ZR 27

1.5K 261 33
                                    

Daddy be taba yarda da zancen Umma cewar Zinneera tana da aljanu ba sai yau, sam be yarda akan kanta tai wannan maganar ba, juye mata kwakwalawa su kai. Shine kawai abunda ransa ke raya masa. Karasa Mommy tai ta direwa Daddy tray dake hannunta ta nufo inda Zinneera take durkushe tana aikin kuka, ta rika tai baya baya da ita ta zaunar da ita saman cushion sannan ita ta zauna kusa da ita taja jikinta ta rumgume. Kuka sosai Zinneera tai kamar ranta zai fita kai ka rantse da Allah kace wani ne ya mutu, sai da tai mai isarta sannan tai shiru tana goge face dinta da hijabin uniform din.

“Sadam kike so?”

Mommy ta tambaya tana dago fuskarta irin yadda ake yi ma yara. Zinneera ta gyada kai tana wani shisshekar kuka.

“Amman miyasa? Sadiq din fa?”

“Bana son shi, ni Sadam na ke so?”

“Me Sadiq yai miki?”

“Be min komai ba, Mommy dan Allah ki taimaka min kisa Sadam ya so ni”

“Sadam yana so.... ”

Kamin Mommy ta karasa Daddy ya tari numfashinta.

“Ya isa haka Hajiya, wannan maganar tana bukatar zaunawa, yarinyarnan bata cikin hankalinta...”

“Na san abunda na ke yi Daddy, da kafafuna na taho nan, babu wanda ya san abunda na furta a yau sai kai sai Mommy, saboda na daukeku iyaye shiyasa na kawo kuka a inda za a share min hawayena, na san idan na fadawa Abbah ko Umma wannan maganar yanke ni zasu yi”

Ta karasa tana kara narkewa da kuka. Mommy ta rika ta

“Ya isa inda Sadam ne ki saka a ranki kamar kin aureshi ne.... ”

“Akan me zaki ce haka? Da Aleeya fa aka tsayar da magana, and ni ban yarda yarinyar nan tana cikin hayyacinta ba”

“Amman ai kasan Sadam yai maka biyayya ne kawai dan ba zai iya ci maka a a ba, amman har ga Allah Sadam Zinneera yake so ba Aleeya ba, ita kuma yanzu tana sonshi sai kuma kace zaka shiga da wani uzuri?”

“Ke tashi muje gurin Safiya”

Daddy ya fada yana mikewa tsaye, sai ita ta tashi tsaye ta rufa masa baya, Mommy ta bisu da kallo har suka fice. A front seat ta shiga Daddy yaja motar da kansa suka dauki hanyar gidansu Umma. Sallamarsa ce ta fito da Umma daga dakinta tana amsa masa da far'arta sai dai ganin Zinneera a bayansa tana hawaye yasa jikinta yin sanyi, yarinyar data kama hanyar islamiya me kuma ya hada ta da Daddy.

“Yaya lafiya?”

Ta tambaya tana kallonsa ta kalli Zinneera.

“To da sauki dai”

Daddy ya fada, sai tai saurin komawa ta dauko tabarma ta shimfida masa gindin ice, ya karasa ya zauna Zinneera ta zauna daga bayansa tana boyon kanta.

“Zinneera ce ta same ni yanzu a gidana ta fada min cewar Sadam take so”

“Sadam... ”

Umma ta daki kirji kamin ta kalli Zinneera.

“Sadam kuma? Ko dai Sadiq?”

“Sadam dai haka ta fada min”

“Sadam danka ko wani Sadam daban?”

“Sadam dai nawa, ko wani Sadam din kike nufi?”

Daddy ya karasa yana tambayar Zinneera sai ta girgiza kai alamar a'a.

“Zinneera lafiya kike kuwa? Nifa makaranta tace min zata tafi kuma lafiya kalau muka rabu da ita, sai kuma yanzu ku zo tare da wannan maganar?”

ZABIN RAIWhere stories live. Discover now