The Weeding and Accident

2K 304 80
                                    

SADIQ POV.

Zauna yake a falonsa rike da kofin ruwa shi be sha ba, kuma ba aje ba daman ba dan yana jin kishin ya dauko ruwan ba, domin rabonsa da wani abu mai nauyi a cikinsa yau kusan kwana uku kenan.
     Kofin ruwan ya aje ya tashi yana murmushi ya nufi dakinsa, yanayin zamantakewar da yai da Zinneera yake tunawa, the funniest moments and sad memories da suke fada ko samun rashin fahimtar juna. Bakin gadonsa ya zauna ya bude yar karamar loka ya dauko wani madaidacin littafi still yana murmushi har yanzu, sannan ya mika hannunsa ya dauki pen ya taso ya dawo falo a gurin da yake zaune dazu.
    He wrote her name on the top of the page, then he's a kasa, sannan ya sake bude wani page din ya fara rubuta farkon faduwarsa how he meet her, reasons din daya saka shi zuwa gurinta, wato da niyar yai kidnapped dinta sai gashi ya fada kaunarta. Murmushi yai ya shafa kansa kamin ya cigaba da rubuta komai daki daki ciki har da gaskiyar daya fada mata na abunda ya aikata da kuma dalilinta data fada masa na cewar saboda shi za tai, at the end ya rubuta ranar rabuwarsu, a lokacin ne idonsa ya cika da kwalla.

“I know kina so na Zinneera, amman ban san yadda akai Sadam ya yaudari zuciyarki ba”

Ya fada yana kai hannu ya dauki kofin ruwan dazun ya sake kurba kadan, ya juye sauran a jikinsa. Sai yai relaxing saman cushion din ya lumshe idonsa yana maida numfashi a hankali. Ya kai kike five minutes a haka kamin ya tashi tare da littafin ya koma dakin ya bude dorowar ya dauko wani madaidacin hoto mai kamar na passport ya rike a hannunsa yana kallon fuskarta.

“I love you so much....”

Sai da ya mannawa hoton kiss sannan ya saka shi a karshen gurin da yai rubutu ya maida littafin a cikin doruwar ya aje, sannan ya nufi akwatinsa ya bude ya dauko kananan kaya ya saka ya dauki makullin motarsa ya nufi badon baribari unguwar mahaifiyarsa.
   Be san inda zai je ba bayan can, daman idan aka bata masa rai wani gurin yana zuwa gurin Zinneera ko ya kira a waya sui fira duk kuwa da itama wani lokacin bacin ran take kara masa, and now be da Zinneera but he still have his mom on his side. Da sallama ya shiga gidan amman ba a masa masa ba kasancewar Mama na can cikin daki, kanensa kuma basa nan, kai tsaye dakin ya nufa sai ya sameta tana hada kayan wanki.

“Ah Sadiq”

“Mama ina kwana”

“Lfy kalau ya aikin”

“Alhamdulillah, wanki ne?”

“Eh wai hada na ke sai na ajewa wacce ta saba yi kamin ta zo”

Ya zauna bakin gadonta cikin damuwa ba tare da ya sake cewa komai ba. Sai itama ta zauna tana kallonsa.

“Kai ka ce ka janye maganar auren nan da kanka, amman kana saka damuwa a ranka ko dai wani abun ne?”

“Ba komai Mama kawai dai kin san sabo yadda yake, dole ne zan ji ba dadi kamin komai ya wuce”

“Karma ka damu kanka ni daman can yarinyar nan bata min sam vata da tarbiya ga rawar kai kamar mai aljanu, ga rashin natsuwa da rashin kunya, daman bata dace ta zama matarka ba, shiyasa na gode Allah daya saka kai da kanka ka gane rawar kanta ta janye neman auren nan, Mata gasu nan kamar pure water a kasuwa, ko a yan'uwa ai zaka samu wadanda suka fita ma”

Yai murmushi

“Mama mata kuma ba yanzu ba, sai na bincika sosai kamin na sake fadawa wata, kawai so na ke ni taya da addu'a Allah yai min nafita a lamarina, ya biya min bukatuna na alheri kuma ya tsare ni”

“Addu'a uwa ga danta ai dole ce, sai dai a kara, amman addu'a kam ai ina maka ita, Allah yai mafita”

“Amin ya Rabb

Ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudin da zasu kai 2k an dari biyu ya mika mata.

“Gashi ko zaki siya wani abu ni zan tafi office”

ZABIN RAIUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum