LABARINSU 7

22 1 0
                                    
*LABARINSU*
*©SALMA AHMAD ISAH*
*TAURARI WRITERS*
*07*
~~~
*Once  you taste a true love, ordinary will never do...*
***
*No. 213, Naf belly Estate, Asokoro, Abuja*
A fusace Anna ta shigo cikin gidan, ta ja ta tsaya tana kallon Siyama dake zaune a falo, ita ta ma manta da Siyaman, wadda ta zo gidan a daren jiya. A yau da safe su na karin kummalo wayar Kuliya ta sameta, hakan yasa ba shiri ta tafi asibitin.
Siyama 'ya ce a wurin ƙanwarta, wadda ta rasu, su biyu ne yaran ƙanwar tata, Siyaman da yayarta Karima. Siyama ta zauna a wurinta tsawon shekaru, kafin zamanta ya koma gidan yayarta Karima, amma duk da haka Siyaman na kawo mata ziyara akai-akai.
Siyama ta miƙe tsaye da sauri, hankali tashe ta na duban Anna, dan Allah ya sani, ta raya abubuwa mabanbanta a cikin ranta, kan abun da ya samu masoyinta, saboda tun da Anna tace mata Kuliya ne ya yi hatsari hankalinta ya tashi, har da kukanta a sanda Annan ta tafi.
“Anna ya jikin nasa ?... Fatan ba wani mummunan ciwo ya ji ba?”
Anna ta kafeta da ido tana kallonta, tun ba yau ba ta riga da sanin cewa Siyama na san Kuliya, amma ita a ganinta kamar hakan ba mai iyu ba ne, ba za ta iya tilasta Kuliya kan ya auri 'yar ƙanwarta ba, duk da tasan cewa idan tace ya yi hakan ko da ba ya so zai yi, amma ba ta san tilasta masa yin abun da baya so.
Bugu da ƙari ma sam Siyama ba ta dace da Kuliya ba, ba wai kyau ne ba ta da shi ba, ba wai ba ta da hali mai kyau ba ne, a'a, sai don sam halayenta ba za du dace da nasa ba, Kuliya ba irin Siyama yake buƙata a matsayin mata ba. Anna ta mata banza, ta cire hijabin jikinta, tare da rataya shi a jikin kujera, kafin ta zauna.
Ganin haka yasa hankalin Siyama ƙara tashi, amma sai ta shiga ƙoƙarin danne hakan, ta yi sauri ta faɗa ɗakinta na gidan, ta shiga banɗaki, ta kulle, tare da sakin kuka, ta jingina da jikin ƙofar bayin, zuciyarta na mata zugi.
Ta sha addu'ar Allah ya cire mata san Kuliya a ranta, don ta san cewa wannan son maso wani take, kuma da ma hausawa sun ce ƙoshin wahala ne. Kuma gashi tana wahalar, saboda Allah ne kaɗai yasan halin da take ciki.
*Brickhall school, Kaura District, Abuja*
RABI'A POV.
Bayan ta gama aikinta na safiyar yau, sai ta dawo senior section ta zauna, tana ta zuba ido ko za ta ga gilmawar ƙanwarta amma shiru. Har lokacin zuwa makatanar ya wuce, ɗalibai sun riga da sun fara darasa.
Ta miƙe za ta bar wurin, da zaton cewa wata ƙila yau ɗin ma ba za ta zo ba kamar jiya, sai kuma ta ja ta tsaya ganin Mishal ɗin na doso wurin, jakarta goye a bayanta, hannunta na dama riƙe da suit ɗinta, yayin da tsintsiyar hannunta na hagu ke liƙe da plaster.
Ganin plastern ne ya tadawa Rabi hankali, hakan ya sa ta dosheta da sauri. Tun daga nesa Mishal ɗin ma ta ganeta, don haka ta ƙara saurin tafiyarta tana sakar mata murmushi.
“Ƙanwata me ya samu hannunki ?”
Abun da Rabin ta fara tambaya kenan, bayan da ta isa gaban Mishal. Mishal ta ɗaga hannunta na hagu ta kalla, sannan tace.
“Ba wata damuwa fa Sisto, is not big deal, wani ɗan ƙaramin raunine na samu, and na je asibiti an yi treating ɗinsa, so forget about me, what happened to your own hand?”
Ta tambaya a sanda ta ga raunin hannun Rabin. Kuma maganar tata ta tunawa Rabin zagayen halin da take ciki. Fuskar nan wadda ke ɗauke da kammaninta ta tuna, amma sai ta share tace.
