yake da mata, yara har da ƙanwa da kuma 'yan uwa, ya iya sadaukar da rayuwarsa don kawai ya ceceshi.
Daga gefe kuma Symon da hannunsa ke  ɗaure da bandage ne, sakamakon raunin da ya samu a artabun da suka yi da 'yan ta'addar nan, sai Sharon wadda ke hawaye, sai kuma Kamis, Sani da Mubarak sun yi jigum-jigum cike da jimamin abun da ya samesu, don gaba ki ɗayansu abun ya shafa.
Ƙofar ɗakin ce ta buɗe, kawun Abubakar wato Alhaji Musa ya shigo, tun bayan da aka gamawa Abubakar ɗin tiyata yace su kira masa shi, su kansa ba su san dalilin hakan ba.
Jin sautin muryarsa ne yasa Abubakar buɗe ido a wahalce, sannan ya kalli kawunsu wanda gaba ɗayansa yake a ruɗe.
“Abubakar?! Me ya sameka haka?”
Da ƙyar Kamis ya iya masa bayanin abun da ya faru. Kawu Musa ya zauna a kusa da Abubakar ta ɓangaren dama, yayin da Kuliya ke riƙe da hannunsa ta ɓangaren hagu.
Da ƙyar Abubakar ya kai hannunsa kan abun oxygen ɗin yana ƙoƙarin cire shi daga kan hancinsa. Ganin hakan yasa Kuliya saurin kai hannunsa kan na Abubakar domin hanashi yin abun da yake ƙoƙarin yi. Cike da dauriya Abubakar ɗin ya girgiza masa kai.
Hakan yasa jiki a sanyaye Kuliyan ya janye hannunsa daga kan na Abubakar ɗin, har ya samu ya cire abun, sannan ya kalli Kawu Musa.
”Kawu... Za... ka... iya... Tuna... Wassiyar Ummuna... Ta ƙarshe ?”
A rarrabe maganara take fita, haka kuma a wahalce, cikin wani sauti mara amo.
Hawaye na yi wa Kamu musa zuba ya gyaɗa kansa, don bi da bi maganganun matar wan nasa ta dawo masa, a sanda take kwance a aibiti cikin halin ciwon naƙuda, rai a hannun Allah, kamar dai yanda ke faruwa ɗanta a yaunzu. Hawaye ya gangaro daga idon Abubakar, da ƙyar ya iya haɗiye wani abu sannan yace.
“Dukkan wasiyyunta na cika su, na reni Mishal da kaina... Na bata kyakkyawar rayuwa... Na... Na bata farin ciki... Abu ɗaya ne ya rage...”
Ya ƙarshe yana ritse idonsa, yayin da Kuliya ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cike da tausayawa. Kawu musa ya gayɗa kansa.
“Na mata alƙawarin in dai Allah ya yarda zan aurar da Mishal ga miji na gari, sannan kafin... kafin na bar duniya, zan barta a hannu na gari...”
Kawu musa ya girgiza kai cike da sallalami.
“Ka dena faɗin haka Abubakar, Insha-Allah za ka miƙe a kan ƙafafunka...”
Abubakar ya yi wani murmushi me ciwo.
“Ba na tunanin haka Kawu Musa... Ba... Ba na jin zan ta... Tashi, don haka nake so a ɗau rawa Mishal aure yanzu-yanzun nan!...”
Wani irin dokawa zuciyar Kuliya ta yi a cikin kunnuwansa. Ya ji wata ƙara a ƙirjinsa kamar ta fashewar glass, kamar glass ɗin windown da aka jefa da dutsi.
Wai me ma yake ji ne ?, kawai dan an ce za ayi wa wata yarinya aure ?, sai gabansa ya yi irin wannan dukan ?, wai shikan wata jaraba ce ke damunsa kan wannan yarinyar ?. Kafin ya gama shawara da zuciyarsa, Kawu Musa yace.
“Waye mijin ?”
Abubakar ya ƙara matse hannun Kuliya dake cikin nasa, sannan ya juyo ya kalli Kuliyan.
“Al... Aliyu Zaid... Bichi... Ku... Kuliya!, Babban abokina... Na san kaf duniya, babu wanda... Zai... Zai iya riƙe Mishal in... Ba shi ba... Don haka shi ne mijin nata!...”
Sakan ɗaya... Biyu... Uku.
RAJA POV.
A karo na uku ya ƙara jan akwatin dake hannun mutumin da suka zo karɓar kaya a wurinsa, kuma shi ma mutumin kamar ɗazu yaƙi ya saki akwatin.
Raja ya ɗaga kansa sama, sannan ya sauƙe.
