17

3.5K 47 0
                                    

BAN FARGA BA ✺✺_* ᴸᴼᵛᴱ ᴬᴺᴰ ᴿᴼᴹᴬᴺᶜᴵᴺᴳ ✺✺✺✺ ✺✺ *(F. J. W. A)* ✺✺✺✺ 17.... *Korafin yayi yawa my Guys, saurin mai kuke kubi littafin sannu a hankali dan yanzun aka fara🙃 Duk kuyi hakuri Gabad'aya Group d'in na cire kowa har ni k'aina Kunce a saku group an sakaku amma bakwa magana kun mayar da group sai kace gidan zaman makoki😃: COMMENT bai dame ni ba, cost bashine a gabana ba muje a haka zaku sami shi a sauran groups da nake* *Yauma ba Editing🙅🏻‍♀️* Da sauri Yusuf yayi k’anta Yana Kiran sunanta Amma i'na Ko numfashi batayi koman ta ya tsaya cak, hankalinsa yayi bala'in tashi Gurin Mimi ya nufa tare da riketa Yana jijjigata “mimi pls ki temaka min karta mutu wlhy Inna tsananin kaunarta sosai wayyyo Yusrah ki tashi Karki min Haka dan Allah” ya karasa maganar Hawaye na wanke masa Fuska Mimi dake tsaye Gabad'aya jin abin take tamk'ar a mafarki Kallon Jidda tayi murya ciki ciki ta fara magana. “Jidda mai kike fad’a Haka? Anya k’anki Bata samu matsala ba!” kafin Maijidda tayi magana sukaji Magana a bayan su “Gaskiya Maijidda ta fad’a Mimi Yusrah 'yarkice ta cikin ki” cewar Mai aikin gidinsu a matukar firgice Mom ta juyo tana binta da wani i'rin Mugum kallo cikin i’hu tace “Kamar ya Nida ’yata zakuce ba nawa ba? yau Naga karfin Hali Yusrah d’ince ba 'yata ba?!” Dad da tund’azun ya kasa Magana gabad’aya jikinsa yayi wani i'rin mugum sanyi Baffa kuwa dafe k’ansa yayi tare da zaman ’yan borin a kasa Granny ma i’do ta kwalalo waje tare da fashewa da kuka domin i’ta har ga Allah lamarinsu ya sata cikin duhu Kallon Maijidda Baffa yayi tare da fad’in “Jidda are u serious?” gyaɗa Masa k’ai tayi hawaye na wanke mata fuska Bata taba zaton Wanan ranar zata zo musu a Haka ba barin ma Mom tayi bala’in Bata tausayi Amma tafi jin tausayin Yusrah Minaty ne ta fad’o d’akin kamar wacce aka jehota kasancewar taji komai domin tun d'azun take tsaye babu Wanda ya lura da i’ta Kan Yusrah tayi ta d’agota tare da rumgumeta tana wani i'rin Kuka mai'cin Rai. Kukan da duk wani mai i'mani saiya zubda hawaye kowa a Gurin kuka yake Amma Banda Yusuf dake bin kowa da i’do mikewa yayi ya nufi Gurin Momy Yana nunata tare da furta “Momy da gaske ne Yusrah ba 'yarki bace Anya kuwa ba mafarki nake ba wannna wacce i’rin Mummunar Al'amari ce !! Ya Allah kasa mafarki nake Ya rabbi kasa inna tashi daga wanan barci Ubangiji karka sa na sake i’rinsa” runtsa i'do yayi Yana yamutsa gashin kansa sake bud’e idanunsa yayi fess cikin na Momy dake zaune tana Kallon Maijidda a hankali jidda ta dafa kafad’arsa tana fad'in “Wannan ba mafarki bane zahiri ne Yusrah k’anwarka ce uwa d’aya uba d’aya” Granny tace “menene shaidar ki na fad’in Haka?” mai'aikinsu tace “Dr ki fito ki musu bayani yanda zasu fahimta Dan Allah” Dr dake tsaye jikin kofa Gabad'aya jikinta yayi sanyi Bata bata zaton Abinda ta aika zai Zama musu matsala ba sai yau. Momy na ganin Dr Saddika ta mike da sauri tare da nufarta cikin in in na tace “yauwa ki fad'a musu a hannunki na haihu ki fad’amusu ke da k’anki Kika kar’bi haihuwata ki fad’a musu Yusrah ’yatace ta cikina ki fad’amusu nace Saddika ...!!” ta karasa maganar tare da cin kwalar rigar Dr hawaye ne ya wanke Dr Saddika fuska “Tabbas nice na kar’bi haihuwar ki Hajiya Maryam Naso ace Kuma abinda Kika Haifa ya rayuwa Amma Kash sai dai ba Haka Allah yaso ba naso ace Yusrah 'yar kice....” katse ta momy tayi cikin hargagi tace “ban Gane ba kamar ya kema kin bi sahunsu ne kai nifa kun hargitsamin kwakwaluwa” Ajiyar zuciya Minaty ta sauke kafin tace “Momy Amatsayin ki na uwa ya kamata ki fita ki bar 'yarki i'ta kad’ai a ’bangaren ku kullun in Zaki tafi aiki Yusrah kuka take maganarta d’aya yanzun momy tafiya zakiyi ki barni ni kad’ai ? Ke kuma sai kiyi tsaki Dad a matsayin ka na uba ya dace ta tashi ka tsallake kasarka ka tafi wata uwa duniya niman kud’i 'yace kwaya d'aya tal Ubangiji ya baku Amma saboda son aiki da ku yan Boko kullun sai dai a barta i'ta d'aya bayan kun barta kunsa maike faruwa bakwa Nan?” share Hawayen fusk'anta tayi sannan taci gaba “tirrr tirrr da iyaye masu i'rin Halinku gaskiya Iyaye musammam ma Mata ya akama a Gyara Ku FARGA tun huri ku lura da tarbiyar 'ya'yan ku Mata Momy ki duba rayuwata wani tasku ne bangani ba a Gurin matar uba kuma yar uwa ga Mahaifiyata gashi duk i'tace silar lalacewa ta gashi ta Bata min rayuwa rayuwar da in ba tare da mace ba bazan ta'ba jin dad’in yinsa ba Kullun inna kuka kuk'an bak’in ciki na rashin samun kulawa daga Gurin mahaifina da 'yanuwan shi gashi yanzun rayuwar dana ke ciki ba ta kwarai bace” karasa maganar tayi tana sakin wani i’rin kuka kowa na Gurin sai da ya tausaya Mata “Gaskiya ne Maganarki Amina *ban farga ba* gashi yau har 'yata ta cikina wai yau ciki ne a jikinta wayyo Allahna...” kuka ta saka sosai Baffa yace “Saddika Yusrah 'yar WACECE” sunkuyar da k’ai tayi kasa sanan tace “Yarka ce Alaji tausayi da tunanin halin da Hajiya mariya zata shiga Nan gaba ne yasa na Aikata abinda yanzun na dawo nake lamada da nasan haka zai kasance wlhy da tun Farko na barwa Hajiya mariya gawar 'yarta” shako waiyar riganta Momy tayi tare da fad'in “what... Da ...dagaske kike Saddika nawa 'yar ta mutu mai yasa Kika min Haka pls Mai yasa..” tarin da Yusrah tayi ne yasa suka nufeta dukk’ansu riƙe take da Hannun kawarta Minaty kallon kowa tayi kafin ta sauk’e idanunta k’an Momy wani kuka ne ya kufce mata matsowa Yusuf yayi da niyar kamata Amma sai ta dakatar dashi ta hanyar d’aga Masa Hannun “Karka matso Kusa dani” tsayawa yayi cak yana kallonta kamar zaiyi kuka mikewa tayi a hankali tana dafe Cikin jikinta har Gurin Mimi tazo ta rumgumeta “Shiyasa nake jinki daban a Raina Ashe kece mahaifiyata gaskiya an cuceni an cuce ki mahaifiyata Amma Babu komai Haka Allah ya tsara A yanzun bana bukatar komai bana son komai mutuwata kawar nake bukata domin an riga an ruguzamin rayuwa” rumgumeta sosai Mimi tayi cikin kuka i'tama ta fara magana “a a Yusrah Karki ce haka pls..” katseta Yusrah tayi da sauri sannan ta nuna cikin jikinta “ban ta'ba jin tsanar wani a duniya kamar cikin dake jikina ba Wai ace Yayana shi yamin mai zan Haifa d’a ko kani ? 'ya ko k’anwa? Nafi K'aunar mutuwata da inga wannna ranar ...” FARHAT

BAN FARGA BA..Where stories live. Discover now