“Me too... Babu komai, just small injury”
Mishal ta ci gaba da kallonta tana mamakinta.
“Sis na tambayeki mana”
Rabi'a ta gyaɗa mata kai alamun tana saurarenta.
“Me yasa kike aiki a nan?”
Rabi ta ɗan juya kanta ta kalli inda suke, kamar me neman wani, sai kuma ta juyo ta kalli Mishal ɗin.
“Ƙanwata an fara darasi, ki je ki ɗauki karanatuki, na miki alƙawarin faɗa miki gobe idan Allah ya kaimu...”
Mishal ba ta ƙara cewa komai ba, sai kawai ta gyaɗa mata kai, kafin ta wuce. Rabi ta bi bayanta da kallo tana murmushi.
RAJA POV.
Tare da Rhoda suka fito daga estate ɗin da suka kama gida a ciki, magana suke kan yanda haɗuwarsu da Alhaji Bala za ta kasance a daren yau, don a ɗazu ya kira waya ya sanar da su cewara a yau ne yake so su haɗu.
A jikin wata mota dake fake a ƙofar gate ɗin estate ɗin suka tsaya. Ya na sauraron jawabin Rhoda, yayin da lumaassun idanuwasa ke kallon ɗaliban makaranarar tsallaken estate. BRICKHALL SCHOOL, shi ne sunan makarantar.
Lokacin tashi ya yi, dan ɗaliban tafiya gida suke, wasu a motoci ake ɗaukarsu, wasu kuma a school bus. Wata magana da Rhodabta faɗa ce ta jawo hankalinsa, hakan ya sa ya juyo ya kalleta.
Tunaninsa ya tsaya cak, sakamakon hoton da ya taho masa da fuskarta. Wannan fuskar da ke kwance a kan tasa fuskar, wannan fuskar da ke kwance a ta Aliyu, haka kuma ita ce kwance a ta Momma.
Da sauri ya juya ya kalli inda ya ganta, fitowa take daga cikin makarantar ita ma, sai dai ita ba ta sanye da uniform, yanayin shigarta ba zai bari ya yi tunanin cewa za ta iya zama ɗalibar makaranatar ba, kuma shekarunta ba za su bari a kirata da malama ba. To me take a nan ɗin?.
RABI'A POV.
Tana fitowa daga makarantar ta shiga dube-dube ko za ta ga ƙanwarta, dan tun da safiyar yau da suka haɗu ba su sake haɗuwa ba, gashi har an tashi. A maimakon ta ga Mishal ɗin da take nema, sai idanuwanta suka kallo mata wannan fuskar.
Tsaye a tsallaken makarantar, jingine jikin wata mota, sanye cikin T-shirt da jeans, gefensa kuma wannan matar ce da ta gansu tare a waccan ranar, kuma ita ma kayan jikinta irin nasa ne, ba don ta ga wannan ɗan uwan nasa na jikin hoton na miji ba ne, da za ta ce wannan macen ita ce 'yar biyun tasa. Ba wai dan suna kama ba, sai dan kayan da suke sakawa iri ɗaya. Last time ma da ta gansu kaya iri ɗaya ne a jikinsu, to gashi yau ma haka.
Wani abu da ta lura da shi shi ne, shi ma ɗin kallonta yake, kamar yanda ita ma take kallonsa. Turewa komai ta yi daga cikin kanta, ta soma tunkararsu, don ta samu ta bashi wallet ɗinsa da ya jefar jiya. Don da ma da ita ta taho, tana ta addu'ar Allah yasa suƙara haɗuwa.
Sai ta kasa magana a sanda ta ƙarasa inda suken, daga shi har wannan budurwar me kaya irin nasa sai kallonta suke, tsoro ya kamata, ta rasa abun cewa, sai ta shiga wasa da ƙarshen hijabinta ta ciki.
Raja ya ci gaba da kallonta, a sanda yake ƙara tabbatarwa da kansa wani abu, ko yaya aka yi, tabbas ya haɗa jini da wannan baiwar Allahn, abun ya wuce kama kawai, saboda ya lura da wata tawada a gefen fuskarta, wadda Mommansu ma tana da irinta.
Abun na ɗaure masa kai, shin dabma akwai sauran 'yan uwan Mommansu a duniya ?, amma me yasa basu neme su ba?, ko da yake ai Momman tace masa babanta ne ya koreta daga gidansa. Sai kawai ya ture komai, ya tsai da tunani ɗaya, ƙaddarar da ta haɗashi da wannan yarinyar, wata ƙila ita za ta sada shi da 'yan uwan Mommansu.
