episode 10

263 14 0
                                    

RANAR WANKA..........
Ummu Subay'a
10
Haydar ne ya tako har inda take cikin izza da isa tareda takama fuskarsa sanye da black glass irinta rashin mutuncin nan yace" Zahra kiyi hakuri ki sakawa ranki hakuri ni ban ta6a sonki ba Kuma bazan ta6a sonki ba har abada, nayi amfani da sonda kikemin ne nayi cimma burina na kama Babban Boko Haram, kiyi hakuri ladanki na wajen Allah" yana gamawa ya juya zai tafi Zahra ta durkusa kasa ta kama wandonshi tana kuka mai ban tausayi" Don girman Allah Haydar kada kamim haka, zuciyar Zahra jaririyace da sonka ta girma da sonka ta saba, wlh bazata ta6a jin kalmar hakuri ba, idan ka barni zan iya rasa Raina" Jan kafarsa Haydar yayi yace "Zahra ki manta Dani kawai"  faduwa Zahra tayi a wajen tana kuka mai cin rai tana rokonsa, Amma ko waiwayawa Haydar baiyiba ya wuce. aka bude mishi mota ya shiga duk jami'an tsaron suka shiga suka tafi dasu Malam.
Duban yaran Malam kanana da sauran Matansa dake kuka ya Kara tunxura Zahra ta kara saka wani kuka, ta tausaya musu Kuma ta tausayawa kanta, Yakura da komai ya faru gabanta ta karaso ta daga Zahra suka shiga gida .
"Zahra Kinga abunda taurin kanka Dana xuciyarki abunda ya sakamu ciki, har zaki Bari zuciyarki ta rudeki kici amanar kawarki da iyalanta" Zahra dai ta kasa cewa komai sai kuka take, tsaki Yakura taja tace "rufemin baki bakiyi kuka bama wlh, ba kukaba yanxu kika fara wlh, kin kuwa San irin bala'inda kika sakamu ciki ki..........." maganar ne ya makale a bakin Yakura ganin yadda Khadija ta shigo a sanyaye gida, zubewa tayi  gaban Zahra tana kuka mai kunci tace " Zahra kin cuceni , Zahra kin ruguzamin rayuwa, Zahra kinci amanata, Zahra ko Babana yankan mutane yake yacisu ke mai rufamishi asirini saboda rayuwata, Zahra Taheer yayi duk yadda zaiyi yaji sirrin gidanmu Amma naki Sam duk da ban San kowayene Shiba, tunda naga kin dage da zama a gidanmu jikina ya bani ba don Allah kike zuwa ba, Ashe so kike ki wulakanta rayuwata Zahra, kiyi dariya kin barni babu kowa ba uwa bbu uba babu yayyi duk an kwashe su, bai kamata kiyi kuka ba Zahra dariya ya kamata kiyi masoyinki ya cika burinsa, Amma ki sani kuka kam yanxu kika fara wlh, ina mai Dana sanin saninki a rayuwa, ina mai takaicin saninki a rayuwata" kunci, takaici da kunya su suka Hana Zahra dagowa ta kalli Khadija sai kuka taketayi tace "na cancanci duk wani hukunci daga gareki Khadija kiyimin duk abunda kikeso kima kasheni kawai na huta" girgiza kai Khadija tayi tana yake tace " ciwon zuciyarda Haydar ya dasa Miki kawai ya isheki hukunci a rayuwarki" mikewa Khadija tayi taje gaban Yakura dake kallonsa idonta cike da hawaye "Anty kuyi saurin barin unguwar na kuje inda 'yan unguwar nan bazasu gane ba daku da Mustapha don akwai wani Yayanmu Shima yana ciki Kuma bayanan aka kama su Baba idan ya dawo yaji labari zai iya hallakaku" Khadija na gama magana ta fice tana kuka, Kuka Yakura tasa tace "Zahra kin cucemu" da gudu taje ta dauki wayarta ta Kira mijinta ta sanar mishi abunda ke faruwa, a kideme yace su jirashi yana hanya su had'a kayansu kafin yaxo, mikewa Yakura tayi ta shiga had'a kayansu cikin gaggawa, tana hadawa ne Khadija ta Kara shigowa wannan karon a firgice take tace "Anty ku fito ku gudu yaran gidamu sunje sakawa shagon Mustapha wuta Kuma sunce zasuzo gidan nan ma.
A sorace Yakura da Zahra suka dibi kayansu da taimakon Khadija suka bar anguwar Sai Kiran mijinta tayi ta sanar mishi, a Sulemanti ya samesu ya daukesu sukaje gidan wani abokinsa suka kwana Zahra kam sai kuka, tun Yakura na bala'i har ta dawo ta fara rarrashinta.
Labari mai dadi daya riske Yakura shina anyiwa mijinta transfer zuwa Enugu, ai washegari da safe suka shirya har Tasha suka Kai Zahra suka sakata a motar Kaduna su Kuma suka wuce Enugu, gidansu da Shago kam an Kona kurmus.

