PART7

13 1 0
                                    

yana shiga Parlourn ya samu mahaifiyarsa Hajiya Bilki rike da waya a hannu, tana ganinsa ta Mike da sauri, Ayan ina ka tsaya tun dazun? ina wayarka inata kira?
Ina Abban naku? Shima wayarsa bata tafiya, ina magana ka zauna kana kallo na, Sai a lokacin ya yi murmushi Ummi to tunda na shigo Sai questions kike watsa mun, baki kuma bani damar amsa koda guda daya ba.
Sauke numfashi ta yi, kafun ta zauna a kusa dashi, hankali na ne ba'a kwance ba tunda nagan ka dauke da wannan yarinyar, ta fada cikin fushi tamkar Khairath din ce a gabanta
mamaki ne ya kama Ayan mai yasa yaga yanayin ta ya sauya? tunanin irin kiyayyar da take wa Khairath din tun can da ne ya dawo masa, ajiyar zuciya ya sauke kardai har yanzun Ummi bata son Khairath? ya yi wa kansa tambayar da bashi da amsarta.
domin kawar da tunanin ma yace, Ummi zan yi wanka na huta.

"OK Son amma kazo kaci abinci kafun ka kwanta dai," No ba yanzun ba Ummi naci abinci a jirgi so bana wani jin yunwa gaskiya.

  "OK fine yana nan dai yana jiranka nasan har yanzun shegen kin abincin nan yana nan.
Yana murmushi ya shige part dinsa.

*****yau kwana biyu kenan da dawowan Ayan, haka kuma kwanan Khairath biyu a Asibitin yau ma suka yi shirin sallamarta.

" Ayan ne ya yi sallama a kofar Parlourn Turaki" amsawa Dattijon ya yi cikin fara'a wacce ta kasa boyuwa, harsai da matarsa ta lura, gyara zaman glass dinsa ya yi yana cewa mutan turai.

"zama Ayan ya yi, kusa dashi yana cewa, our everlasting Grandpa, cikin dariya yace nine nan, duka suka saka dariya har fulani dake zaune kusa Turakin.

" ran Turaki ya dade barka da yamma, barkanmu dai Malam Muhammad. Fulani muna lafiya?lafiya lau Muhammadu, fatan kana lafiya kaima, ya kuma kasar nan?
Alhamdulillah.

" Ma sha Allah, Noman ya fada maka ina ki ranka ba? Eh ranka ya dade"cewar Ayan yana gyara zaman sa.

" yauwa dama dalilin kiran nasan cewar iyayenka basu fada maka ba. wato Muhammadu na yanke shawarar hada ka aure da yar uwarka Ummul_khairi!
Idanuwa Ayan ya zubawa Turaki tun lokacin da yafara magana, yana kaiwa a sunan Khairath Ayan yaji wata irin faduwar gaba da bai san daga ina tazo masa ba.
kallon Turaki ya yi na wani dan lokaci kafun ya sadda kansa kasa, haka kuma kirjinsa na wani irin bugawa na rashin dalili aure da Khairath? farinciki ya kamata ya yi ko sabanin haka...?maganar Turaki ce ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fada.
"Muhammadu ka yi shiru baka ce komai ba.
murmushin yake ya yi, kafun yace, Allah ya taimaki Turaki, naji abunda ka fada kuma in sha Allah ni mai yi muku biyayya ne, amma ranka ya dade ita Khairath din tana sona? dubansa Turaki ya yi cikin jin dadin abunda ya fada da farko, kafin yace kai kana sonta ne?
"shiru Ayan ya yi, dariyar manya Turaki ya yi, kafun yace Muhammadu tashi kaje ubangiji Allah ya muku Albarka.
Amin daga shi har Fulani suka amsa.
Fitowa ya yi daga parlourn Turakin, ya Fito zuwa harabar gida suka hadu da Noman" dubansa Noman din ya yi, dan yasan dalilin kiran da akaiwa Ayan din bazai wuce zancensa da Khairath ba.
Ayan"Noman ya kira sunansa, kaji wannan hadin gambizar da akai maka da Khairath ko?

"a mamakance Ayan ya dubesa," hukuncin iyayen namu kake kira da hadin gambiza? da sauri Noman ya shiga cewa, a a ba wai ina nuna rashin da'a bane akan hadin nasu face dai ina ganin rashin dacewar hadaka da Khairath din sam baku dace ba.... Enough Noman, bansan mai kake kokarin tabbatar wa ba amma ka sani dacewa ta da Khairath ko rashin dacewa ta da ita, abune wanda nine zan yi desiding so please mind your tongue. yana gama fadar hakan ya wuce abunsa.

"Aikuwa nima ina da alhakin yanke wa, dan duk duniya nine na dace da Khairath ba kai ba kuma muddin ina numfashi Khairath tawa ce ni ni kadai, dole Sai na mallake ta koma mai zai faru saidai ya faru na riga na shiryawa kudurina muddin raina.!
" Cewar Noman"da Ayan ya bari a tsaye cikin bacin rai.

