44

1.6K 351 227
                                    

Idonta cike da kwalla ta karaso gurin da Zinneera take tsaye, hannu ta kai ta rika ta sai kuma ta shafa fuska ta rika hannayenta she can't believe Zinneera ce yau a gidanta da kafafunta, da sauri ta rumgume ta ta fashe da kuka, kuka mai karfi har sai da tsayuwa ta nemi gagararta.

“Hajiya take it easy wannan kuka kamar ta mutu”

Suhail ya fada cike da damuwar yadda Hajiya Karima take zubar da kwalla. Wata kyakkyawar budurwa ce ta fito wacce ba zata wuce shekara goma sha hudu ba ko ma kasa da da haka tana nufo inda suke tana kallonsu.

“Brother me yake faruwa?”

Kafadunsa kawai ya daga mata. Sai ta shiga lekon Zinneera da Hajiya Karima dake rungume da ita.

“Hajiya lafiya...”

Sai a sannan Hajiya Karima ta tsagaita kukanta har ta saki Zinneera tana share hawayenta.

“Zinneera ce”

“Zinneera...?”

Yarinyar ta maimaita wace kike ba mu labari. Hajiya Karima ta gyada mata kai, sai yarinyar ta rumgume Zinneera da sauri tana murmushi.

“Wow Hajiyarmu tana bamu labarinki ta fada mana tana da wasu yaya bayan mu and wata rana zamu hadu and finally mun hadu I'm so happy”

Tun da ta fara maganar bata numfasa ba har sai da ta kai karshe.

“Okay Talkative ya isa haka, bari mu shiga ciki kunan sai ki fara bata labarin”

Suhail ya fada. Sai Hajiya Karima da yarinyar sukai murmushi, Hajiya Karima ta rika hannun Zinneera ta jata suka nufi cikin gidan, a duk tsayin da suka yi a waje Zinneera is bleeding mararta sai murdawa take. Suhail ne a bayansu shi ya lura da jinin dake zuba a duk takun da Zinneera tai.

“Zinneera tsaya...!”

Sai duk suka tsaya kuma suka juyo domin da karfi yai maganar, karasa yai kusa da su ya kai hannu zai daga zanen Zinneera.

“Ko kin ji ciwo da kika bugu da mota”

Kamin ya kai hannunsa Zinneera tai saurin yin baya.

“Aa ba a kafa ba ne”

“A ina ne?”

Ya sake tambaya yana mikewa tsaye. Sai tai shiru sai hawaye ke sauko mata. A take hankalin Hajiya Karima ya tashi.

“Buguwa da mota kuma? Garin ya?”

Ta tambaya tana duba jikinta. Suhail ya fada mata abunda ya faru.

“Suhail na sha fada ka daina gudu da mota a cikin gari amman kaki gashi nan na bugu har ta ji ciwo”

Hajiya Karima ta fada tana shirin fashewa da kuka.

“Hajiya Calm down, ban gudu na ke ba kawai dai ita dince ta tsallaka titi bata duba ba”

“Bari na dauko Hijab dina muje asibiti, Nooriya Help your sister ta shiga mota”

Ta karasa tana kallon matashiyar yarinyar mai kama da ita.

“Aa ba muguwar da nai da mota ba ne, ba sai munje asibiti ba”

Zinneera ta fada sai duk suka kalleta.

“To mienene?”

Sai kuma tai shiru kamar mai tunanin abunda zata fada.

“Hajiya shiga da ita ciki ni bari na je nai sallah magariba kar lokacin ta ya fita”

“Okay amman jinin fa?”

“She will be fine, a canja mata tufafi zan kaita asibiti idan na dawo”

Yana fadar hakan ya juya ya koma gurin motarsa.

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now