                             ABUJA
Maryam ta washe ta waske ta koma babbar mace ga hutu ga gyara sai ta dawo kamar wata black America, zaune take a dinning table tana breakfast Sultan ya shigo ya sameta ya zaune a gefenta sai kallonta yake, daga ido tayi tayi masa fari da ido tace "kallon fa ya Sultan" tsaki yaja yace "me abun kallo a jikinki" dariya Maryam tayi tace "ka fini sani tunda kai ke kallo" Mommy dakejin tattaunawarsu tana zaune a falo tace "shashancin ya isheni haka, Sultan oyaa ga hanya ka ficemin anan" dariya Sultan yayi yace "momcy abun hadda korine akan wanan kwailar" tsaki Mommy taja tace "koma mecece zo ka wuce" ficewa Sultan yayi yana magana kasa kasa" wlh sai na girbe shukan nan" Mommy tace "me kace" dariya Sultan ya karayi yace "cewa nayi Allah ya baku hakuri" ta6e baki Mommy tayi tace " ke Kuma zo nan" babu musu Maryam taje ta zauna gefen mommy " kada ki dinga sake jiki da yaran nan, bakiga yadda kike bane ko mace sha'awa zaki Bata balle matasan nan" sunkuyarda kanta Maryam tayi tace " tooooh" tsaki Mommy taja tace" kunyar uwar wa kike, kee saurareni aure zakiyi fah tamm" wayar Mommy ne ya fara ringing ta daga taga Hajiya Hauwa, ihu tasa tace "abun yazo" picking tayi tareda da sallama, magana sosai sukayi ta kashe wayar ta dubi Maryam tace "yarinya ranar da muke jira tazo maza tashi kije kiyi wanka Direba xaixo ya daukeki ya kaiki gidan Hajiya Hauwa Shatteema ya dawo" murmushi Maryam tayi don itama ta kwadaitu taga wannan Shatteeman da Mommy keta kwadaita Mata aurensa.
Maryam na shiga wanka Mommy ta Kira Hajiya Madina C.O.E na Arewa fashion parlour ta turo Mata kayanda tayi order da mai kwalliya da turaruka
Yadda aka fidda Maryam Kai kace Amaryan Kanuri ko Shuwa ne, sanin Hajiya Babba Balarabiya/ Shuwa ce yasa Mommy sakawa akayiwa Maryam adon Shuwa da lupaya masu kyau da daukar hankali, ba wani kwalliya kyaunta kawai mai kwalliyar ta fitar Mata ga uwar kamshin datake fitarwa ta ko ina hmmmmmmmmmmm wani Abu sai bakar mace kyakyawa , don nan take Maryam ta dauke ido da kyau sai kace Sarauniyar kyau na Africa.

*SAKONKU*
*" Ta Bature lallai kin cika 'yar baiwa, bakya rubutun banza sai kin nishadantar damu, bari mu gyara zama don Jin chakwakiyar cikin novel nan, Allah ya Kara basira"*
        *Ummu Aira daga Ghana*

Ta Bature ce✍🏻

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now