“Ka cika gardama, ni kuma ba na san gardama, ka fahimta ?”
“Kuɗin da kuka bamu bai cika ba, don haka sai kun ciko za mu baku kaya”
Mutumin ya faɗi yana kallon idon Raja. A hankali Raja ya ɗaga kafaɗarsa ta dama, sannan ya gyaɗa kansa, tare da sakarwa mutumin akwatin.
“Na fahimta”
Ya faɗi yana neman bindigarsa a aljihun wandonsa na baya, kuma yana kamo bindigar, ya fiddo da ita, sannan ya saitata a kan mutumin, bai yi wata-wata ba, ya matsa kunamar. Ƙaran harbin bindigar ya karaɗe wurin.
Mutum ukun da suka zo tare da wanda aka harba suka yi ƙoƙarin guduwa, amma sai Rhoda da Zuzu dake tare da Raja suka buɗe musu wuta.
A nitse Raja ya sukunya saitin gawar mutumin dake yashe a ƙasa, ya kai hannunsa sannan ya finciki akwatin.
“Kun yi wa kanku, babu kuɗi, sannan babu kaya... Ko dan ga ta rai ma ai kun yi!”
Daga haka ya miƙe ya juya, Rhoda da Zuzu na take masa baya.
*T.O.C Douglas Crescent, Kaura District, Game Village, Abuja.*
_“Kamar yanda na maka bayani tun daga farko... Ina son na fito takarar sanata ne... Don haka ina buƙatar wasu 'yan kuɗaɗe masu yawa... Wanda zan yi amfani da su wurin yin campaign, kasan yanda mutanen Nigeria suke!, Kaji ne, sai da tsaba, idan ba su ganka da wani abun duniya ba, ba za su ko kalleka ba, bare su zaɓeka... Don haka na ce ka dawo kusa da ni.... Don ku min aikin da ya fi wanda kuke yimin shi a garin kano!...”_
Tar muryar Alhaji Bala ke fitowa daga cikin laptop ɗin dake gaban Raja, zaune yake a kan kujerar falo, Rhoda na zaune a gefensa. Waɗanan su ne ire-iren maganganun da suka yi da shi a ranar da suka tattauna da shi a ganawarsu ta farko. Ba tare da sanin shi Alhji Balan ba, Raja ya naɗi komai ta cikin wata na'urar ɗaukar hoto da magana, wadda ya saƙala a gaban rigarsa a waccan ranar.
Rhoda ta ɗaga hannunta, tare da bubbuga kafaɗarsa.
“Mun yi aiki me kyau Raja... Ina tunanin wannan hujjar ma kaɗai ta ishe mu... Ba ma buƙatar wata...”
Bisa ga mamakinta sai ta ga ya girgiza kansa, ya na jingina da jikin kujera.
“Basu isa ba Rhoda, muna buƙatar wasu”
Cike da mamaki take kallonsa, wata hujja za su buƙata bayan wannan ?, 'yar wannan maganar tasa da suka naɗa wadda ba ta wuce mintuna biyu ba, ita ce ta shigo da su wannan rayuwar da ba ta su ba. A ganinya wannan kaɗai ta isa ta hutar da su aikin bautar da suka sha tsawon shekaru huɗu.
“Rhoda, ba ni da ke kaɗai Alhaji Bala ya zalinta ba, ya zalinci mutu ne da dama... Kuma ba shi kaɗai ne yake zalincin ba, har da ɗansa Usman... Kin san yara nawa Usman ya yiwa fyaɗe ?”
Cike da ƙunar zuciya Rhoda ta girgiza masa kai, dan kuwa maganarsa ta tuna mata da bayanta, rayuwarta ta baya da mahaifiyarta. Dama abun da ya zamo sanadiyyar rabuwarsu da mahaifiyar tata.
“Kusan yara mata goma ya yi wa fyaɗe!...”
Idonta ta rintse tana kawar da kai. Raja ya zauna da kyau, sannan ya kamo hannaunta.
“Kada ki damu, za mu ga ƙarshen komai, za su kwashi kashinsu da hannayensu, sai an ƙwatawa kowa hakkinsa... Ba ni... Da ke kawai ba... Kowa Rhoda, i mean each and every body da suka taɓa zalinta”
A hankali wata ƙwalla ta sauƙo daga idon Rhoda, ta kwantar da kanta a kafaɗar Rajan, shi kuma ya shiga bubbuga bayanta, alamun rarrashi. A hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama cikin faɗin.
