PART 9

23 2 1
                                    


"Dauke kai Khairat ta yi ganin irin kallon da kawayen nata suke watsa mata, Amal" ce ta kasa hakuri tace Babe kikace kurma ne.
Cikin tamke fuska tace uhmm. meye to, Asmee ta amsa da, sai kuma gashi yana waya, babe fada mana Gaskiya kodai soyayya kuke yi?
   "what! ta yi saurin fada, ke fa Asmee matsala ta dake bakya da tunani, kawai soyayya da wannan din? Mtsss bana son shirmen banza, shine fa wanda za'ai mana wannan auren hadin wai and daga dawowarsa yabi ya takura mun ya hana rayuwata sukuni.
daidai da muryarsa wannan idan naji rasa sukuni nake yi bare kuma uwa uba kallonsa wannan kam mutuwa nake so ba adadi... ta karasa fada tana lumshe idanuwa, wasu siraran hawaye na sauka a kumatun ta, wallahi kallonsa wannan idan inayi gajiyar dani yake yi, and kunsan wani abun haushin anytime we get closer to each other, my heartbeat faster, I don't know why the feeling is too strange, bansan ya zan yi ba komai yabi ya isheni wallahi. ta yi shiru tana sauke numfashi a hankali.
"Asmee da Amal kam mutuwar tsaye suka yi, dan su dai irin wannan a finafinan India suka saba gani, dukkan abunda ta fada a experience dinsu da soyayya, to duk abunda take ji so ne kauna ce mai zafi take shigarta, amma sam ta kasa gane hakan.
Cikin saukakkan harshe Amal tace Khait kina sonsa ne? da sauri ta bude idanuwanta daga lumshe su da ta yi.
ta zubawa Amal da ta yi tambayar, gyada kai Amal ta yi dan sake tabbatar mata da abunda ta ji to shi take nufi.
Cikin damuwa da sanyinta da ita kanta bata san tana dashi ba, tace Amal bansan meye so ba, bansan yaya ake jinsa ba, haka kuma bansan ta wace hanyar ake haduwa dashi ba kuma sartsen da ake cewa yana wa mutane bansan karan da na taka ko zan taka har ya sartse ni yaya yake ba... Amal abu daya na sani ganinsa na wahalar dani banason yanayin Amal" idan yana guri atmosphere din ma canja wa yake, Amal"i really don't like the moment Banaso nidai nafison da dina, nafi son Khait dina, wacce bata saba da komai ba Sai rayuwarta, banason bakon yanayin da yake shiga ta sam banaso hanani sukuni yake yi, what for? I want my old Khairat back banason wannan bakuwar dake ziyartata. So ko abunda ya dangance sa banason su.... Asmee ce ta karbe zancen nata, Babe a ganina a wannan karon ko bawa so dama kiyi wa zuciyarki jagora ki samu ki gana da soyayya lallai zaki moreta kuma ina ganin cewa bazaki yi asara ba kamar yacce da yawa ma'abota soyayya ke kuka da ita bana tunanin zaki kuka da ita, domin a ganina kinyi choosing right person... dan haka ma nasan soyayya ta tanadar miki aji mai tsarin karatu Wanda babu nadama a cikinsa..... hummmmmm taja numfashi kafun ta sauke idanuwanta a kan kawayen nata guda biyu, a hankali kuma ta shiga cewa, nifa kun kasa fahimta ta daga Soyayyar har wanda kuke hasashen ni bana bukatar su..... amma ai su suna bukatarki cewar Amal, dama kawai zaki basu, amma dai Babe kiyi tunani kuma wannan karon ki saurari zuciyarki ba tunaninki ba..... bari mu barki ki huta,cewar Asmee tana mikewa Amal ma tashi ta yi suka kama hanyar fita suna mata Allah ya kara lafiya, hadi da jaddada mata ta fa samu ta yi tunani.

"lallai kuwa tunanin ta durfafa......