“Sannunki!”
Rhoda ta katse shirun da wurin ya ɗauka, kusan shuɗewar muntuna kenan, amma Raja da yarinyar babu wanda ya yi magana, shi ya sa ita ta ari bakinsu ta ci musu albasa.
Rabi'a ta ɗago ta kalleta, sannan bakinta na rawa ta ce.
“Sannu”
“Me kike nema ?”
Rhoda ta tambaya. Kuma kafin yarinyar ta amsa, Raja ya jiya ya kalli Rhodan, ko bai faɗa ba tasan me yake nufi, dan haka sai ta yi shiru, sannan ta juya ta koma cikin estate ɗin.
Ganin yanda yarinyar ta ke ta kame-kame ne yasa shi yi wa Rhodan alama da ta bar wurin, dan bisa ga dukkan alamu, ido ne ya mata yawa. Ya ɗaga kafaɗarsa ɗaya sannan wannan salihar murya tasa, me sawa mutum ya yarda da shi a tashin farko tace.
“Ya hannunki?”
Rabi ta kalli hannun sannan ta amsa da.
“Ya yi sauƙi”
“Ya ya sunanki?”
Sunanta ?, to me zai yi da sunanta ?, ko de shi ya santa, ita ce ba ta da masaniya game da shi ?, ta haɗiye wani abu sannan tace.
“RABI'A!...”
Wani abu me kama da Allura ya caki Raja a ƙahon zuciya, zuciyar tasa ta shiga rawa a ma'ajinta, wani abu me kama da rauni ya shiga bin jikinsa, an kuma. RABI'A?!, Cewa ta yi sunanta RABI'A!.
Jin ya yi shiru ya sa Rabi ta ɗago da hannunta wanda ke riƙe da wallet ɗin, ta miƙa masa.
“Ga shi, wallet ɗinka ce da ka cillar jiya”
Her voice was innocent, babu wani abu a cikinsa sai nutsuwa da kamun kai. A hankali kammanninta suka shiga rikiɗewa a idonsa, daga Rabi'a yarinya zuwa shekarun Mommansa a sanda ta rasu. Sunansu ɗaya, kammanninsu ɗaya. Sai yake jin kamar Mommance ta dawo. Amma ba wannan ba, shi sam bai lura da babu wallet ɗin tare da shi ba, saboda bai nemeta ba, shi yasa bai kula ba.
Kafaɗarsa ta dama ya ɗaga, kafin ya kai hannunsa ya karɓi wallet ɗin. Buɗewa ya yi ya kalli kayan ciki, babu abun da aka ɗauka, komai yana ciki yanda yake, kuma harda kuɗaɗensa ba ta taɓa ba.
“Aiki kike a nan?”
Ya tambaya, a sanda yake zaro kuɗi daga cikin wallet ɗin, Rabi ta ɗan kalleshi kaɗan, wai shi me ke damunsa ne?, yanayinsa kamar me jin bacci, haka ma muryarsa kamar wanda ya yi wani aiki ya gaji. Sai kuma ta yi saurin kauda idonta, ta kalli sauran ɗaliban dake tafiya ta ce.
“Eh...”
“Na fahimta”
Kuma ya fahimta ɗin, abun da tunaninsa ke gaya masa ne ya tabbata, aikatau take a wurin, bai sake cewa komai ba, ya miƙa mata duka kuɗin cikin wallet ɗin da ya fitar.
“Sunana Raja... Ki yi kuɗin  mota da wannan, sannan nagode da ajiyar da kika min, AMMATA”
Abubuwa huɗu ne suka haɗu a maganar tasa, sunansa, kuɗin da ya bata, godiyar da ya mata, sannan kuma sunan da ya kirata da shi; AMMATA!.
Ta kalli dumin kuɗin da yake bata, sannan ta kalli fuskarsa, wannan lumsassun idanuwan nasa ne a kanta. Dan haka sai ta girgiza masa kai.
“Ni ma na gode, ka bar shi kai...”
Maganar ta bi iska, sakamakon hannunta na dama da Rajan ya kamo, ya danƙa mata kuɗin...
*
Rabi'a ta shawo kwanar layinsu, dai-dai kwanar da masu kayan siyarwa kan taru. Tsayawa ta yi a kusa da wani mai kifi dake soyawa. A kullum idan ta zo wucewa ta wurin sai ta haɗiyi yawu, saboda, kwaɗayin kifin da ke ranta.