“Wannan hujjar ta yi kaɗan mu kai babban mutum irin Alhaji Bala ƙasa, muna buƙatar hujjojji masu tarin yawa, waɗan da ba wai ƙasa kawai za su kai shi ba, rugu-rugu za su yi da shi... Za mu kai masa wannan kayan, kuma kin san daga haka zai ƙara yarda da mu, mu kuma daga haka za mu ƙara ƙaimi wurin kai shi ƙasa!”
Rhoda ta share hawaye, tana yarda da maganar ɗan uwanta ɗaya tilo da ya rage mata a duniya, tun da har ya faɗi tasan zai cika, zai aikata duk abun da yace... A idanunsa kawai take hango irin faɗi tashin da ya riƙa yi a rayuwarsa don kawai ya ga ta samu gobe me kyau.
“Lokacin sallah ya yi, zan je masallaci”
Ya faɗi yana miƙewa, sannan ya dafa kanta, ya fice daga falon.
A balcony ya haɗu da su Zuzu. Suna zaune sai zuƙe-zuƙensu suke. Wutar da ya hango a jikin tabar Jagwado ce ta sa hayyacinsa ƙoƙarin rabuwa da gangar jikinsa.
Suma kuma sai a lokacin suka lura da shi, don haka suka yi saurin kashe wutar dukansu, dan sun san matsalarsa da wuta. Sun san halin da yake ciki, shi yasa ba sa shaye-shaye a kusa da shi. Saboda suna sonsa, suna sonsa Saboda yanda ya temaki rayuwar kowannensu. Sai da Raja ya dafe bango, sannan ya dawo hayyacinsa, da ƙyar ya kallesu.
“Lokacin sallah ya yi, ku tashi muje ku yi...”
“Ai kasan ba ma je gaban Ubangiji muna warin wuwu ba ko... Oga Raja ka bari sai mun ɗan eh yi wanka... Ka gane ko?...”
Cewar Alandi yana miƙewa. Yanda yake magana kawai ya tabbatarwa da Raja cewa sun bugu, ya girgiza kansa yana ɗaga kafaɗarasa, ya sauya komai a tare da su, wannan shaye-shayen ne ya kasa hanasu yi. Amma ya ƙudircewa ransa cewar, suna gama wannan aikin zai sada kowannensu da Rehab.
Agogo ya duba, ya ga lokacin tashin ɗaliban makarantar nan ya kusa, dan haka a gurguje ya ƙarasa masallacin estate ɗin.
Ya yi sallah, sannan ya fita ya tsaya a inda ya saba tsayawa don ganinta.
*Brickhall School, Kaura district, Abuja..*
MISHAL POV.
Tsaye take a tsakiyar abokan koyan faɗanta na Kungu fu. Sanye take cikin uniform 🥋 ɗin koyar da wasan kungu fu ɗin, ta ɗau matsayarta. Yayin da hannunta na dama ke dunƙule ta seta yarinyar da aka haɗasu faɗan, ɗayan ma a dunƙule yake amma a ƙasa.
Ɗaya yarinyar ce ta kawo mata duka, hakan yasa cikin salon faɗan na kungu fu ta ware hannunta na dama, ta kama hannun yarinyar, tare da banƙara shi, ta rataya hannun yarinyar a kafaɗartsa, sannan ta kaiwa yarinyar bugu a gefen ciki da hannunta na hagu.
Tini yafinyar ta shiga ɗaga hannunta, alamun saduda. Mishal ta saketa, hakan yasa hall ɗin koyon wasan nasu ya karaɗe da tafi, ita ce ta yi nasara kamar kullum. Cike da girmamawa ta miƙawa malamin kungu fu ɗin nasu gaisuwa, sannan ta ja baya.
Malamin nasu ya ɗan musu wasu jawabai a kan wasan, sannan aka sallami kowa. Ita ta koma jikin lokarta inda ta saba aje kayanta ta sauya kayan, sannan ta damƙawa Angelica riƙon jakarta, suka fito a tare.
Sai da ta je wurin Adawiyya suka yi sallama, sannan ta karɓi jakarta a wurin Angelica, tare da sallamarta, ta shige mota, Baba Ali ya tayar, suka fita daga makarantar.
Kamar jiya yau ma sai da ta ga Kuliya tsaye a jikin gate ɗin estate ɗin nan, to wai shi wannan me yake zuwa yi nan ?, ta tambaya kanta. Sai kuma ta share, tare da faɗawa kanta cewar; to wai ina ruwanta ma?.
Har suka kai gida tana shan hannu. Fita ta yi daga motar, a sanda suka iso gidan, ta shiga cikin gidan, Daala ta samu ita da Mama Ladi suna wasa a falo, kai tsaye sama ta wuce, ta shiga ɗakinta.
Abu na farko da ta fara yi shi ne, aje jakarta a kan work table ɗinta, sannan ta shiga wanka ta fito, ta sauya kaya zuwa wata yaluluwar shift dress, rigar bata sauƙa har ƙasa ba, bakinta kan singalinta. Ta nannaɗe gashin kanta cikin bun, tare da saƙala wani hair pin ɗinta me shape ɗin bow.
Da saurinta sauƙo zuwa ƙasa, sannan ta faɗa kitchen dan ta samawa kanta abun da za ta ci, duk da ta ga abinci a kitchen ɗin, amma alƙawari ne ta ɗaukawa kanta cewar ko yunwa za ta kasheta ba za ta ci abincin da Hajjara ta girka ba.
Jallof ɗin rice stick ta shiga yi, babu jimawa ta gama, sannan ta dawo ta zauna kusa da su Daala ta soma ci.
Loma ta uku kawai ta yi, wayar landline ɗin dake falon ta yi ringing, hakan ya sa ta aje bowl ɗin hannunta, ta miƙe tsaye ta na ɗaukan wayar.
“Hello!”
Ta faɗi a sanda ta kara wayar a kunneta, muryar kawu Musa ce ta doki dodon kunnuwanta, cikin kuka da shessheƙa.
“Hafsat ke ce ?”
Gabanta ya faɗi, amma sai ta dake tace.
“Eh Ammu(Kawu)... Ni ce”
“Ina Hajjara?...”
Sai ta kalli falon, kamar me neman Hajjaran a falon, sannan ta kalli danning area tana amsa ma sa da:
“Ba ta kusa”
“To ki sanar mata da ku yi maza-maza ku taho International Hospital, Abubakar ba lafiya!...”
Duk rashin hankalinta, da ƙarancin shekarunta a duniya ta san cewa jinya kawai ba za ta saka babban mutum kamar Ammunsu kuka ba, dole akwai wani abu dake faruwa da yayanta mara kyau, kk mutuwa ya yi ?!.
RABI'A POV.
Kamar yanda ta saba ganinsa  jingine jikin gate ɗin estate ɗin nan, yana kallonta da lumsassun idanuwansa. Yau ma haka ɗin ne.
A memakwan kullum da ta saba wucewa ba tare da ta masa magana ba, yau sai ta ɗago masa hannu, sannan ta yafito shi.
Sai da gaban Raja ya faɗi, ganin yanda ta kira shin, amma sai ya dake, ya fara takawa zuwa gabanta.
A lokacin da ita kuma ta hau hanya ta fara tafiya, kamar jiya sai ya fara binta a gefe.
“A can kake da zama?”
Bayan ɗan wani lokaci ya ji ta tambaya. Sai ya ɗaga ƙafaɗarsa ta dama sannan ya amsa mata da.
“Eh, a nan nake da zama”
“Wannan ɗayar ƙanwarka ce ?”
Ta kuma tambaya, hakan yasa ya kalleta kaɗan, wato jiya shi ya mata tambayoyi, yau kuma ita ce ke masa. Kafaɗarsa ya ɗaga cikin faɗin:
“Sunanta Rhoda, kuma ƙanwata ce”
Rabi ta gyaɗa kanta tana kallon hanya.
“Kai ma Cristian ne ?”
Sai da ya ɗan tsaya ya kalleta na 'yan wasu sakkani, sannan ya ci gaba da tafiyar.
“Ni musulmi ne”
“To miye ma'anar RAJA ?!”
Ta tambayi abin da ke mata yawo a ka tsawon lokacin da ya faɗa mata sunansa. Bisa ga mamakinta sai ta ji ya yi murmushi, hakan yasa ta juya ta kalleshi, murmushin kuwa yake, wanda ya ƙara bayyana kamarta da shi.
“Raja na nufin Fata, i mean wish, za kuma ki iya kiransa da hope, amma sunana na gaskiya Zaid ne!”
Zaid?!, Zaid!?, Zaid?!... Ta maimaita sunan kusan sau biyar a cikin ranta, to Zaid ɗin bai fi ba?, amma ya na wani kiran kansa da Raja.
Sai ta tsaya a sanda suka fito bakin titi. Kamar jiya yau ma sai da ya tsaida mata taxi, sannan yace kada a ɗau kowa sai ita.
Daga haka ya ɗaga mata hannu, ya koma layin da ya fito. Rabi ta yi murmushi tana kallon hanya. Hirarta da shi na sa ta nishaɗi sosai.
*No. 213, Naf Belly Estate, Asokoro, Abuja*
KULIYA POV.
