19

2.9K 48 1
                                    

*_✺ BAN FARGA BA✺_* ✺✺✺ ®🌁(F.J.W.A) 19…. *Nagode sosai da Addu'oinku na i'sa lafiya💗* Cikin fargaba da tashin hankali suke bin motarsa Gabad'aya Hankalinsu ya gama tashi ganin i'rin Gudun da yake zubawa a Kan titi a wani tsadaden Asibiti ya tsaya da motarsa bai ma shiga da motar ciki ba domin a ganinsa Bata lokaci ne fitowa yayi ya d'auketa da gudu yayi cikin asibiti yana kwalawa nurse Kira da sauri suka fito ganinsa da Mara lafiya ne yasa d'aya daga cikin su komawa ba'afi minti 1ba, sai gata da gadon tura Mara lafiya Zuwa tayi da niyar Karban Yusrah wani banzar kallon daya watsa Mata ne yasata jan baya da sauri cikin ƙaƙƙausar murya yace “inna Doctor Dr...?” Dr Saddika da fitowar ta Kenan ya sata fad'in “Subahanalillah mai'yasa meta ko Haihuwan NE?” A hankali take bud'e idonta tun tana ganin dishi dishi har ta bud’e su fesss Ak'an fusk’ansa, dafe mararta tayi a hankali ta motsa labbanta alamar son yin magana ganin Haka yasa ya kai kunninsa dai²n bakinta “Zan mutu cikina sai juyi yake yi” ta karasa maganar Hawaye na wanke Mata fuska a hankali ya nufi d’akin da Dr ta nuna Masa dai-dai lokacin da su Mimi suka karaso gurin d’aurata yayi akan gadon kallonsu Dr tayi kafin tace. “kud’an bamu guri...” bai Bari ta karasa ba yace “babu inda zamu...” kallon tsana Minaty ta watsa Masa Taski yayi yana watsa Mata kallon banza, girgiza kai Mimi tayi domin Duk abinda sukeyiwa junansu tana ankare dasu a hankali ta kama hannun Baffa da granny suka bar d’akin Dad ma Hannun Yusuf ya kama suka fita d’aki ya saura daga momy sai Minaty a hankali suka karasa bak’in gadon Zuwa wannna lokacin Yusrah ta galabaita duk ta fara fita daga hayyacinta Momy tace “Saddika haihuwace wai ko menene?” lumshe ido Saddika tayi tare da jingina da bango a hankali tace “Haihuwa ce Amma bazata i'ya haihuwa da k’anta ba, Addu'ar ku muke bukata Momy” ta karasa maganar tana share Hawayen fusk’anta, Jiki a sanyaye momy ta nufi gadon da take a Hankali take Magana bayan ta Kama hannunta “Baby ki yafe min kinji Pls nasan ban tsaya na kula dake yanda ya kamata ba, maganar Granny gaskiya ce, da take cewa Ban farga ba..¡ gaskiya maganar Haka ne dana farga da ban barki a gida cikin part d’inmu ke d’ayaba, ashe maganar ki abin lura ce duk lokacin da zani aiki kina cikin damuwa da tashin Hankali ashe....Ashe... Kinsan abinda kike fisk’anta” kuka ne ya kwace Mata “Momyna Baki min komai ba, inna kaunarki sosai banji tsanarki ko kad’an a Raina ba.. nasan Haka Allah ya kaddaramun nasan kuma ni ba mai tsawon rai bace momy inna ji a jikina bazan kuma rayuwa a cikin ku ba, Inna jin wani i'rin a jikina inna ji kamar zuciyata zata fashe an Bata min budurcina bani da wani Amfani i’dan na rayu wa zai Aure ni wa zai Soni ?” lumshe ido tayi hawaye na gangarowa a k’an fusk'anta, “bani da wani Amfani momy domin duniya ta i'sheni Bata Raina bani da wata kima yanzun inna rayu zan dawwama cikin k’unci da bak’inci anyi min mugunta abin bak’inciki Yayana uwa d’aya uba d’aya Duk Ak'an rashin samun kulawar iyaye Haba yaza nayi...! yanzun fa ciki gareni har wata d’add’aya wata Bakwai tsaban tashin hankali cikin bai k’ai haihuwa ba za'a fed’eni ya Allah kayi gaggawar d’aukar raina Rabbi karka barni na Kara a cik’akk’un mintis a duniya Allah yasa d’a ko ’yar da zan Haifa ya rayu ko ta rayu ya Zama lzina ga Iyaye masu i'rin Halin ku momy