Chapter eight

7 2 0
                                    

🤍MATAR SARKI🤍

By Aysha Rano✨

Wattpad@aysharano22

*In dedication to Aunty Sis*
Ina kuke manyan mata???
Ina 'yan gayu da 'yan kwalisa wanda sukeda burin gyara jikinsu????
Ina matan da suke fama da infection????
Kina buqatar kayan sawa na mata masu kyau kuma cikin farashi mai sauqi???
  Toku matso kusa yau ga Aisha Rano tazo maku da mafita,
ZAHRA'S_COLLECTIONS
DEALER IN ALL KINDS OF;
1.APHRODISIACS,(KAYAN QARIN NI'IMA); ZUMA ,HAKIN DAKA, SABULUN NURUL HUBBI, HADIN SARAUNIYA, TSUMI,DAHUWAR KAZA, YAN SHILA,DAHUWAR ZABI, BADAKARIYAR GUMBA...
2.APHRODIASICS SUPPLEMENTS
3.HIPS ENHANCEMENT SUPPLEMENTS
4.BREAST ENHANCEMENT SUPPLEMENTS
5.BREAST FIRMING SUPPLEMENTS
6.SLIMMING SUPPLEMENTS
7.WEIGHT GAINING SUPPLEMENTS
8.ANTI_AGEING SUPPLEMENTS
9.IMMUNE BOOSTERS SUPPLEMENTS
10. FAT BURNER SUPPLEMENTS
11. WHITENING SUPPLEMENTS
12. ⁠INFECTION SET

DIFFERENT KINDS OF TEXTILE FABRICS, E.G SHADDA, WRAPPER, MATERIALS, LAFAYAS,ABAYA AND MORE
DIFFERENT KHUMRA, SHU'UMAR KHUMRA, MAR'ATUSSALIHA KHUMRA, NURUL HUBBI KHUMRA, ANGEL KUMAR, BODY OILS.
PHONE NUMBER:09033446324/09079860649.

08

Karfe uku da 'yan mintuna suka sauka Nnamdi Azikiwe international Airport Abuja...daga nan kuma suka sake hawa wani jirgin wanda bai saukesu ko inaba sai a Shangu International Airport...tun kafin su sauka dama anzo daukansu daga Palace don haka suna sauka kai tsaye suka nufi motocinda akazo daukan nasu dasu...Uncle Galadima motarshi daban tareda Umma don ba gida daya zasu sauka ba,Sultan da Tafeeda na mota daya sai su Ummi suma a mota daya tareda Fateeha da Muhammad...tun daga airport Sultan ya fara shan jinin jikinshi don yanda yaga fadawa suna kaman zasu mashi sujada abun har tsoro ya bashi kawai sai yakejin kmr something is about to happen to him amma ko kusa bai ta6a kawoma ranshi cewa wai shi zasu nada sabon sarki ba kawai dai yasan kila su bashi wani karamin sarauta snn suce bazai koma California ba ya zauna a Shangu amma kwata kwata tunaninshi bai taba bashi cewa shine ma zai zama sarki ba.
Har suka iso Palace bai iya yace komai ba shikam Tafeeda phone dinshi yaketa pressing suna chatting da Maleeka har motocinsu suka shigo MASARAUTAR SHANGU...tun daga first gate zaka fahimci lallai masarauta ce mai girman gaske wacce kuma takai ko kuma ince ta isa a kirata da masarauta sbd tsananin kyau da tsaruwarta...ginin masarautar gaba daya gini ne kusan na gargajiya amma a zamanance irin na gidan sarauta kuma a kallon farko zaka fahimci ba karamin dukiya Allah ya horema ma'abota cikinta ba...kana shigowa first gate zakaci karo da titi dodar wanda shine zai sadaka da can cikin masarautar...babu komai a wajen daga titin sai wani uban fili dake kewaye da titin sai kuma dakunan securities da masu gadi...idan ka shigo second gate kuma gidajen bayi ne a da wanda yanzu da ba'a bauta ake kiransu hadimai sai kuma sauran qananun ma'aika hadda su Primary da Secondary school a wajen da kuma islamiyya sbd yaransu...a bakin third gate kuma zaka sake cin karo da securities da kuma fadawa idan ka shiga ciki kuma a nan babbar Fadar sarki take wacce yake zama litinin,laraba da kuma juma'a...sauran ranakun kuma yana Fadar cikin gida sai kuma qaton parking space da yake cike taf da motocinsu...daga nan sai gate na hudu which happens to be the last gate wanda a nan ne Chambers dinsu suke...Chamber sarki yana daga farko kuma gininshi yafi kowanne kyau da tsaruwa da kuma girma don kana gani zakasan eh lallai wnn na sarki ne bama sai an fada maka ba...ta cikin Chamber Sarki yanada access to duk Chambers guda hudu na matanshi wanda zai iya shiga kai tsaye kuma a kowanne lokaci ba tareda yabi ta tsakar gidan ba haka suma matan duk wacce keda girki ta nan takebi ta shiga sbd ayi maintaining privacy din sarki...daga nan tafiya ce mai dan nisa kadan zuwa inda Chambers din su Mami suke...na Ummi ne a farko wanda ya kasance na mai babban daki sai na Mami a bayan nata sai kuma na sauran Yara da kuma na baqi wanda duk akwai tazara sosai a tsakaninsu.