A hankali ya sako ƙafarsa ta dama cikin falon gidan Anna, wadda take zaune a kan kujera tana tsige zogale. Kanta ta ɗaga ta kalleshi. Ba shiri ta miƙe tsaye, hakan yasa trayn zogalen dake kan cinyarta kifewa a ƙasa, zogalen ya zube.
Ba komai ya bata tsoro ba, sai ganin yanda idanuwan Kuliyan suka yi ja, fuskar tasa ma ta yi ja, bisa ga dukkan alamu kuka ma ya yi.
Suna haɗa ido da ita ya fashe da kuka, ba ƙaramin razana Anna ta yi ba, sanin halin ɗan da ta rena, Kuliya ba ya kuka a kan abu ƙarami, idan har ka ga ya yi kuka, to abun ba ƙarami ba ne, ita za ta iya cewa ma tun ranar da ta dawo da shi Abuja har wa yau bata taɓa ganin kukansa ba.
Da sauri ta ƙarsa kusa da shi, kuma tana zuwa kusa da shi ɗin ya rungumeta yana fashewa da kuka. Anna ta ja hannunsa ta zaunar a kan kujera bayan da ya saketa, da gudu ta shiga kitchen ɗinta, ta ɗauko ruwan sanyi ta ba shi. Sannan ta zauna a gefensa tana shafa kansa.
“Me ya sameka Aliyu?”
Kuliya ya aje gorar ruwan da ya shanye kusan rabinta, sannan ya share hawayensa. Yana kamo hannun Anna.
“Ba na faɗa miki cewar yau za mu fita kame ba ?”
Ya faɗi cikin wata murya mai rauni, wadda za ta iya cewa sam ba ta san ɗan nata na da ita ba.Da sauri ta gyaɗa masa kai tana shafa kansa.
“To a wurin ne... Ɗaya daga cikin 'yan ta'addan ya yi ƙoƙarin harbi na, shi... Shi ne Abubakar abokina, ya ture ni... Shi... Shi kuma harbin ya same shi!”
Annan ta gyaɗa kai, dan tasan Abubakar ɗin.
“To yanzu me ya samu Abubakar ɗin ?”
Ya haɗiye yawu yana share hawaye.
“Shi ne muka kai shi asibiti... Bayan an masa tiyata an cire alburushin... Yace a kira masa kawunsa... Ni da kai na... Na kira kawun nasa, na yi masa kwatance, ya zo ya samemu har asibitin...”
Ya kai hannu yana share hawaye, sannan ya ci gaba.
“To Kawun nasa na zuwa, yace yana so a ɗaurawa ƙanwarsa aure kafin ya rasu... Da kawun nasa ya tambayeshi waye mijin... Sai... Sai yace ni ne, cewa ya yi ni ne Anna!”
Ya ƙarashe a raunane. Anna da ta fara fahimtar inda zancen ya dosa, ta share masa hawaye ta na masa alamun ta na jinsa. Sai da ya ja hanci sannan ya ci gaba.
“Yanzu haka an ɗaura mana aure da ƙanwar tasa, Anna wani irin so Abubakar yake min?, da har zai iya kasada da rayuwarsa ya ceci tawa, sannan ya aura min ƙanwarsa da yake ganin ita kaɗai ce ta rage masa!”
“Kana da zuciya me kyau Aliyu, duk da kana da saurin fusata, ni nasan kana da kyawawan halayen da za'a so a tare da ɗan adam na gari... Yanzu ina Abubakar ɗin?”
Annan ta tambaya tana ƙara share masa hawaye, bisa ga mamakinta sai ta ga ya kwantar da kansa a kafaɗarta yana fashewa da kukan da ya fi na ɗazu, a hankali ya ɗaga kafaɗarsa ta dama.
“Anna Abubakar ya mutu!, Muntuna biyar da gama ɗaurin auren ya mutu!, Anna kuma bai mutu ba sai da ya kama hannuna, sannan yace na kula masa da ƙanwarsa, kada na bari ta wahala, Anna ina zan kai wannan nauyin?, Ina zan kai nauyin da ya ɗora min?!”
Anna ta rintse ido, a sanda take jin sauƙar hawayensa a kan jikinta, da ƙyar ta daure ta ci gaba da shafa bayansa.
“Allah zai temakeka Aliyu, shi kuma Abubakar Allah ya ji ƙansa, ya sa mutuwar ita ce hutu a gareshi, Allah ya baku zaman kafiya da matarka, ya kauda idomln maƙiya daga kanku!...”
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriters*LABARINSU*

#TaurariWriters

LABARINSUWhere stories live. Discover now