Amina inna sanki kamar 'yar uwata domin sanki a jinina yake pls ku fita ku barni kawai..” Kuka suke sosai Gabad'aya zuciyar likitocin ya karye sunji tsananin tausayin su haka suka bar d’akin kowa na sahrar kwalla “Allah Sarki Nima sai da na share kwalla domin na tuna da wani Abu ...lol” cikin gaggawa aka had’a kayan Aiki Zaman dirshan Yusuf yayi Yana kuka wiwi domin tayi mugum bashi tausayi lokacin da ya ganta za'a shiga da i'ta dak'in tyata granny ma kuka sosai take i'ta so take taji makasudin labarin .... So take tasan Taya Haka ya kasance ? Suna zaune shuru kusan awa d’aya ba Labari can Dr ta fito daga d'akin da sauri suka nufeta cikin rawar murya Minaty tace “Dr ya take ?” kallon su sosai Dr tayi ganin yanda suka Zama wani i'rin kamar sune masu nakudar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace “An cire Mata 'ya mace... Yanzun za'a Gyara su kafin ku shiga kuganta” cikin minituna kalilan aka gama komai Nan aka kaita d’akin hutu gbdyn su suka shiga d’akin kwance suka isk'eta tana zubda hawaye Koda suka Gama shugowa idanunta ta watsa Masa Nan shima ya tsaya kallonta a hankali yazo tare da kama lallausar hannunta, wani kuk’an bak’in cikine taji ya kwace Mata daga ta fara wani i'rin mugum shaguwa wani mugum tari tayi Nan take sai ga jini a matukar firgice yayi k’anta da niyar kamata wani mugum tsawa Mimi ta watsa masa babu shiri ya ja birki... Kukan yariyar ne ya ankarar dasu sai yanzun suka ma tuna da jaririyar Dr ne ta d'auke ta tare da mikawa Yusrah girgiza Mata Kai Yusrah tayi tare da kawad da idanunta gefe ganin yarinyar sak Yusuf hannunta na dafe da Kirjinta wani i'rin juya kai take tare da fashewa da wani mugum kuka Saddika tace “kar’bi yarki ki Bata Nono Tasha Karki ce Zaki horata domin Bata san komai ba” Da kyar Yusrah ta i'ya furta “Yata ko k’anwata ...” Mika Hannun tayi tare da Kar’ban yarinyar Minaty tayi wa alamr tazo cikin sauri kuwa tazo Kama hannunta tayi sosai tare da Mika Mata Jaririyar “na Baki i'ta halak malak ki lura min da i'ta Inna rokon Allah ya rayata ya kuma shiryata burina d’aya yanzun shine Naga Andaura Miki Aure keda Yusuf kuma yau nake so yanzun yanzun nake so ......wani mahaukacin tari ta fara yi ba kakkautawa i'danunta ta runtsa da k'arfi tana matse Kirjinta domin tana ji kamar yaji aka dasa Mata a Kirjinta a hankali ta zaro wani Farin takarda jikinta wani i'rin Bari yake Mimi ta mikawa kafin Mimi ta karaso inda take taga Hannunta nayin kasa a hankali da mugun gudu ta karaso tare da riƙe ta sosai “Mimina in...n.a sanki sosai Inna sanku duka ku yafe min na yafe muku ku min Addu'a ga Yarinyar Nan A kula da i'ta Kar a barta Kar a banzatar d i'ta ....” Kallon fusk'an kowa tayi tana sake musu murmushin karfin hali tsayar da kallonta tayi a k'ansa a hankali tace “burina kawata in har sonda kake i'kirarin kana min na gaskiyace ka Auri Amina domin da i'ta ka dace kun dace da j..u.n.a” Lumshe i'dunuwa ta fara yi a Hankali ta fara furta kallamar “La’ilahaillallahu....” da sauri momy tayi kanta tana Kiran sunanta Ama inah Rai yayi halinsa fusk'anta kwance da murmushi kamar ka kirata ta Am'sa timmmm sukaji fad’uwar Abu a kasa Suna juyawa sukayi arba da Yusuf shima ko numfashi baya yi da Sauri Dad yayi k’ansa Mimi kuwa mutuwar tsaye tayi..... *Wayyo Yusrah ta Ubangiji ya Miki Rahama* Washhhh Muje Zuwa *FARHAT*

BAN FARGA BA..Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin