PART 8

9 1 0
                                    


Wayarta da ya ajiye a kusa da ita ta duba, dauka ta yi da niyar kiran Dad"dinta. kamshin da wayar ke yi ne yasa ta koma karata a hancin ta, wani lumshe idanuwa ta yi a hankali take taji ta shiga wani yanayi wanda tunda tazo duniya bata taba tsintar kanta a makamancin sa ba. sake yin relax ta yi a jikin pillow da take kwance hakan kuma ya sake bata damar sake lumshe idanuwan nata, saidai me? kyakyawar kirar sa ce ta shiga yi mata gizo hadi da kawalwalniya. tundaga tsayinsa kyaunsa da zatinsa, ba fari bane haka kuma ba baki bane.
yanayin kalarsa tafi kyau a kirasa da kalar black Americans. haka kuma yana da tsayi da ya dace da kirarsa ta mazan taka,tun daga idanuwansa hancin sa duka halita ce mai burgewa musamman idanuwan nasa masu jan hankali wanda idan akayi sa'a ya kafe mace dasu takan rasa sukuni kokuma inda zata jefa kanta idanuwan sa na da matukar jan hankalin yan mata, shi yasa da yawa abokan karatun sa ke ma sa lakabi da lady's mirror (madubin yan mata) "Ayan kyakyawa ne a sahun maza kyawawa, tundaga gashin kansa har zuwa farcen kafa, yana daga cikin wa dan da Allah ya yiwa baiwa ta kyau da haduwa ta ko wace fuska.
Khairath" sosai ta lula cikin duniyar karewa halittarsa kallo haka kuma muryarsa dake dauke da amo mai ratsa zuciya. ta matukar shagala da tunanin nasa,sake gyara kwanciya tazo yi, ai kuwa cikin rashin sani taja kafarta da ta zame dazun, aikuwa ta canyara ihu, take ta dawo hayyacinta, kuka ta shiga yi dan sosai kafar take mata zugi.
wayarta ta janyo da sauri, wannan karon ko bi ta kan kamshin ba ta yi ba, ta shiga kiran wayar Dad"yana ta ringing amma bai dauka ba, kuka ta koma sakawa Dad" ta fada tana sake sakin wani kukan.

"wani tunanin ne yazo mata ta koma kiran Papa" ringing daya biyu kuwa ya dauka,  yana dauka ta sakar masa kuka, cikin rarrashi ya shiga tambayarta mai ya same ta? tana kukan ta fada masa zamewa ta yi ta fito daga wanka.
rarrashinta ya yi, kafun yace baya nan yana makaranta, amma zai turo yanzun Doctor ya duba kafar, ya karasa fada yana rarrashinta jin har lokacin kukan take.
da kyar ta yi shiru ta kashe wayar.
kusan minti sha biyar da ajiye wayar ba wanda ya shigo gashi tana so ta tashi ta saka kaya amma kafar tace bata san zancen ba, tuni kuma kafar ta kumbura ta hau sosai.
itan kuwa banda hawaye ba abunda take yi, Sai uban gumi da take zubawa dan sosai kafar take mata radadi.
"turo kofa akayi hadi da sallama, tana jin kamshin da muryar ta gane waye, dan guntun tsaki ta saki tana ci gaba da wayenta ko kallonsa ba tayi ba, sai ma haushin Papa da taji wannan din dama ya kira, bacin ma duk shi yaja mata ta tsaya wani shinshinar banza turarensa shine ta fama kafar. bata gama tunani da jin haushin nasa ba taji saukar muryarsa a kunninta, Karbi"ya fada yana mika mata riga da mayafi, kallonsa ta yi cikin mamakin yaushe ya karaso dakin har ya bude closet dinta? wata zuciyar tace mata lokacin da kika lula duniyar tunani.
kawar da kanta ta yi duk kuwa da yacce ta kagu ta saka kayan, do I have to repeat myself?
a sanina dai ba kurma bace ke. turo baki gaba ta yi hadi da sakin kunkunin ai duk kai kaja mun, duk da baisan mai take cewa ba, amma sosai ta bashi dariya duk da fuskarsa sam bata nuna hakan ba.
bakinta da ta cuno ya kurawa ido yana cigaba da kallon yacce ta zuba wata irin fuskar shagwaba, a ransa yace Danm it! she is so cute, a sarari kuwa ajiye mata kayan ya yi kusa da ita.

