PART 6

11 1 0
                                    


"Yau sati daya kenan da yin zancen auren Khairath da Ayan,kuma a yau ne Ayan zai dawo daga birnin London, amma Khairath.. har yanzun ganin abun take tamkar a mafarki, duk da kuwa sosai zuciyarta take cikin firgici hakan bai hanata jin cewar auren ba abu bane da zai faru da rayuwarta ba.

Kwance take a kan sofa, tana faman danne danne a wayarta wanda Instagram ne take kallo, saidai rabin hankalinta baya kan abunda take kallon, hasalima gabanta da ke yawaita faduwa ne yasa ta koma shiga damuwa ita dai a iya saninta tunda take a duniya bata taba shiga damuwa kalar wannan ba.

  Bude kofar aka yi hadi da sallama aka shigo, daga idanuwanta ta yi, ta dubi kofar "Dad ta fada a ranta cikin mamaki, dan rabon sa da ya shigo dakinta ta manta dama abunda yake kawo sa dakinta yawanci idan bata da lafiya, cike da mamaki ta shiga kallon sa, har ya iso kusa da ita ya zauna ganin ya zauna ne ya sa ta mike zaune. Good afternoon Dad"
Afternoon Dad's Princess"  ya fada yana murmushi.
itanma yake ta yi dan baza a kira abunda ta yi da murmushi ba.
"hannunta ya rike duka biyu yana karewa yanayin ta kallo, a ransa yanajin tausayin yarsa da halin maraicin da take ciki.

UMMUL_KHAIRI" ya kira cikakken sunanta, a sanyaye, itanma cikin mamakin yacce ya kira sunan nata, ta dube shi.
bai jira amsawar ta ba, yaci gaba da cewa...a yau Muhammad zai dawo kasar nan, ina sake baki umarnin kiyi biyayya ga umarnin mahaifina.,kuma umarnin na.
nunkuwa faduwar gabanta ya shiga yi, ta dubi mahaifin nata, idanuwanta na cikowa da hawaye, Dad" a kaf Family din Turaki babu wacce ta dace da AY ne sai ni? Dad dudu du nawa nake? If grandpa yana da tsufan da yakasa tuna shekaru na ya kuma dubi girman future dina da matsayin career ta da zanyi building please Dad why can't you see it?
ta karasa fada tana sakin wani irin kuka yayinda zuciyarta ke cigaba da gudu mai hade da bugawa da karfi.
Murmushi Dacta ya yi, Khairath "ke yarinya ce, har yanzun kallonki nake lokacin ma da kika shigo duniyar ba ma a yanzun da kike ba.
Khairath, duk uba na gari bazai cutatar da yarsa ba, Ayan da kike ganin bai dace da ke ba kuma ba lokacin aurenki bane, Khairath shine zabina kuma zabin mahaifina. Khairath ki mana biyayya lallai bazaki tabe ba..and that's my Promise! ya karasa fada yana sake damke hannayen ta.
girgiza kanta ta shiga yi hadi da kwace hannuwan ta, zama tayi a kasa gefen gado hadi da ta kurewa ta hada kanta da guiwa, no Dad.. no, Dad u're being unfair to me, how Dad how? ta yaya zan amince da wannan kudirin naku?
Dad kana wasa da rayuwata ne saboda BANI DA UWA! ta karasa fada tana sakin wani irin gursheken kuka mai taba zuciya.
Dacta jin zancen nata ya yi tamkar saukar aradu, mai ke shirin faruwa dashi ne yasan yarsa tana da kafiya da kuma karfin zuciya, amma mi yasa akan wannan ta kasa kwantar da hankalinta ta fuskanci gata yake mata, yau shi Khairath ke raina riko fa gatan da ya mata? har take danganta hukuncin sa da rashin uwa ko rashin gata?
"kasa ce mata komai ya yi, a sanyaye ya tashi yana jin wani irin jiri jiri na dibarsa, ashe wannan ranar zata zo da Khairath zata ji kanta a marainiya wacce bata da uwa bayan duk gata da kokarin kaucewa hakan da ya yi, kar dai alkawarinsa ga Noor" ne ya rushe? wani sarawa kansa ya koma yi take ya fada kofar dakin..a hankali ya yi kokarin ficewa daga dakin saidai wani irin numfashi da Khairath ke saukewa  ne yasa ba shiri ya dawo hayyacinsa cikin azama Kuma ya dawo gareta.

   "Khairath wani irin numfashi take mai ban tsoro, cikin sarkafewar harshe take kiran Mami"... Mami..." Mami...na...take kuma ta shiga kakkafewa, numfashin na wani irin sarkafewa.

Cikin tsoro da firgici Dacta ya yi kan yarsa, yana kiran sunanta, saidai ganin halin da take ciki take shima jikinsa ya shiga wata irin rawa, cikin karfin hali ya fice waje, yana neman taimako.

   "cikin rashin sa'a bai samu kowa a parlor ba hakan yasa ya nufi asalin tsakar gidan, yana kiran sunan duk wanda yazo masa a cikin yan uwansa. cikin sa'a yana fitowa daidai shigowar motoci biyar a jere, ya gane motocin gidan ne dan haka cikin azama ya isa garesu, su din ma ganin halin da yake ciki babu shiri suka yi saurin cin burki.
Alhaji Babba"ne da wasu daga cikin yan gidan, bai tsaya tambayar daga ina suke ba ya shiga jan hannun Alhaji Babba yana kiran sunan Khairath din.

IDAN RANA TA FITO...Where stories live. Discover now