PART3

7 1 0
                                    

Ihu mutane suka saka take wasu suka fara arar na kare, su Sadiq ma ganin abunda ya faru da gudu suka ja Khairath suka fice daga gurin.


Sadiq ke tuka motar Asmee na zaune a kusa dashi yayin da Khairath da Amal ke baya, shiru motar ta dauka, ba mai cewa komai, daga bisani dai Asmee ta gaji da shirun tace, guy's ina muka nufa ne?

    Ina kuwa muka nufa Khaith ce ai zata fada ko?
   Cewar Amal tana duban Khairath din.

banza ta yi dasu duk da kuwa taji abunda ko waccen su ta fada.
  Sadiq ne ya yi karfin halin magana,
"Khaith are you ok?
   baijira amsawar ta ba yaci gaba da magana, Khaith seriously I'm scared what if something happens to him.... ya karasa fada muryarsa na rawa, Amal ta karbe da cewa Allah ya kiyaye dai kam because idan bai tashi ba wallahi all of us will be arrest.... be quite just quiet Amal, wallahi saidai ku, kuje prison but not me, Khaith bakyason zancen prison but mai yasa kika yi abunda kika yi yanzun kuma ma ai zancen Sadiq da Amal gaskiya ne Khaith idan bai tashi ba wallahi duk kama mu za'ayi babban damuwa na ma babansa ba karamun mutum bane, maganar ba lallai ya wuce a banza ba nasan dole a nemo mu....na shiga uku na, ta karasa fada cikin muryar kuka.

_Stop the car!_ khairath ta fada cikin bacin rai.

   dan waiwayo wa Sadiq ya yi kafun yace what's wrong muna tsakiyar hanya ne fa.  Eh na sani ai kawai ka tsaida mun mota ku fice I cannot just sit down and watching u saying stupid things......I can't, just stop the car.
babu yacce ya iya haka ya tsaya gefen titi fito khairath din ta yi ta je gefen da yake "fito ta fada kai tsaye galala dukan su suka yi suna jiran ganin mai take shirin yi. Fitowa ya yi, ta shiga ta zauna, sabon invitation kuke jira kafun kuyi joining nasa waje?

     dukansu kallon ta suka yi, sanin da suka yi ba wai zata canja ra'ayinta bane ko kuma ta maimaita musu abunda ta fada bane yasa suka yi saurin ficewa daga motar.

A guje taja motar ta bade su da kura.

gudu take tamkar  zata tashi sama, cikin mintuna sha biyar ta isa gidan, fa sauri security ya bude mata gate.

   gidansu ta nufa da hanzari security din gidan ma da sauri ya bude mata gate, ko parking mai kyau bata yi ba ta fito ta kashe motar ta shige gida, Doctor Muhammad da ke kallon shigowar ta, ta Balcony dinsa, ajiyar Numfashi ya sauke a ransa yana sake yi wa yarsa tilo addu'ar shiriya, farincikin sa daya duk tsiya zata dawo gida ta kwana komai dare, haka kuma bangaren karatun ta tana matukar maida hankali.

Fatansa kawai abunda ya yi saura na addini ta maida hankali ta nutsu tasan yanzun ita ba yarinya bace.

Tana shiga part din nata bedroom ta shige ta fada kan gado, tana faman sauke numfashi a hankali tunanin abunda ya faru ya shiga dawo mata, sai a lokacin taji wani tsoro ya shige ta maganganun su Sadiq yaci gaba da kai kawo a kunnuwanta what if bai tashi ba?

      Me kenan na aikata kisan kai...ohhh no.. no this can't be me mai ya hau kaina ne wai? Amma ai mari na ya yi, wata zuciyar ta fada mata hakan, eh he. Slapt me.. bakincikin marin ne yazo yadanne tsoron da ta fara ji. a hankali kuma ta sake jin wani sabon bacin ran hadi da haushin Afnan da tsanarsa suna sake kama ta.

      "tsaki kawai ta yi ta tashi ta hau cire kayan jikinta, wanka ta shiga tana fitowa ta saka sleeping drees din ta. Fadawa ta yi kan gado hadi da rungumar pillow ta fara baccinta.

*ASUBA TA GARI* ..., *_khaith_*

Alhaji Al_Dahir TURAKI a kishin gide kan lallausar carpet din da ke gefen sitting room din nasa, hannunsa rike da littafin Riyadhul_salihin. yana karantawa.
   Sallama aka yi hadi da shigowa, Ukasha ne Babban dan Alhaji Aminu, wanda shima jika ne ga TURAKin.

"Wa'alaikumussalam warahmatullah, turakin ya amsa cikin fara'a, Malam Ukasha, bismillah mana Zo ka zauna, dariya a fuskarsa yace Allah ya taimaki Turaki sannu da hutawa, yauwa malam Ukasha fatan dai komai lafiya?

Lafiya lau Alhamdulillah"ranka ya dade Turaki,dama CP ne yakeson ganin ka shine nazo neman izinin shigowa da shi.
Commissioner of Police kenan?
Eh ranka ya dade. to Allah yasa dai lafiya, amsawa Ukasha ya yi da to Amin ranka ya dade. maza kaje ka shigo da shi to.

"Sallama CP ya yi hadi da shigowa, tashi daga kishingiden Turaki ya yi yana amsa sallamar, bismillah CP zauna mana. Zama ya yi daga gefen Turakin a kasa, bayan ya zauna suka hau gaisuwa, kasancewar dama sunsan juna kasancewar daya daga cikin yayan Turaki abokinsa ne tare suka yi karatu.

    Ranka ya dade, ba komai yasa ka ganni ba, waton case ne aka kawo mana akan an kwada wa dan gidan commissioner of finance kwalba jiya da daddare.
      Subhanallah"ince ko da sauki? Turaki ya fada, daya bangaren na zuciyarsa na mamakin alakar wannan zancen da shi... bai gama mamaki ba CP yaci gaba da cewa... ahhh da na bibiyi maganar dan kama mai laifin sai ahh wato aka tabbatar mun da yarinyar ai yar nan gidan ce..! ya karasa fada shi kansa yana mai jin nauyin abunda ya fada.

Shiru Turaki ya yi na wasu dakiku ya yin da   zuciyarsa ta ke wani irin zafi, dan ko ba'a fada ba yasan wace da wannan aikin.

"baice komai ba hasalima wayarsa dake kusa da shi ya dauka dannawa ya shiga yi da alama wani yake kokarin kira, ganin hakan yasa CP bai ce komai ba face kallon Turakin da yake, Assalamu'alaikum, Alhaji Hamza ka fita ne? OK to maza kazo yanzun inason ganinka.

   Katse wayar turaki ya yi, kafun yace, Commissioner dan bani mintoci na kira Yayan uban nata yanzun zaizo dan Allah sai kuje ayi duk abunda ya dace.
Gyada kai CP ya yi.

Sallamar Alhaji Hamza ce ta sa dukan su suka dubi kofa, hadi da amsawa, gaisawa CP da Alhaji Hamza suka yi, kafun Alhaji Hamzan ya zauna yana mai gaida mahaifin nasa.

Amsawa turaki ya yi, kafun yace Alhaji Hamza dalilin da yasa na kira, yarku ce dai yau ma ta koma debo wani abun maganar saidai wannan karon ta tsallake iyakarta bazan cigaba da zuba mata ido tana kokarin bata mun sunan zuri'a ba. Lallai Khairath zata fuskanci hukunci na!

    Allah ya huci zuciyar Turaki" Khairath ai har yanzun yarinya ce, ayi mata afuwa wata rana sai labari, wannan abun kullum nake fadawa zuciyata shi yasa ma nake dauke kai ga dukkan wani aibun ta da Za'a kawo min.

     A sake hakuri dai ranka ya dade, in sha Allah watarana Sai labari.
numfashi ya sauke kafun yace shikenan, yanzun ka tashi kuje ku duba yaron da ta yiwa rauni, ka dauki Umar da Lawal kuje tare, kuma ku tabbatar kun bawa iyayen yaron hakuri yacce ya kamata.

In sha Allah. Alhaji Babba ya amsa, kafun ya tashi sallama CP ya yiwa Turaki, suna kokarin ficewa Turaki ya kira Alhaji Babba.
dubansa ya yi a tsanake yace kuna dawowa ka kira mun taron gaggawa, kuma ka tabbatar yarka ta halarci taron!

Amsawa ya yi da in sha Allah, suka fice.




'''Vote share and''' '''comment''' 😻

# *Turakifamily*
# _Khaith_
# ~zaitun~
# '''love trust'''
# _destiny and fate_
# *Romance and love*




_Xinnee Smart_

IDAN RANA TA FITO...Where stories live. Discover now