Phone Call

2.2K 280 19
                                    

Karasowa Aleeya tai kusa da su hawaye na zuba a idonta. Sai Sadam yai saurin mikewa tsaye ya nufi dinning ya aje kofi sannan ya juyo yana kallon yadda suka rumgume juna suna kuka, be san miyasa yake jin rashin kyautawa a kular da yake bawa Zinneera ba, musamman ma ganin da Aleeya tai musu a yanzu yasa shi.

‘Ba dan wani abun kai ba, sai dan tana bukatar wani kusa da ita, babu wanda zai zargi komai a ciki, kuma me ye abun zargi a ciki?’

Zuciyarsa nata kokarin wanke sa sai dai baya jin natsuwa da hakan, a dayab bangaren kuma yana jin kamar ba zai iya jurewa da hawayen da zinneera take zubarwa ba, yana jin digar ko wane hawaye daya fito daga idonta kamar saukar ruwan zafi a zuciyarsa. Sosai Zinneera ta rike Aleeya tana ta kuka kamar daman can an fada mata a kafadarta zata yi kukan. Sun dauki lokaci a haka sannan Aleeya ta shiga rarrashin Zinneera ba dan ita ma ta gama kukan ba, sai dan tausayin yar'uwata daya cika mata zuciya. Sai da suka zauna a saman sannan Mommy ta sauko tana kallonsu cike da tausayawa.

“Aleeya kin zo?”

Sai ta gyada mata kai domin kuka ya ci karfinta ba zata iya magana ba.

“Be kamata ki karawa yar'uwarki nauyin zuciya ba, karfafa mata kuiwa ya kamata kiyi ba ki saka ta kuka ba, ya kamata dukanku ku dauki komai a matsayin kaddara, ba kusan abunda Allah ya tsara zai faru nan gaba ba”

Ta gyada kai a karo na biyu tana share hawayenta ta kalli Zinneera cike da tausayawa.

“Umma ma ta damu fiye da ke”

“Bana son jin komai Aleeya bana son komai na tsani kowa ina son kebewa ni kadai a wani gurin da zan manta da komai na dan wani lokacin”

Zinneera ta fada cikin muryar kuka.

“Amman Zinneera...”

“Aleeya please... Kowaye ba zai so jin komai a yanzu ba, kin san wacece Zinneera ki dan daga mata kafa please”

Sadam ya saka baki daga can jikin dinning da yake tsaye. Kai ta gyada masa ta sake kallon yar'uwata.

“Bari na tafi gida Umma bata san na zo nan ba, bari na tafi gida”

Ta mike tsaye sai Zinneera ta riko hannunta suka fito tare. A harabar gidan Aleeya ta kalleta ta ce

“Ina son yar'uwata, ban taba jin son ki kamar yau ba”

Zinneera bata ce komai ba, sai hawaye take. Suna daf da kaiwa gate Sadam ya faka motarsa gabansu ya budewa Aleeya gidan gaba.

“Shigo na saukeki”

Ba musu Aleeya ta shiga, Zinneera ta tsaya a gurin tana kallonsu har suka fice, sannan ta juyo ta nufo gurin da ake faka motocin gidan ta zauna kasa jikin wata motar rumgume da hannayenta. Tunanin ne ya zame mata biyu, ta ina Sadiq zai iya samu miliyan ashiri cikin shekara daya? Idan be samo ba me zasu masa? Idan kuma ta fada masa hankalinsa zai tashi, idan kuma ta bar abun a rufe ta ya zai san abunda ya faru? Tana jin lokacin da Suraiya ta faka motar amman bata dago ba har ta rufe motar ta shiga ciki. Tayi minti talatin a ciki kamin ta fito fuskarta cike da tausayi ta rika zagayen motocin har ta hango wacce Zinneera take zaune taje ta lallabata ta taso da ita ta shiga da ita ciki.

Driving yake kana kallon yadda Aleeya ta kawar da fuskarta tana share hawaye.

“Tsakanin ke da Zinneera ban san wane yafi wani jin zafin lamarin nan, bana son ganin kukanku dukanku ku biyu, babu abunda kukan zai canja musu da zaki daina hawayen nan da kin taimaka min”

Ya fada da hakikan gaskiyarsa, domin kukanta yasa shi jin babu dadi. Juyowa tai ta kalleshi da jajayen idanuwanta, a kalla yau akwai wanda ya damu da zubar hawayenta, sai ta ji wata natsuwa da annshuwa sun ziyarci zuciyarta.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now