Kasancewar Fadawa ko securities basuda hurumin shiga inda Chambers dinsu yake don ko Sarki iyakacinshi da Fadawa third gate basa taba shiga inda Chambers dinsu yake sai idan zai zauna Fadar cikin gida shima kuma ba kowa ke shiga ba tareda wani kwakwaran dalili ko babban uzuri ba amma hadimai mata suna shiga haka zalika jakadiyar sarki itama tana shiga don a ciki ma gidanta yake kafin a isa Chamber sarki...wnn dalilin yasa motocinsu na gama yin parking duk da suka fito su kadansu suka shiga fourth gate babu wani bafaden daya bisu sai kirarinsu kawai kakeji daga nan inda suke...Uncle Galadima dama bai karaso cikin Palace ba kai tsaye aka wuce dashi gidanshi don ba cikin Palace yakeda zama ba...Sultan da tunda ya shigo cikin Palace din yakebin ko ina da kallo yaga anyi gyare gyare sosai an kumayi renovating abubuwa da dama ba yanda ya tafi ya barsu ba...a hankali ya sauke wani numfashi cikin ranshi yana ayyana yanda zama zai kasance mashi a nan wanda ko ba'a fada ba yasan zaisha takura da tsidige tsidige wajen su Ummi za'a ce yayi kaza ko kuma ace bai kamata yayi kaza ba...wnn na daga cikin reasons da yasa baison zaman Shangu sbd yanda baida freedom din yin rayuwa yanda yakeso sai ace yayi ba daidai ba komai saida taka tsan tsan wai sbd gidan sarauta ne...kai tsaye Chamber dinshi dake bayan Chamber sarki suka nufa shida Tafeeda yayinda suma sauran kowa ya nufi Chamber dinshi...a bude suka samu kofa don haka suka shiga ko ina yana nan tsaf kmr ana rayuwa a ciki dama duk yayi tafiya ya dawo zaizo ya samu Chambershi tsaf an gyara mashi ko ina an tsaftace shi...Tafeeda ya wurga kanshi kan Three seater dake nan cikin Parlor yana sakin wani ajiyar zuciya ya lumshe ido yana cewa"Ohhh i missed this Palace"...kallonshi Sultan yayi yana dan ta6e bakinshi yace"what's there to miss in this Palace?...banda tsanani da takurawa mutane ba abunda suka iya"...bude idanu Tafeeda yayi yana cewa"bazaka gane bane i feel very safe and peaceful here sam ba hayaniya ko wani tashin hankali"...kallon you are not normal Sultan ke binshi dashi kafin yace"nan din ne ba hayaniya ko tashin hankali Habeeb kasan me ake nufi da gidan sarauta kuwa?"...girgiza kai Habeeb yayi yana cewa"kaga kome zaka fada ka fada you are entitled to your opinion amma nidai to me this is the most peaceful place i have ever been"...girgiza kai kawai Sultan yayi ya wuce bedroom da suitcase dinshi a hannu yace"then you are not normal"...Tafeeda yace"naji...kaima you are not normal"...shidai bai tanka mashi ba har ya shiga one of bedrooms dinshi...kayanshi ya fara ragewa bayan ya ajiye suitcase dinshi ya shiga bathroom ya watsa ruwa snn ya dauro alwala ya fito don suna hanya akayi sallah asr...a nan cikin dakin ya gabatar da sallahr ya kuma jima sosai nan inda yake yana addu'a kafin daga bisani ya mike ya dauko Alqur'ani snn ya sake