Ita fa da abata kaza gwamma an bata kifi. Gabshi kuma gidansu ba kifin ake ci sosai ba, sun fi cin kaza akan kifin. Hakan ya sa ba sosai take samun damar cin kifin ba.
Hannunta na hagu dake damƙe da kuɗaɗen da Raja ya bata ta ƙara damƙewa, hakan ya tuna mata da yanda suka kwashe da shi a ɗazu.
A ɗazun bayan da ya kamo hannunta, sai ya saka mata kuɗaɗen, sannan ya ninke hannunta kan kuɗin.
Yayin da ita kuma ta saki baki da hanci tana kallonsa, wani abu me kama da ruɗani na kai-komo a cikin kanta.
“Idan na faɗi abu ba'a mun musu... Kin fahimta ?”
Ta shiga gyaɗa masa kai, kuma ba ta bar gyaɗa kan nata ba sai da ya saki hannunta. Ita kuwa ta fahimta, ba ta jin akwai wani wanda zai kaita fahimtar yaren nasa. A kan idonta ya ɗaga mata hannu, sannan ya bar wurin, ya barta da raunanniyar zuciya.
Ta haɗiye wani abu a fili, sannan ta juya zuwa wurin me kifin. Magana ta masa kan ya bata na dubu ɗaya, sannan ta miƙa masa dubu ɗayan.
Me kifi ya saka mata soyyayar karfarsar a takarda, ya ninke ya danƙa mata. Ta kamo hanyar gida ranta fes.
Tana kaiwa gidan ta faɗa ɗakinsu, sai da ta faki idon kowa, ta saka kifin a jakarta. Sannan ta fito tai alwalar sallar la'asar.
Ta yi sallar, kafin ta fito ta shiga yin ayyukanta  da ta saba a gidan. Ta yi wanka ta saka kaya baya-baya. Ta dawo ɗaki ta zauna, tana ta dube-dube.
Anti saratu dake kwance a kan katifarta, ta lura da abinda take hakan ya sa tace.
“Rabi lafiya ?”
“Hmm, ina Mama ?”
Anti saratu ta yi murmushi.
“Ta tafi gantalinta, Fatima da Mahmud su na gidan kawu Abubakar. Umma kuma ina jin tana ɗakinta, faɗamin ta samu ne ?”
Ta tambaya ta na tashi zaune... Ran Rabi ƙal, ta tashi daga kan carpet ɗin da take, ta dawo bakin katifar ta zauna.
“Ina mutumin da na faɗa miki cewa ya temakeni jiya ?”
Anti Saratu ta gyaɗa kanta tana tuna zancen da suka yi jiya, sanda ta tambayeta a ina ta ji rauni.
“To ai na faɗa miki cewar ya cillar da wallet ɗinsa... Na ganshi ɗazu, kuma na bashi kayarsa, shi ne ya fitar kuɗin ciki gaba ɗaya ya bani, ya ce na yi kuɗin mota...”
Ta ƙarshe tana miƙa mata kuɗin. Bakin Anti Saratu buɗe ta karɓi kuɗin, ita da kanta ta shiga lissafawa.
“Rabi!... Dubu hamsin da uku ne fa?”
Anti Saratun ta faɗa ido waje, ita kanta Rabin sai da ta yi mamaki, duk da dama tasan kuɗin ba kaɗan ba ne.
“To da huɗu ne ma, tun da kin ga har kifin dubu na siyo”
Ta faɗi ta na miƙewa tsaye, tare sa nufar jakarta, ta fiddo da kifin dake duƙunƙune cikin leda, ta dawo ta zauna kusa da Anti Saratun ta miƙa mata.
“Rabi... Ko dai ya na ciki ne ?”
Ta tambaya a sigar zolaya, Rabi ta yi murmushi tana hango rashin tabbatuwar hakan, don ko da wasa ba ta hango hakkan ba, babu ma ta yanda za ayi hakan ta faru, dan akwai banbanci tsakaninta da shi, wani irin banbancin da take ganin tazararsa kamar, ta Mutum da lokacin mutuwarsa, dan mutum bai san lokacin da zai mutu ba. Haka ita ma ba ta san adadin tazarar dake tsakaninta da shi ba.
Kuma ita ta na ganin wata ƙila shi ma yana mata kallon wadda take kama da shi ne, ko kuma yarinyar dake buƙatar temako, ba ta san shi ba, ba ta san ya rayuwarsa take ba, amma tana da tabbaci kan shi ba sa'anta ba ne, akwai tazara me tarin yawa tsakaninta da shi.
Abun da ba ta sani ba shi ne, wannaan tazarar da take gani ta kusa zama kusa, wata iriyar kusa da za ta bata mugun mamaki. Amma kuma kafin faruwar kusan, sai wasu ƙaddarori sun gifta a tskani.
Ita ta buɗe musu ledar kifin,suka ci tare, tana tambayar Anti Saratun; kan yaya za su yi da kuɗin?.
“Abun da zai faru kawai zan aje miki su a wurina, idan kina buƙata sai kimin magana, ni kuma na baki...”
Rabi ta yi dariya tana kai wani kifin bakinta, yau tana cikin farin ciki, wanda ba za ta iya cewa ga dalilinsa ba.
RAJA POV.
Tsaye yake a gaban mutumin da ke amsa sunan ALHAJI BALA. Yayin da shi ma Alhaji Balan ke kallonsa. Fuskar Alhaji Balan na ɗauke da murmushin alfahari, dan sosai yake alfahari da Raja, though wannan shi ne karo na farko da suka fara haɗuwa, amma ayyukan da yake dominsa suna isowa kunnuwansa.
Yayin da shi Rajan yake kallonsa da wani gutun murmushi, salihar fuskarsa na wani irin haske da ba ka ce na miye ba, waɗanan lumsassun idanuwan nasa suna kallon Alhaji Bala ƙasa-ƙasa. Daga shi sai Rabbil izzati suka san abinda yake tsarawa a cikin kansa.
Suna tsaye ne a katafaren falon gidan Alhaji Balan, wanda ke ɗauke da maka-makan set ɗin kayan da kallo ɗaya za ka musu ka shaida tsadarsu.
Rajan na sanye cikin wani green khaki trouser, sai baƙar crew neck sweater, ƙafafunsa sanye cikin canvas baƙaƙe.
Alhj Bala ya ɗaga hannunsa na dama, tare da bubbuga kafaɗar Raja, yana ƙara faɗaɗa murmushin kan fuskarsa.
“Zauna mana ZAKI!”
ZAKI?!, Bai yi ƙarya ba, dan ya na amsa wannan sunan a wata duniya, wata duniya can da ban, wanda ta zama sanadiyyar kasancewarsa a wannan rayuwar.
A hankali ya juya ya kalli Rhoda dake tsaye a bayansa, sanye cikin irin kayan dake jikinsa, kalabar attachment ɗin dake kanta ta sauƙo har kan kafaɗunta.
Da ido ya mata alama da ta zauna, zaman ta yi a kan kujerar dake kusa da ita, sannan shi ma ya zauna a kusa da ita, dan kujerar me ɗaukar mutum biyu ce.
Alhaji Bala ya kalli yaransa uku dake zaune a falon, sannan y ce.
“Ku ba mu wuri, za mu gana...”
Cike da girmamawa suka tashi suka fita, ya rage daga shi sai Raja da Rhoda.
“Ita ma wannan yarinyar taka ya kamata a ce ta fita ko?, Dan maganar da za mu yi sirri ce!”
Alhaji Bala ya faɗi yana kallon Rhoda, kamar me neman amsa a wurin Rhodan, ya juya ya kalleta, ita ma shi take kallo, kafin ya juya ya kalli Alhaji Bala. Ya ɗaga kafaɗarasa ta dama, sannan wannan innocent voice ɗin nan nasa yace.
“Na fahimta, amma ba za ta iya fita ba, she is my other half, komai zan yi sai na sanar da iya, ba na taɓa yin wani abu ba tare da saninta ba... So you can say what you want at her present”
Alhaji Bala ya gyaɗa kansa, sannan ya gyara zaman malum-malum ɗin jikinsa, alamun dai maganar da za ta fito daga bakinsa babbace...
Raja da Rhoda suka miƙe a tare, bayan da Alhaji Baka ya kawo ƙarshen maganarsa, hannu Alhj Bala ya miƙawa Raja suka gaisa.
Daga haka suka yi sallama suka kama hanyar fita daga falon. Ƙofar falon ce ta buɗe, hakan yasa Raja da Rhoda tsayawa.
Wani mata shi ne ya shigo, yana binsu da kallon ɗai-ɗai, daga Rajan har Rhodan sun san waye, USMAN!, ɗan Alhaji Bala na fari. Babu wanda ya kula shi, har suka raɓa shi suka fice.
“Ya aka yi yanzu kuma ?”
Alhaji Bala ya tambaya yana kallon Usman ɗin, Usman ya sosa ƙeyarsa yana kallon babansa.
“Kuɗi nake buƙata”
“Dama na sani, ka je, zan saka maka a account...”
Ba ko godiya, haka ya gyaɗa kansa sannan ya juya ya bar falon.
Ya na saka ƙafarsa a wajen ɓangaren mahaifinsa ya fiddo da wayarsa daga aljihu, ya aika wa abokinsa Bash kira.
“Usee boyyyy!... So Sup? (To yaya ake ciki?)”
Muryar Bash ɗin ta faɗa ta cikin wayar. Usman ya saki murmushi, har fuskarsa na haskawa ta cikin hasken fitulin dake haskawa a harabar gidan nasu, kasancewar lokacin dare ne.
“An samu kuɗaɗen nan, a tanadar mana babes ɗin kawai, dan gobe akwai chilling”
“Oboy!, that's my gee, kar ka damu, ka kwantar da hankalinka kamar kana jirgin sama mai ya ƙare, akwai zafafan 'yan mata, masu tafiya  kyau na zuba, kai dai kawai sai na ganka goben”
Daga haka wayar ta katse, sannan ya jefa wayar aljihunsa. Wannan shi ne halinsa, ainahin halinsa da kowa ya sanshi da shi, shaye-shaye, neman mata da kuma bin abokan banza, shi ya sa yake ɓarin kuɗi, kuma mahaifinsa ba ya hanashi kuɗin, a duk sanda zai tambaya sai an bashi.
KULIYA POV.
A hankali yake saka kayansa cikin ƙaramar jakarsa ta goyon baya. Yau aka sallame shi daga asibiti, don haka ya shirya tsaf, don barin asibitin.
Ya riga ya tsara tarin abubuwan da zai gabatar a cikin kasan, ya riga ya tsara kaf, abubwan da zai gabatar bayan ya bar asibitin. Ba zai sararaba sai ya ga ƙarshen aikin da ke gabansa, shi matsalarsa ɗaya, fushin da Anna ke yi da shi, don tun bayan da ya kwanta jinyar kusan kwana huɗu kenan, amma ba ta zo ta duba shi ba.
Tun ranar farko da ta zo ta gama masa wankin babban bargo ba ta ƙara dawowa ba.
Sai kuma ita, itan da kamanin fuskarta suka manne a cikin tunaninsa, dai-dai da sakan ɗaya idanuwanta sun kasa barinsa ya huta, tunani barkatai yake a kanta. Ya kasa gane kan marsalar da ta samesa, yasan cewa shi bai taɓa samun kansa a cikin irin wannan halin ba.
Bai taɓa so ba, bai san ya yake ba, bai taɓa kusantar inda yake ba, bai taɓa budurwa ba ma, balle yace ya taɓa sanin kalar yanda so yake.
Amma a kallon farko da ya mata wani abu a kanta ya samu gu ya yi zaman darshan a zuciyarsa. Kuma sam ba ya jin zai bar hakan ta faru, zai yi duk yanda da zai yi wurin ganin hakan ba ta faru ba.
Haba!, Shi ne fa?, ALIYU ZAID BICHI?, Shi ne KULIYA manta sabo, wanda ba ya ɗaukar raini duk ƙanƙantarsa.
Abun da tai masa rannan ya dawo tunaninsu, yanda wutar masifa ke ci a idonta, a lokaci guda kuma sai ya ga mamaki ya maye wannan masifar, bai san mamakin me take ba, wata ƙila ganin girmansa ne ya sa ta shiga mamakin, ko kuma wani tunani ne ya haska a cikin kanta, amma dai koma menene shi ba zai bar abun da ke kai kawo a cikin kansa ya auku ba, don ya sani, hakan shi ne zai zame masa babban kuskure a rayuwarsa. Soyyaya tsakaninsa da ƙanwar abokinsa, no way!.
Abinda bai sani ba shi ne, ɗan adam ba shi da dama, ko iko na sauya ƙaddararsa zuwa yanda yake so, Allah shi ne wanda yake jujjuya ko wani irin lamari.
Sannan kuma wannan ƙaddarar dake shirin faruwa kwanaki kaɗan, ita ce za ta ƙaryata wannan zancen nasa, ta murmushe zancen nasa har garinsa.
#Labarinsu
#SalmaAhmadIsah
#TaurariWriter*LABARINSU*

#TaurariWriter

LABARINSUWhere stories live. Discover now