"gashi ki saka yanzun Doctor zai shigo ya dubaki, daga haka ya juya zai fice, ni bazan saka ba, ai dai ma ni banyi niyar saka wannan kayan ba. kuma ma ni ina ruwan mutum dani... sarai yaji mai tace dan haka ma ya juyo a hankali ya dube ta," mai kike cewa ne? bai jira amsarta ba yaci gaba da cewa, I'm just trying to help but idan ba kyaso ni meye nawa ne?
If you like kiyi zamanki a haka you can even removed that towel for making your self more comfortable ehheen... And I'm sure that Doctor din da zai dubaki ma bashi da matsala da nudity dinki so be comfortable cause ba yau ya saba gani ba..pillow ta janyo ta shefa masa tana sakin siririn kuka, komai iskancin ta ba wanda ya taba dubanta ya jefeta da irin wannan kalaman. Sosai taji bacin rai I hate you kuma bazan saka din ba, and zan yi duk abunda nake so ba ruwan mutum dani. shi dai tuni ya fice daga dakin bai ko bi ta kanta ba.
Cikin kuka ta dauki rigar ta saka, a ranta tana jin idan Dad yazo ko kulasa baza ta yi ba, dan duk shi yaja mata da ya dauka waya ai da bata kira papa ba.
  tana gama saka rigar ta yafa mayafin rigar tana cigaba da tsiyayar ruwan hawaye.
"turo kofar akayi aka shigo," Ayan ne a gaba sai d
Doctor a bayan sa, rike da box da wata jakar a hannunsa. Sallama suka yi suna karasowa inda take.
Cikin murmushi doctor din ya dubeta, how are you? bata amsa masa ba sai turo baki da ta yi, cikin turanci "Ayan din ya  dubi doctor ya shiga cewa, doctor she can't hear you she's a Deaf her ears got problem since her childhood so Apparently she can't hear you. ta'ajibi ne ya kama Khairath na yacce tana ji tana gani ana zuba karya a kanta a gabanta kuma.
datse hakwaranta ta yi suka bada kara, Doctor da tunda aka fada masa bata ji ya shiga tausaya mata ganin yacce ta taune hakwaranta sukayi kara ya sake tabbatar masa da bata ji, sake dubanta ya yi cikin tausaya wa.
hannu ya daga mata alamun sannu ta yacce akewa kurame, bakinciki ne ya ishe ta wasu hawayen suka shiga sarabtu a kumatun ta, shi kam dariya ce ta kusa kubce masa na yacce yaga ta cika ta yi fam jira kawai take ta fashe.
kafar likitan ya shiga dubawa inda ya yi wa Ayan bayanin kafar ta ta buguwa ne ta yi, kashin ya dan goce wanda dole sai yaja mata an mikar dashi. "amsawa Ayan ya yi da, why not just start doctor.
kafar aka kama a hankali doctor din ya shiga jan kafar, tun Khairat na daurewa, tana kukan zuci har bata san lokacin da ta canyara ihu ba," Wayooo Dad" Dad....mami... Mamina.... Papa...ka taimake ni wassh... Dad.. Dad, haka ta dinga kwallarawa duk Wanda yazo bakinta kira tana kuka, doctor kam cikin mamaki ya cigaba da jan kafa, jin tana magana bacin an fada masa kurma ce.
"Ayan kam tuni idanuwansa sun rine sunyi jazir, sosai yake jin zafin wahalar da take sha ji yake tamkar ya karbe mata ciwon. sosai ya shiga damuwa ganin halin da take ciki, sam yanzun babu wannan tsiwar da shagwabar, asalin kuka take mai hade da azaba.

IDAN RANA TA FITO...Where stories live. Discover now