komawa ya zauna ya bude suratul Baqarah zai fara karantawa kawai sai Zarah ta fado mashi a rai...ya zubawa Qur'anin ido yana tuna yanda tayi karatunta a waccan ranar cikin nutsuwa da kwarewa...ya tuna yanda sautin muryanta ke fita da kuma kira'arta da duk mutum yaji saiya rantse dama can balarabiya ce sbd yanda Arabic yayi blending sosai a bakinta...a hankali yayi flipping zuwa Suratul Nisa'i wanda bazai manta ba itace surar da aka fara janyo mata ta karanta...lumshe ido yayi yanaso ya tuna ayar data fara dashi nan take kuwa ya tuna  ta fara ne daga shafin *walmuhsanatu minannisa'i illa ma malakat aymanukum* wadda itace aya ta 24 cikin suratul Nisa'i...da sauri ya budo zuwa page din yakai hannu a hankali yana shafa page din and at the same time yanajin wani abu mai nauyi yana tasowa a cikin zuciyarshi...bai bawa abunda yakeji din muhinmanci ba kawai ya lumshe ido snn ya shiga karantawa daga farkon shafin and abunda ya sake bashi mamaki shine aya goma ciff ya karanta kmr yanda itama ta karanta ya tsaya a daidai aya ta 34 kmr yanda tayi...yana kai aya ya bude ido snn ya sake budo Suratul Anfal wadda itace sura ta biyu data karanta a ranar itama ya budo daidai ayar data fara karantawa har ya rufe ido zai fara daga inda ta fara din lokaci daya kuma ya tsaya cak kmr wanda aka sama full stop...bude idon yayi da sauri ya dauki Alqur'anin dake gabanshi ya duba yaga da gaske fa inda ta karanta yake kokarin karantawa kawai saiya rufe Qur'anin ya dafe forehead dinshi da hannu bibbiyu yace"Innalillahi wainna ilahiri rajiun"...ya karasa salatin yana girgiza kai sai kuma kmr zaisa kuka ya sake cewa"is this girl a witch or something?..i really don't understand?...why can't she just leave me alone?"...ya karasa mgn yana hargitsa gashin kanshi...lokaci mai tsaho ya dauka a haka yana mai jin haushin kanshi daya kasa dakatar da kanshi daga tunawa da ita bayan bai hada komai da ita ba kafin daga karshe ya sake daukan Qur'anin ya sake budo Suratul Baqarah snn ya fara karantawa daga farko...ya dade sosai nan zaune yana karatun bai tashi ba saida yaji an fara kiran sallahr magrib ya shiga bathroom yayi alwala snn ya fito don zuwa masjid sai a snn ya tunada Tafeeda daya tafi ya bari tun daxu a parlor...bai sameshi Parlon ba don haka ya shiga bedroom da yasan zai sameshi aiko yana ciki kwance akan gado yana bacci ko kayan jikinshi bai cire ba...karasawa ciki Abdul'ahad yayi ya daddage ya daka mashi duka a baya aiko ba shiri Tafeeda ya mike zaune da sauri yana kallon Sultan dake tsaye kanshi...tsaki Tafeeda ya saki yana sosa inda ya daka mashi dukan yace"gsky kai mugu ne wlh... haka ake tashin mutum a bacci?"...Sultan yace"it's time for prayer"...tsaki ya kara saki kafin ya sauka daga gadon ya shiga bathroom yayo alwala snn ya fito suka fita masjid tare.

🤍MATAR SARKI🤍Where stories live. Discover now