season 2 episode 2

294 11 8
                                    

RANAR WANKA 2

Bonus Episode 2

GODIYA TA MUSAMMAN

Hajiya Hauwa Saudia
Hajiya Umma Isa Niger
Hajiya Balki Giwar Mata
Anty Zee Daura
Maryam Mandira
Salma Gusau
Fareeda Askira
Jamila Jamzy

JINJINA
Ranar wanka group 1&2
Kanu/Shuwa
Ful6e Gongola
Ful6e Ngoruje
Mo Allah Barkidini
Da duk fans na Ummu Subay'a 🥰


Washegari Shatteema da Umar sukayi sammako xuwa Kaduna ba tareda sun sanarda kowa ba.
              
                   KADUNA
Sallamar Mami Zahra tayi zataje kitso makobta tana fita taci karo da Maryam a kofar part dinsu, harara Maryam ta bugawa Zahra taja tsaki tace " Ta Allah bata mutum ba nan gani nan bari wlh, badai Boka da malam ba ba'a isa a kwacemin Miji ba" sam Zahra bazata lamunci daukar wannan maganar ba ta juyo a fusace tace" me kuma ake da Matar joni Matar shune, tun kan kisan waye Shatteema nasanshi, Kinga shudina zaki samu kenan, ya gama duk kallamansa akaina, ya gama duk soyayyarsa akaina, a haka kuma na nuna banaso" bata jira cewar Maryam ba tayi gaba.
Ganin ana bude gate ya sakata dakatawa da fitan tana jira taga mai shigowa, ganin Motar Ya Anwar yasata murmusawa ta karasa gaban motan, ya fita ta rumgumeshi ita kam ma ta mance da shiba muharraminta bane, daidai lokacinda Motar su Shatteema ya shigo cikin gidan kuma idonsa akansu, nan zuciyanshi ya shiga bugawa, tunaninsa ya hargitse ya rasa abunda ke masa dadi.

Rage tsayinsa Anwar yayi yazo dai-dai kunnen Zahra yace "Mata ta Fara rumgume Mijinta tun kafin aure" nan hankalin Zahra ya dawo jikinta ta sakeshi tana murmushi tana rufe fuskarta, daidai da karasowarsu Shatteema wajen, a razane Zahra ke kallon Shatteema, sabon sonsa keta kewaye jinin jikinta da gabobinta, duk da ya rame ya kara kyau, ya kara haske ya kara haduwa.
Hannu Anwar ya mika musu sukayi musafaha
Anwar ya dubi Zahra data kafe Shatteema da ido yace" bazaki gaisu bane Zahra" anan Zahra ta tsaya tsayin daka ta ture duk abunda ke mata yawo a zuciya tace" ban sansu bane ai" kamar Shatteema zaiyi kuka yace "mune yau Zahra kike cewa baki sanmu ba" cike da tsiwa da matsifa tace " eh ku din, ku suwaye ne, da can ne nasanku Amma yanxu duk kun mutu a xuciyata, bbu wata danganta tsakanina daku ta sanayya, idan kunxo gidanmu don nine gwara ko koma don ga Mijina nan insha Allah" a nan Anwar ya Gane bakin zaren.
Umar dake tunanin mezai iya cewa ya bude baki yace" Amma Zahra ya kamata ki mana adalci kiji abunda ya kawomu" wani mugun harara Zahra ta hurgawa Umar zatayi magana Anwar ya dakatar da ita ta hanyar cewa" shut up, wuce ciki" bbu musu Zahra ta wuce ciki tana kwalla.
Falon Abba Anwar ya musu masauki ya Kira Abba ya sanar mishi yayi baki.

"Baba nasan nayi laifi kuma na kuntatawa Zahra Amma yanxu na gane kuskurena don Allah a taimakeni a auramin Zahra" Shatteema ne durkushe a gaban Abba Yana Kora masa jawabi, ssai Shatteema ya bawa Abba tausayi Amma bbu yadda ya iya yadda Zahra ta kafe Akan zancenta bazata sauya ba, a nutse Abba yayiwa Shatteema bayani ya karashe da bashi hakuri daya karbi kaddara, haka Shatteema naji na gani damar auren Zahra ta kubuce masa, haka suka koma Abuja ba tareda biyan bukata ba

Tunda Zahra ta shige dakinta kuka take mai cin rai, Mami ta bata hakuri har ta gaji ta shareta, da daddare Anwar ya shigo suka gaisa da Mami ta mishi bayanin kayan lefe da sauran abubuwan bukata na auren, bayan sun gama lissafine yake tambayar Zahra Mami tace" tana dakinta"

Kwance Akan bed Anwar ya sameta kamar mara lafia, zama yayi kusa da ita yace" Zahra nasan ganin Shatteema ne ya jefaki wannan halin, don Allah kada ki cutar da kanki kije kawai ki cewa Abba kin amince Zaki aureshi ni wlh zan hakura" tashi Zahra tayi ta zauna ta kama hannun Anwar, wani yarrrrrr Anwar yaki a jikinsa tace" waye Shatteema? Yaushe nasan Shatteema? Shekara nawa nayi da Shatteema? Har zan iya fifitashi akanka, kai na sani tun tasowata, kai ka kaunace ne tun ban san kaina ba, kai yanxu nakeso kuma nake kauna, don Allah Ya Anwar a tsakanina dakai mu rufe babin wani can daban Wai shi Shatteema, mu duba rayuwarmu na gaba kawai" kalaman Zahra ya sanyaya zuciyar Anwar ssai, janye hannunsa yayi a rikonda Zahra ta mishi cikin sanyin murya yace" Zahra Allah yayi miki albarka, nagode da wannan matsayin da kika bani, Allah ya bani ikon faranta miki kamar yadda Kika faranta mini" a shagwabe Zahra tace" ai kai kullum a farantamin kake Ya Anwar" ta kara da cewa" Amma Ya Anwar idan akayi auren ni anan zan zauna har sai na gama makarantar koh"

"Kenan zan dauki hutu har ki gama nima na tare anan din" Anwar yayi maganar cikin zolaya, daria Zahra tayi tace" uhmmm uhmmm nikam"

Hira sukayi ssai ganin Zahra ta Fara nuna alamun bacci ne yasa Anwar gyara mata kwanciya ya mata addu'a ya fice

UMMU SUBAY'A ❤️

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 18, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now