PART 5

12 1 0
                                    

*IDAN RANA TA FITO...*

_writer Xinnee Smart_

*5*
"Tana saka kafarta a babban parlourn gidan ta samu Dacta a zaune shi da Hajiya Uwani" wacce kallo daya zaka yi mata kasan cewa tana cike da damuwa.

Kokarin hawa sama take ba tare da tace musu komai ba, Dacta ya dakatar da ita, ta hanyar kiran sunan ta.
Khairath"
Ya ambaci sunanta, juyo wa ta yi ba tare da ta amsa kiran ba.
Alama ya yi mata da hannu na tazo ta zauna.

Wani yankewa gabanta ya yi, ya fadi to kiran meye kuma ni? a sanyaye ta zauna kan kujerar da take fuskantar sa.

"gani Dad" ta fada a sanyaye.

"Khairath" shi dinma ya ambaci sunanta cikin nutsuwa, kafun yaci gaba da magana.
"Shin kinji hukuncin da Mahaifin mu ya yanke akan ku?

Wannan karon kam tsoro da firgici ne suka shigeta jin abunda Dacta ya fada, akan su? ita da wa? to wani maganar yake nufi ko bayan wancan da aka gama?

jin ta yi shiru ba tare da ta amsa masa bane yasa yaci gaba da magana... "Allah ya sani nayi farinciki da hukuncin Mahaifina, abu daya ne ya tsaya mun a rai ta yacce kika tunzura shi ya yanke hukuncin cikin fushi.
bansan mai kika aikata ba, amma dai kamar ko yaushe a matsayina, na mahaifi, ina sake yi miki nasiha da kiji tsoron Allah ki kuma nutsu ki kyautata rayuwarki.

Domin kowa ya gyara zai gani haka kuma kowa ya bata zai gani, to mu gyaran yafi mu bata, kodan kyakyawan karshe, Khairath "yanzun ke ba yarinya bace kuma ki sani ina mai baki Umarnin da kiyi biyayya ga hukuncin mahaifina! lallai idan kikace zaki bijire to hakan zai sa ki fuskanci hukunci na.

" tunda ya fara magana Khairath ke binsa da idanuwa tamkar wacce aka dasa haka kuma jin ta da ganinta ta zamana tamkar dai mutum mutumi, ita dai harshenta kansa jinsa take tamkar an daddaure sa. ta ma gagara fadar komai.

"Dacta kam daga haka ya tashe ya haye saman sa, Uwani ma ganin ya tafi ta tashi ta shige daki da hanzari dan tana da abun yi a cewarta zama bai ganta ba.

****
" Pro wallahi ko matan duniya sun kare bazan zuba ido dana ya auri yarinya mara tarbiya kamar Khairath ba!
" soyayyar da Turaki yake wa yarinyar nan ta rufe masa idanuwa ta yacce baya ganin komai da yake mai muni akanta haka kuma ya yanke irin wannan hukunci akan nagartaccen mutum irin Ayan... sam babu adalci wallahi. " ta karasa maganar ta tana sakin gursheken kuka.

" Alhaji Babba dake zaune a gefen gadonsa da jarida a hannunsa haka kuma yake sauraren ta tunda ta soma zancen nata.
"jin taki saurarawa da kukan nata ne yasa ya cire farin glasses din sa.
Bilkisu"
ya kira sunanta ganin bata da niyyar amsawa ne yasa yaci gaba da cewa, yanzun ke saboda Allah ko kunyata bakiji ba kika sakani a gaba kina fadar wadannan bakaken kalaman marasa dadin ji akan yata yar dan uwana, kuma ya mafi soyuwa a gurin mahaifina da ni kaina ba.

Shin" bakiji rashin dacewar abunda kike fada bane, akan hukuncin da sirikin kuma Baffanki ya yanke bane? Mai yasa ku mata a koda yaushe kuke da gajeren tunani ne?
to ki saurara kiji mai zan fada miki wallahi tamkar yacce mahaifina ya yanke wannan hukuncin babu wanda ya isa ya tayar dashi, to haka nima muddin nine na haifi Ayan" ya yiwa umarnin Turaki biyayya ya gama.
Kuma ki tashi ki fice min a nan mutumiyar kawai, shirmammiya.

daga fadar hakan yaci gaba da duba jaridarsa ba tare da ya ko sake dubani inda take ba.
Itanma sanin da ta yi ba lallai ya sake sauraren mai zata fada ba, yasa ta fice daga dakin ranta na suya.

shigarta daki saiga wayar yar uwarta kuma aminiyarta Hajiya Uwani"
Hello"ta fada lokacin da ta dauka wayar, daga gefen Hajiya uwani, amsawa ta yi.. Hajiya Bilkisu"ince dai ko baki amince da wannan hadin gambizar ba?

IDAN RANA TA FITO...حيث تعيش القصص. اكتشف الآن