*******A hankali Khairat na samun sauki, haka kuma kullum Ayan sake bar mata abun tunani da shauki yake tun Khairat bata son gazgata zuciyarta a dandamalin sonsa har ta fara aminta da dukkan mizanin da ta dorata na soyayyarsa wani irin so mai zafi tuni ya yiwa zuciyar kawanya.ta yacce bata ji bata gani, akan son har wani bugu zuciyarta ta sauya mai dauke da zafin so, a duk lokacin da ta gansa ko taji muryarsa takan ji tamkar ta tashi ta kankamesa ya zama ita ta kuma zama shi tanajin tamkar maida sa jikinta shine abunda zai saka radadin soyayyarta raguwa.

"a bangaren Ayan" kam dama ya riga da ya yi tasa damarar ta tunkarar duk wani abu da zai shiga tsakaninsa da Khairat dinsa. yana yi mata wani irin so mai zafi ne mara misaltuwa mara ambatuwa haka kuma mara kiyastuwa, baki bazai iya furta adadinsa ba haka kuma idanuwa baza su iya ganin adadinsa ba hannu bazai iya rubutawa ba, saidai asalin shaukin yaci gaba da gudana haka kuma da wanzuwa, shi dai yana kaunar Khairat da dukkan zuciyarsa, duk kuwa da irin saka shi a daki da Umminsa ke yi akan ya bijirewa auren, kullum son Khairat sake nunkuwa yake a zuciyarsa, yana jin cewa a yanzun kam koda Turakin da kansa ne ya yi kokarin hana aurensa da Khairat baya jin zai lamunce, a cewarsa he rather elope with her, da ta zama mallakin waninsa, dan haka ma  a yau ya yi shirin tunkararta da sirrin zuciyarsa.  duk da irin kwarin guiwar da zuciyarsa take bashi akan Khairat din, hakan bai hanasa jin fargabar rashin muradinsa ba, saboda sam bai san inda Khairat din ta fuskanta ba,, tana da matukar wahalar sanin inda ta dosa, attitude dinta a kansa kullum karuwa suke., shi yasa ma a wannan karon yayi damarar kawar da kila wa kala a tsakaninsu, komai ta fanjama fanjam.



*******Khairat ce a parlourn ta, tana kwance a kan tree seater,, tana  sanye cikin shigarta ta rai da rai riga da wando, rigar golden yellow ce mai dogon hannu haka Kuma wuyan rigar ya rufe duka saidai daga kafadar a tsatsage yake, wandon jikinta kuwa kalar baki ne wanda ya matukar kama ta.
kunnuwanta na saye cikin wani golden color earing, gashin nan ya sha gyara an tsaga shi kashi biyu ta saka band ta kakkama shi. Sosai ta yi kyau matuka banda kamshi babu abunda take, littafin mercy cane ne a hannunta mai suna, Love me the way you use to.sosai labarin jaruman cikin littafin ya dau hankalinta, musamman yacce jarumin yake kaunar jarumar, a ranta ta shiga kiyasta inama itace jarumar kuma Ayan"ya kasance jaruminta?

Wata zuciyar ta shiga ce mata, abun da kamar wuya, kedai kiyi ta haukar sonsa wata kila son ya zama ajalinki amma shi kam babu alamun soyayyarki a tattare dashi. wasu siraran hawaye ne suka gangaro mata, sosai ta lula cikin duniyar tunani.bata ankara ba taji an warce littafin dake hannunta, ko bata dago ta dube shi ba tasan waye saboda kamshinsa na rai da rai wanda ta gama sabawa dashi. tashi ta yi zaune a dabara kuma ta yi saurin goge hawayenta wanda ya dade da ganinsu.