" Ayan yazo fita ya hadu da Abbansa ya fito gidan su Khairath, kai tsaye ya nufe shi, gaishe shi ya yi, shima Abban amsawa ya yi cikin fara'a yace malam Muhammad"an sallamo Khairath fa daga asibitin ma muke yanzun. inaga ka shiga ka sake duba jikin nata, naga tun ranar da aka kaita baka koma zuwa ba. daga haka Alhaji Babban ya shige shi zuwa gidansa yana amsa waya. ba shi da wani zabin da ya wuce yin abunda Abban yace, dan haka kai tsaye ya nufi gidan su Khairath din.

"babu kowa a parlourn da ya shigo dan haka ya dan tsaya tamkar ya juya Sai ya dan tsaya, Aina daga cikin masu aikin gidan ce ta shigo parlor tana ganinsa ta zube tana gaishe shi, amsawa ya yi kafun yace ina ne gurin Khairath din, tace sama ne ranka ya dade. OK" ya fada hadi da nufar saman, yana zuwa yaga kofofi biyu ya ma rasa wacce zai bude, sauke tunaninsa ya yi akan wacce ke fuskantar sa, tura ta ya yi a hankali, cikin sa'a ta bude, zubawa kyakyawan parlour din ido ya yi, ko ba'a fada masa ba yasan wannan parlour din na Khairath ne,dan khairatyn sa tun ta kuruciya yasan ma'abociyar son pink colour ce, so definitely wannan parlour din nata ne.
shiga ya yi cikin parlourn hannuwansa zube a cikin aljihu, sallama ya yi cikin muryarsa ta mazan taka mai tada hankalin yan mata musamman marasa karfin zuciya, bugu da kari mayun mata.

Shiru ba'a amsa sallamar ba, a hankali yaci gaba da cewa anyone hello" shima dai shiru babu amsa, hakan yasa ya juya zai fice, tamkar a mafarki yaji kuka kasa kasa, yanajin muryar ya gane muryar ta ce, to me kuma ya sameta ya tambayi kansa.
tamkar yayi wucewar sa amma kuma sai yaji bazai iya ba, hakan yasa ya dan tsaya jikin kofar bed room din da yaji kukan na fitowa, hi are you ok? shiru bata amsa masa ba, babu ma alamun taji mai yake cewa, sai ma sheshekar kukan ta dake sake fitowa. juyawa ya yi zai fice ganin bata da alamun magana, Sai Jiyo ta ya yi tana sakin sabon kukan hadi da fadin, Dad"help me.. Dad... tana fada tana sakin kuka, ji ya yi bazai iya jure jin kukan nata ba, hakan yasa ya tura kofar dakin ya shiga.
da santala santalan fararen cinyoyinta da ke zube a kasa ya fara cin karo, wani irin bugawa kirjinsa ya yi. ita kuwa tana jin an bude kofa ta zata Dad ne ta wani rintse ido tana sakin sabon kuka, Dad I fall down Dad my leg.. ta fada cikin muryar kuka mai hade da shagwaba, daurewa ya yi ya matsa inda take ganin da gasken faduwa ta yi, duba da guntun towel din dake jikinta, ga alama wanka ta Fito santsi yajata ta zame, ummuhmm"ya yi gyaran muryar da ya tilasta mata bude idanuwan ta, cikin tsoro ta ware idanuwan da kyau.... Who.... Why...o....are....y..ou? ta fada firgicin ta na sake bayyana, shi kuwa cikin dake wa yace are you in need of help or you wanna asked me such questions?
wani mugun tamke fuska ta yi hadi da zabga masa harara, malam tambayarka nake waye kai, kawai zaka wani shigo wa mutane daki haka, sake dubanta ya yi fuskar sa shima a hade yace, do I look like someone da zaki saka gaba kina watsa wa tambayoyi? C'mon now, ya fada hadi da mika mata hannunsa.
    kawar da kanta ta yi tamkar bata ga hannun nasa ba, gajeren tsaki ta saki hadi da dafa kofar toilet din a hankali cikin jin zafin kafarta ta mike, ta daddafe towel din jikinta a hankali ta taka daya biyu za tayi taku na uku ta sake zame wa har ta sadakar da ta fadi ta jita a jikin mutum. sake tamke idanunwanta ta yi hadi da sauke ajiyar zuciya.
Kamshin turarensa da ta shaka da kyau da kyau ne yasa ta sake yin wani relax a hannunsa, sosai kamshin ya yi mata dadi.
  A hankali ya sureta koma damke shi ta yi, dan ta zata yadata zai yi, kallonta ya yi yaga yacce take a tsorata ce, baisan lokacin da ya saki murmushi ba.
a hankali  ya nufi gadonta da ita, a hankali ya sauke ta pillow ya saka ya jingina bayanta a kai.wayarta da yagani a kan mirror ya dauko ya ajiye a kusa da ita, da sauri ya juya ya fice daga dakin.

    Zubawa kofar da ya fita idanuwa ta yi, a hankali kuma zuciyarta na wani irin bugawa, saidai wannan bugawar ba na cuta bane da alama bugawa ne na samun canjin yanayi, yanayin da ko wani dan adam kan samu canje canje a cikin canji kuwa harda na rayuwa da abunda ta kumsa.

"a hankali ta sauke ajiyar zuciya, gashin ta da ya rufe idanunwanta ta gyarawa zama, tana sake bin kofar dai

#destiny
#love saga
#family triangle
#turaki
#Kayan
#zaitun khaith
#romance






*_Xinnee_smart*_ 💋

IDAN RANA TA FITO...Where stories live. Discover now