episode 4

341 16 0
                                    

RANAR WANKA............
04
A kwana a tashi asarar mai rai, Zahra da Maryam sun kammala makarantarsu ta secondary, idan kowaccensu ta fara Shirin barin gari, ana washegari zasu bar gari Zahra taje har falon Mama ta samu Maryam da Mama tareda Ahmad.
"Ya Ahmad yaushe a garin" Zahra ta tambayi Ahmad, harararta Ahmad yayi yace" ban saniba, kin damu danine balle kisan yaushe na dawo" charap Mama ta kar6i maganar tace" Ina kuwa ta damu dakai, da zamuje visiting dinka ba cewa tayi bazata ba" bakinta Zahra ta kama cikin mamaki tace " laaah ba Ya Nasir bane yace bazanje ba motar ta cika" tsaki Mama taja tace" tohm maganar ya isheni haka" Murmushi kawai Ahmad yayi don Maryam ta riga ta bashi Labarin abunda ya faru da sukaje visiting din.
"Mama nazo sallamarki ne gobe tone 1 zanbi na tafi Maiduguri" washe baki Mama tayi tace" tareda mutumiyar kenan zaku bar gari, Allah sarki zamuyi kewarku" kallon Tara saura Zahra tayiwa Mama a zuciyarta tace" ~kewar diyarki kawai zakiyi~" a zahiri Kuma tace " kana dawowa muna tafia, Kuma nasan kafin mu dawo ka koma" kafin Ahmad yayi magana Maryam tace" nikam wajen Ya Ahmad kikazo ne ko wajena" harara Ahmad ya hurgawa Maryam yace" kishi kike dani ne" dariya Zahra tasa tace" tambayeta kam tabi ta saka ma hiranmu Ido" mikewa Ahmad yayi yace" Mama ki turomin abincin idan zan kwanta zanci, and Lil-Zee kada ki manta gobe kan ki tafi kizo ki sallame ni" bai jira amsar kowa ba ya fice, itama Mama mikewa tayi ta basu waje.
Maryam ta dubi Zahra tace" wlh I will really miss you Sweetheart" murmushi Zahra tayi tace" same here Sweetheart, naji kishin kishin wai Abba zai bamu waya gobe" ihu Maryam tayi tace" don Allah dai" janyota Zahra tayi tace" ki rufamin asiri mana, kada ace ni na baki labari, hira sosai sukayi kamar bazasu sake ganin juna ba, sai 12:30 am Mama ta leko tace" Amma dai lafiyarku Koh, maza kuje kuyi bacci don ku tashi da wuri, Zahra kije kitchen ki dauki abinci ki kaiwa Yayanki" babu musu Zahra ta wuce kitchen, ita Kuma Maryam ta wuce bedroom
Kwance Ahmad yake akan bed dinsa yana karanta wani novel mai suna MY LOVE FOR YOU, shigowa Zahra tayi da abinci a hannunta ta ajiye ta kwace littafin ta karanta sunansa, murmushi tayi tace" su Ya Ahmad da karanta love story, ka sama mana Anty ne?" ta karashe maganar tana dariya" kwace littafinsa yayi yace"jeki sai da safe, ba hali mutum ya karanta love story sai ya fara soyayya, wuce ko da rankwasheki" ficewa Zahra tayi tana dariya.
Buguwa Zahra tayi da abu cikin firgici da tsoro tayi baya zata fad'i taji an tareta ta fad'a kirjinsa, cikin sanyi murya yace" Ina kika fito cikin daren nan" jin muryan Anwar ne yasata ajiyar Zuciya ta kara makalewa a jikinsa tace" na kaiwa Ya Ahmad abincinsa" janyeta yayi daga jikinsa fuska a had'e yace " how dare you zakije dakin Ahmad cikin uwar daren nan, bakya ganin kin girma ne, wama ya aikeki" cike da shagwa6a Zahra tace" Mama ce fah ta aikeni, Kuma ai komin girman danayi Ya Ahmad muharrami nane" tsaki Anwar yaja yace" tafi ki ban waje ana Miki magana kina bawa mutane amsa" a shagwa6e Zahra ta bar wajen tana gunaguni, Washegari asuban fari duk suka shirya Anwar yakai su tasha
                           MAIDUGURI
A gajiye Zahra ta iso Maiduguri, bata bukatar Dan jagora saboda ba bakuwa bace, Adaidaita ta dauka Tasha har kofar gidan Anty Yakura, Yakura kanwar Mami ce ita take bin da Mami, tanason Zahra sosai sosai shiyasa Zahra ke sauka a gidanta, Kuma bata ta6a haihuwa ba.
Zahra na shigowa Yakura ta ruga a goje ta rumgumeta tareda da kar6an Jakarta ",Oyoyo Zahra hasken Mata" dariaya Zahra tayi suka karasa cikin gidan.
Tar6an girma da arziki Yakura tayiwa Zahra tanata haba haba da ita, haka shima Babagana mijin Yakura daya dawo ya nuna farin cikinsa ssai da zuwan Zahra.
Tace kunun Aya Zahra take ta dubi Yakura tace " Anty yanzu a gida kike sayrda duk yawan kunun Ayan nan" Yakura dake share goruna tace" Shagon da Uncle dinki ya bude a farkon layin nake kaiwa acan yake karewa tass" Peak milk Zahra ta juye a ciki tace" ai kina yinsa cikin aminci shiyasa dole ya kare" murmushi kawai Yakura tayi suka cigaba da aiki, suna gamawa Yakura ta dau Hijab dinta tace "bara nakai shagon" "muje tare dai Anty" cewar Zahra tana kokarin daukar tata Hijab din, Yakura batayi musu ba ta dauki kula daya Zahra ta dauki daya suka kai shagon "Mustapha  ga Zahra diyata ce daga Kaduna tazo ita zata dinga kawo maka kunun da abinci" washe baki Mustapha yayi yace" sannu Anty Zahra" hararar wasa Zahra tayi masa tace" Anty Kuma, babba dakai yaushe nakai Anty" dariya Mustapha yayi yace" sunan Antynane shiyasa nace Antyn" baki Zahra ta ta6e tace" tooh ai sunane kawai yazo daya" "uwar surutu muje mun bar gida bbu kowa, in yaso anjima kika kawo mishi abinci sai ku dora daga inda kuka tsaya" cewar Yakura taja hannun Zahra suka tafi
                       ABUJA
Tunda Maryam ta sauka a Abuja taketa shan kamshi don daga darajan ajinta, kuma ta samu gidan Mommy (Batula) daidai da tsarinta, mike kafa kawai take sai abunda 'yan aiki sukayi a gidan.
Yaran Mommy hudu ne Kuma duk Maza ne Sultan, Ameer, Bilal da Khalid Kuma duk manya ne bbu sa'anta, shiyasa ta samu freedom sosai.
Maryam na zaune a falo tayi crossleg tana latsa wayar Mommy hankali kwance taji Sallama amsawa tayi cikin halin ko in kula, daga ido tayi ta dubi mai Sallamar, shigarta kadai ya tabbatar mata ba karamar mutum bace, nan Maryam ta saki fuska tace" sannu da zuwa" fuskar matar babu yabo bbu fallasa tace" Ina Hajiya Batula?" muryan Mommy sukaji tana cewa " Kamar muryan Hajiya Hauwa nakeji a gidan nawa" rumgume juna sukayi irinta aminta bayan sun gaisa sun ta6a hira Hajiya Hauwa ta dubi Mommy tace" Ina kika samu kyakyawar yarinya haka" murmushi Mommy tayi tace "Maryam ce 'yar kanwata Sadiya dake Kaduna" "hausawa sukace a Bari ya huce shike kawo rabon wani, anyi Mata mijine?" Hajiya Hauwa tayi tambayar tana tsare Mommy da ido dariya Mommy tayi tace" haba 'yar yarinyar nan this year fah ta gama secondary duk bata wuce 16 years bafa, but inaso na hadata aure da Sultan" dafa kafardar Mommy Hajiya Hauwa tayi tace" ajiye maganar Sultan a gefe sahun giwa ya take na rakumi da SHATTEEMA nakeso a hadasu aure" a razane Mommy tace "ke Hauwa wani Shatteema" dariya Hajiya Hauwa tayi tace" Shatteema dai dakika sani, nima General ya bani daman zabo masa Mata tunda Hajiya Babba ta kasa, kinga ni ba wani dangi gareni na kirki ba balle na samu a wajen, tunda ke kawata ce ta arziki Kinga sai kema kuci arziki ku yagi arziki, amma fah sai ya ganta ya amince" cikin farin ciki da zumudi Mommy tace "kuje da ita mana sai ya ganta, ai da safe ake kama fara" dariya Hajiya Hauwa tayi tace" baya kasarma yaje Dubai Kuma inaga zai kai wata a wajen, idan ya dawo zan kiraki ki turomin ita, and don Allah Batula kar ki kai maganarnan gaban malamai ko bokaye, Abu ne na tsakani da Allah nakeso ayi, banason munafurci don muddin kikayi baza kare muku da kyau ba, Kuma kada ki sanarwa kowa sai Abu ya kankama" ajiyar Zuciya Mommy tayi tace " haba Hajiya wlh na daina duk halayen nan na nitsu rabonki da kiji nace boka ko Mallam yace tun yaushe wlh na daina" "Allah yasa" inji Hajiya Hauwa.

Ta Bature ce

RANAR WANKAWhere stories live. Discover now