Zama ya yi a kan kujerar dake fuskantar ta, littafin ya shiga karantawa, jin shiru bai ce komai bane yasa ta dago dan ganin ko ya fita ne bata sani ba, idanuwanta ne ya sauka a kansa yana karanta littafin kuma daidai inda take karantawa, wuf ta yi zata karbe littafin ya yi sama dashi aikuwa da sauri ta hau kujerar zata karba, ya tashi daga gurin yana sake daga littafin, cikin muryarta ta shagwaba ta shiga cewa, ni ni gaskiya kabani littafi na...dira kafa ta shiga yi tana kukanta na shagwaba AY"ni ka bani littafina zan gaya ka da Dad" to...... yacce ta kira Ay din Sai da tsigar jikinsa ya daga, haka kuma kallonta a hakan cikin irin wannan yanayi ji yake tamkar yakai mata runguma,shi kadai yasan kalar azabar da yake ji a yanzun, sosai sonta ke hudasa ta ko wani sassa babu sassauci. sosai ya shagala da kallonta hadi da fadawa kogin tunani. har baisan lokacin da tazo ta kan Kujera ta warci littafin ba, Sai dariyarta yaji, dubansa yakai kanta dan ganin mai take wa dariyar Aikuwa idanuwansa ne suka kai kan, littafin, sai a lokacin ya gane shi take wa dariya, dariya take sosai tana jin dadin ta karba littafin hadi da yi masa gwalo sai tsalle take yi a kan kujera, shi dinma murmushi ya yi, yana sosa kansa, Allah yasani yana son khairat koma nata burgesa yake haka ya shagala da kallonta tana ta dariyarta, a hankali ta lura da irin kallon da yake watsa mata, take ta dawo nutsuwarta itama, a hankali kuma bugun zuciyarta ya shiga sauyawa kokarin sauka take daga kan kujerar ta yi taga taga zata fado, cikin azama ya tare ta. wata irin ajiyar zuciya ta sauke da taji ta a jikinsa, a hankali ya sauke ta kasa, kokarin barin parlourn ta ke, cikin husky voice dinsa yace Can we talk?
  "a hankali ta dakata hadi da juyowa ta dube shi, kafun ta koma kujerarta ta zauna, shi dinma zama ya yi.
A karon farko taji kunyar zama haka a gaban wani namiji, ta kasa sakewa sam sosai taji kunyar rashin mayafi a jikinta, dan haka ma, a sanyaye tace masa please two minutes, gyada mata kai ya yi ba tare da yace komai ba, itanma ba tare da jiran amsar sa ba ta shige bedroom dinta. tana shiga ta dafe mirror din dakin tana sauke ajiyar zuciya, kallon kanta ta shiga yi a mirror din, ta ga yacce zuciyarta ke hawa da sauka, a hankali ta dafa saitin zuciyar. ta shiga magana da kanta Calm down Khairat calm down..... ba fa maye bane ba cinyeki zai yi ba, but shi dinne his Eyes are so attractive ohh my God"ta fada a marairaice he's so Handsome and dashing. ta fada tana lumshe idanuwanta, firgigit kuma ta bude dan dukan kanta ta yi, he's waiting for you.... C'mon.
Juyawa ta yi ta dauki nayafinta, ta lulluba a kai  kafun ta dawo parlourn.

"zama ta yi a kujerar da ta tashi, idanuwansa ya zuba mata, a ransa kuma sosai yaji dadin yacce taga dacewar ta rufe kan nata, duk da mayafin bashi da wani girma, amma yasan decision din mai girma ne a gurin khairat hakan yasa ya sake samun kwarin guiwar maidata tasa, haka kuma ya daidaita abubuwa da yawa daga rayuwarta sosai ya samu kwarin guiwar hakan.

"cikin nutsuwarsa ta koda yaushe ya dubeta, a hankali kuma ya soma cewa, I know ba abu mai sauki bane hukuncin da Iyayenmu suka yanke a kanki, haka kuma nasan cewa ba lallai bane hakan ya yi miki ko kuma ya kwanta a ranki ba, amma ina da mafitar hakan a tunani na..... Sosai kirjinta ya buga mai yake nufi da ba abu mai sauke bane hukuncin da aka yanke a kanta shin bashi da ra'ayinta ne shi din? so yake yace ya fasa zai nema mafitar hana auren aikuwa idan kudirinsa kenan baza ta bari ya cika shi ba, lallai dole ta dakatar dashi tun kafun ya furta bazai aureta ba dan idan shi baya sonta ita ai tana sonsa.... cigaba da magana ya yi, dan haka ma na yanke hukuncin zan yi duk yacce zan yi dan nasa mana mafita..... Khairat zan so kiyi wa magana ta kyakyawar fahimta a gaskiya Khairat.... Bana sonki!

*Toh fa😳*


#love saga
#family
#Ayan Khairat (Kayan) 🤭
#destined by fate




_Xinnee Smart_ 💋

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jan 21 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

IDAN RANA TA FITO...Where stories live. Discover now